Wa ya ci riba ko hasara a sayen ƴan wasa a Premier League a bana?

Asalin hoton, Getty Images
An kashe kusan sama da fam biliyan uku a cinikayyar ƴan ƙwallo a Premier League, inda aka kammala hada-hada ranar Litinin.
Kuma Liverpool ce kan gaba a yawan cefane da ta kashe sama da fam miliyan 400, wadda ta ɗauki Alexander Isak daga Newcastle a matakin mafi tsada a Burtaniya.
Haƙika za a yi tata-burza tsakanin ƙungiyoyin Premier League 20 da za su kalubalanci kofuna bana, har da na babbar gasar tamaula ta Ingila.
Liverpool ce mai rike da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi.
Bari mu duba ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a Premier League.

Asalin hoton, Getty Images
LIVERPOOL
Ƙungiyar Anfield ce kan gaba a yawan kashe ƙudi wajen sayen ƴan ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan wasa a matakin mafi tsada a Burtaniya a kakar nan.
Ta fara da sayen Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Alexander Isak kan fam miliyan 125 ranar da kasuwar za ta ci ta watse.
Cikin ƴan ƙwallon da ta saya har da Jeremie Frimpong kan fam miliyan 30 da Milos Kerkez kan fam miliyan 40.
Haka kuma Liverpool ta sayar da Luis Diaz da Darwin Nunez da Jarell Quansah daga karshe ba ta samu damar sayen Marc Guehi daga Crystal Palace, wadda ta ce ba ta samu ɗaukar madadin Guehi ba.

Asalin hoton, Getty Images
ARSENAL
Arsenal ta fitar da makudan ƙudi, wajen sayen ƴan wasa da yawa, domin mara wa Mikel Arteta baya, wajen lashe kofuna a bana, musamman Premier League, wadda rabonta da kofin kaka 22.
Cikin ƴan wasan da ta ɗauka har da Viktor Gyokeres, wanda ya kawo matsalar rashin mai buga gurbin cin ƙwallaye, bayan da ke fama da jinya.
Haka kuma Gunners ta sayi Eberechi Eze da Noni Madueke da Martin Zubimendi da Christian Norgaard da Cristhian Mosquera da kuma Piero Hincapie.
Kuma Gunners ta ɗauki mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga, duk dai domin ta taka rawar gani a kakar nan, sannan Arteta ya kara lashe kofuna bayan FA Cup a kakarsa ta farko da kuma Community Shield.

Asalin hoton, Getty Images
NOTTINGHAM FOREST
Duk da rashin jituwa tsakanin kociya, Nuno Espirito Santo da daraktan tamaular ƙungiyar, Edu Gaspar, Forest ta shiga kasuwa ta yi cefanen ƴan wasa don ganin ta yi abin kirki a kakar nan.
Sau biyu a ƙungiyar tana sayen ɗan wasa a matakin mafi tsada a tarhinta, bayan sayen Dan Ndoye da kuma Omari Hutchinson.
Ta kuma kashe fam miliyan 30 ƙudin sayen James McAtee, sai kuma Douglas Luiz da ya koma buga Premier League daga Juventus ta kuma ɗauki Nicolo Savona.
A ranar da za a rufe kasuwar cinikin ƴan kwallo ta ɗauki aron Oleksandr Zinchenko ta sayi Dilane Bakwa.
Ta kuma yi nasarar riƙe ɗan wasan tawagar Ingila, Morgan Gibbs-White, bayan da Tottenham ta yi kokarin sayen ɗan ƙwallon.

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanda suka yi hasara
NEWCASTLE UNITED
Duk da cewar Newcastle United ta sayi ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa da ɗan ƙwallon Stuttgart, Nick Woltemade, wadda ta fara da ɗaukar ɗan wasan Nottingham Forest, Anthony Elanga.
Sai dai kuma ba za a manta da batun Alexander Isak ba, wanda ya dage sai da bar St James Park, har da ƙin buga mata wasannin atisayen tunkarar kakar bana da wasa biyu da ta buga a Premier League ta bana.
Kuma rashin Isak ya sa tana shan wahala wajen cin ƙwallaye, hakan ya sa ta yi zawarcin madadinsa daga ciki har da Hugo Ekitike da ya zaɓi Liverpool da Benjamin Sesko da ya koma Manchester United har da Joao Pedro da kuma Jorgen Strand Larsen.

Asalin hoton, Getty Images
ASTON VILLA
Aston Villa tana fatan yin gogayya cikin ƴan shidan farko a Premier League a kakar nan, amma ta ci karo da cikas kan dokar kashe ƙudi daidai samu.
Duk da haka ta sayar da matashi, Jacob Ramsey, wanda magoya baya ba su ji daɗi ba.
Sai dai ƙungiyar Villa Park ta ɗauki Harvey Elliott daga Liverpool da kuma ɗan wasan Manchester United, Jadon Sancho, amma dai Villa ba ta samu yin cinikin da zai bata damar yin abin kirki ba, kenan sai abin da ta gani.

Asalin hoton, Getty Images
BRENTFORD
Byan da Brentford ta rasa kociyanta, Thomas Frank da ya koma Tottenham ta kuma sayar da ƴan ƙwallo uku da ya haɗa da Bryan Mbeumo ga Manchester United, yayin da Norgaard ya koma Arsenal da kuma Newcastle da ta sayi Wissa.
Sai dai ta sayo Dango Outtara daga Bournemouth kan fam miliyan 42.5, amma dai tana da jan aiki bayan rashin fitattun ƴan ƙwallonta uku a kakar nan.










