Me ya sa Bayer Leverkusen ta kori Ten Hag bayan wasa biyu kacal?

Tsohon mai horas da Leverkusen da Man United Eric Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon mai horas da Leverkusen da Man United Eric Ten Hag
    • Marubuci, Constantin Eckner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • Lokacin karatu: Minti 4

Bayan kama aiki a Bayer Leverkusen, tsohon mai horas da Manchester United Eric Ten Hag ya gaza jagorantar ƙungiyar na tsawon ko da mako 10.

Ba mako 10 ba ma, ko mako 9 bai cika ba, inda ya yi kwana 62 kacal a ƙungiyar, bayan buga wasan gasar Bundesliga biyu kacal.

An kore shi ne bayan Leverkusen ta gaza yin nasara a karawarta da Werder Bremen a ranar Asabar.

Da farko Leverkusen ce ta shige gaba da ci 3-1, inda Bremen ta samu jan kati, amma daga baya aka tashi wasan canjaras 3-3.

Hakan ya biyo bayan kashin da Leverkusen ta sha a gida a hannun Hoffenheim a wasanta na farko na gasar Bundesliga na wannan kaka. Wasa ɗaya ne kacal Ten Hag ya samu nasara a matsayin mai horas da Leverkusen.

An naɗa Ten Hag a muƙamin ne a ƙarshen watan Mayu domin maye gurbin tsohon kocin ƙungiyar Xabi Alonso, wanda ya koma Real Madrid.

Da farko, Leverkusen ta yi tsammanin zai iya jan ragamar sake gina ƙungiyar bayan rasa ƴan wasanta irin su Florian Wirtz da Jonathan Tah.

To sai dai sakamakon wasannin farko-farko na wannan kakar ba su yi kyau ba, amma ba wannan ne babban dalili ko kuma ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka haifar da korar Ten Hag ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kusan tun farko Ten Hag ya fara shafa wa kansa baƙin fenti sanadiyyar wasu matakai da ya ɗauka da kuma halayyarsa.

Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leverkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leverkusen ta sha kashi da ci 5-1.

Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Xhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaya saboda Leverkusen ta rasa manyan ƴan wasa da yawa.

Amma ƙungiyar ta riga ta sanar cewa Xhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland.

Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan wasansa tare da cewa ba su da kuzarin da ya kamata duk da cewa shi da tawagarsa ne suka jagoranci tawagar.

Bugu da ƙari an zargi Ten Hag da rashin kwarjinin da ake koci ke buƙata domin jan ragamar babbae ƙungiya, musamman ma ƙungiyar da ta kawo sabbin ƴan wasa da dama.

Da alama ya riƙa shan wahala wajen shawo kan ƴan wasa su bi tsarinsa. Na kusa da ƙungiyar sun ce bai iya yi wa ƴan wasa wata ƙwaƙƙwarar huɗuba gabanin buga wasa.

An ma bayyana cewa bai yi wa ƴan wasan jawabi ba gabanin karawarsu ta farko da Hoffenheim.

Akasin Alonso, wanda aka ce shi ya riƙa karin ganin ya ƙara ƙwarewa a harshen Jamusanci tare da samun ƙarin gogewa lokacin da yake jagorantar ƙungiyar ta Leverkusen.

Erik ten Hag takes a Bayer Leverkusen training session

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Erik ten Hag bai samu damar saita ƙungiyar ba domin tunkarar kakar wasanni da aka fara

Abin ya bada mamaki sosai yadda shugabannin Leverkusen suka yanke shawarar korar Ten Hag da wurwuri haka.

Wannan ba abu ne mai alfanu ba ga daraktan wasanni na ƙungiyar Simon Rolfes - wanda ya dage kan a ɗauki Ten Hag a lokacin da ƙungiyar ke son ɗaukar sabon koci a watan Mayu - har ma da shugaban ƙungiyar Fernando Carro.

"Raba gari a wannan mataki na farko-farko abu ne mai ciwo, to amma mun ga cewa haka ne ya fi dacewa," kamar yadda Carro ya bayyana a ranar Litinin.

Wani zai yi tsammanin cewa ya kamata a ce sun yi bincike mai kyau kafin ɗaukar Ten Hag aiki tun farko.

A ƴan shekarun da suka gabata Ten Hag ya kasance ƙwararren mai horaswa lokacin da ya samu nasara sosai a Ajax.

Ya lashe gasar Holand sau uku sannan ya kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League a shekara ta 2019.

Ko a shekarar farko na jagorancin Manchester United aikinsa ya yi kyau babu laifi, kuma an alaƙanta barin aikinsa daga ƙungiyar kan rikicin da ƙungiyar ta fuskanta amma ba domin gazawarsa a matsayin mai horaswa ba.

Amma a yanzu Leverkusen da alama tana cikin ruɗani. Kusan za a iya cewa a shirye suke su sayar da duk wani ɗan wasa da ya nuna aniyar barin ƙungiyar.

A lokaci guda kuma ƴan wasa irin su Malik Tillman da Jarell Quansah sun tafi ƙungiyar tare da sa ran cewa Ten Hag ne zai ci gaba da horaswa.

A yanzu Leverkusen na buƙatar nemo wanda zai maye gurbinsa. Akwai rahotannin cewa sun tattauna da tsohon kocin Barcelona Xavi, haka nan kuma tsohon mai horas da Dortmund da Leipzig Marco Rose na cikin waɗanda ake ganin za su iya samun aikin.

Ko ma wane ne za su ɗauko, ba za a manta da batun korar Ten Hag ba a nan kusa.