Manchester United ta kori Erik ten Hag

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Manchester United ta Ingila ta kori kocinta, Erik ten Hag daga aiki.
A shekarar 2022 ce ƙungiyar ta naɗa kocin wanda ɗan ƙasar Netherlands ce, inda ya karɓi ragamar aikin daga kocin da ya yi riƙon ƙwarya Ralf Rangnick.
Ten Hag ne kocin ƙungiyar na biyar tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson a 2013, baya ga waɗanda suka yi riƙon ƙwarya guda uku.
Sai dai tun bayan da ya fara aiki ne sakamakon wasannin ƙungiyar ke kwan-gaba-kwan-baya.
A sanarwar da Manchester United ta fitar, ta ce tsohon ɗan wasan gaban ƙungiyar Ruud van Nistelrooy ne zai yi riƙon ƙwarya.
Erik ten Hag ya lashe kofuna biyu a shekara biyu a ƙungiyar, daga ciki akwai doke Manchester City da Man U ta yi da ci biyu da ɗaya a wasan ƙarshe na kofin FA, wanda shi ne kofin farko da ƙungiyar ta lashe bayan shekara shida.
Rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a hannun West Ham a ranar Lahadi, shi ne na huɗu a gasar Premier ta bana, inda yanzu take mataki na 14 a teburin gasa da maki 11.
Wannan ne karo na biyu a tarihin ƙungiyar da ta tara mafi ƙarancin maki, bayan kakar 2029-2010 da ya tara maki 10 a wasa tara na farko.
Erik ten Hag ta kashe £645.8m tun bayan da kocin ya fara aiki a 2022, inda ko a farkon kakar bana, aka sayo masa wasu tsofaffin ƴanwasan da suka yi aiki a baya.











