Ƴanmata shida da za su haska a gasar kofin Afirka ta 2024

Asalin hoton, Backpage Pix/Getty Images
A ranar 5 ga watan Juli ne za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka na ƙwallon ƙafar mata (Wafcon) na 2024 da aka jinkirta.
Mai masaukin baƙi Morocco, wadda ta zo ta biyu a gasar da ta gabata, ita ce za ta buga wasan farko inda za ta kara da Zambia, tare da ƴar wasa Barbara Banda, wadda ita ce ƴar wasa mafi hazaƙa ta Afirka ta shekara.
Afirka ta Kudu ta dawo gasar da nufin kare kambinta yayin da Najeriya, wadda ta ɗauki kofin sau tara - fiye da kowace ƙasa - za ta so ta sake lashe shi tun bayan da ta yi hakan a 2018.
Yayin da wasu ƙasashen ke zuwa gasar a karon farko, wasu kuma ke neman kafa tarihi, BBC ta duba ƴan wasa shida da ake ganin taurarinsu za su haska a lokacin gasar.
Asisat Oshoala (Najeriya)

Asalin hoton, Getty Images
Ƴar wasan na taka leda ne a ƙungiyar Bay FC a gasar ƙwallon ƙafar mata ta Amurka (National Women's Soccer League).
Mai shekara 30 da haihuwa, ƴar wasan za ta kawo gogewarta a gasar da nacewarta wajen ganin an samu nasara.
Wannan ne karo na shida da take buga gasar ta cin kofin Afirka, bayan da ta gaza buga gasar ta shekarar 2022 bayan samun rauni a gwiwarta a wasan farko.
Ƴar wasan wadda ta lashe kyutar mafi ƙwazo a Afirka sau shida ta taimaka wa Super Falcons lashe kofin a shekarar 2014, 2016 da 2018, kuma ta lashe gasar zakarun Turai sau biyu tare da ƙungiyar mata ta Barcelona.
Duk da cewa tauraruwar Oshoala ta ɗan dusashe bayan komawarta da wasa Amurka, har yanzu ana mata kallon zaƙaƙura kuma ana sa ran za ta taka muhimmiyar rawa a ƙokarin Najeriya na sake cin kofin.
Clara Luvanga (Tanzania)

Asalin hoton, Al-Nassr FC
Wadda ta lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafar ƙungiyoyin mata ta Saudiyya sau biyu a ƙungiyar Al-Nassr, Luvanga na hango nasara a gaba, inda a bara ta shaida wa BBC cewa tana son zama ƴar wasa mafi ƙwazo a Afirka.
Ƴar wasan gaban mai shekara 20 a duniya na da damar samun ƙwarewa daga fitattun ƴan wasa a duniya, kamar Christiano Ronaldo da Sadio Mane waɗanda ke buga wa tawagar maza ta Al-Nassr wasa.
Luvanga ta jefa ƙwallo 19 a raga a kakar wasa da ta gabata, lamarin da ya sa ta zo a matsayi na hudu cikin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallo a gasar ta Saudiyya.
Haka nan ƙwallayen da ta zura a wasannin da Tanzania ya buga gabanin gasar na nuna cewa tana da idon mikiya wajen hangen inda za ta zura ƙwallo a raga.
Babu tabbas ko masu tsaron baya za su iya hana ta wali.
Sanaa Mssoudy (Morocco)

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwazon da ta nuna a shekarar 2024 ya sanya ta zama ƴar wasa mafi daraja a gasar zakarun ƙungiyoyin ƙwallon Afirka ta mata.
Haka nan an ayyana matashiyar mai shekara 25 a matsayin cikin mafi ƙwazo a tawagar Morocco a kakar da ta gabata, inda ta taka rawar ganin da ta bai wa ƙungiyar AS FAR damar lashe kofin gasar ƙungiyoyin ƙasar karo na 12.
Mssoudy ta zura ƙwallo a zagayen ƴan takwas da kuma matakin kusa da ƙarshe a gasar Wafcon da ta gabata a ƙasar ta Morocco.
Ana ganin ƙwarewarta za ta taimaka wajen ƙara wa ƴan wasan Morocco karsashi domin neman lashe gasar a karon farko.
Jermaine Seoposenwe (Afirka ta Kudu)

Asalin hoton, Getty Images
Afirka ta Kudu za ta so ta dogara da Seoposenwe wajen jefa ƙwallaye a raga - musamman ma bayan Thembi Kgatlana wadda ta lashe takalmin zinare a gasar Wafcon ta 2018, ta fita daga tawagar.
Kamar Kgatlana, Seoposenwe da aka haifa a Cape Town taka leda a Mexico.
Mai shekara 31 ɗin na ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan Banyana Banyana tun bayan da ta fara taka musu leda a 2010.
Ta sanar da cewa za ta yi ritaya bayan gasar ta Wafcon bayan buga wasa fiye da 100.
Aissata Traore (Mali)
Traore ta ci ƙwallo huɗu a wasannin neman shiga gasar lokacin da Mali ta doke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Guinea domin samun gurbi a gasar karon farko tun 2018.
Mai shekara 27 ɗin, ita ce kan gaba wajen cin ƙwallaye a kungiyar Fleury 91 mai buga gasar Premier Ligue ta Faransa a kakar wasa ta 2024-25.
Tana cikin tawagar Mali da ta ƙare a mataki na huɗu a gasar Wafcon ta 2018.
Barbra Banda (Zambia)

Asalin hoton, Getty Images
Banda dodon raga ce.
Ta fi kowane ɗan wasa - maza da mata - jefa ƙwallo a raga a nahiyar Afirka a fagen gasar Olympic bayan ƙwallayen da ta zuba a biranen Tokyo da Paris.
Mai shekara 25 ɗin kuma 'yar wasan gaba ba ta taɓa cin ƙwallo a Wafcon ba saboda ba ta buga gasar 2022 ba sakamakon rikicin jinsi, wanda aka sasanta daga baya.
Banda ce 'yar wasa ta biyu mafi tsada daga Afirka a tarihi, bayan 'yar ƙasar tasu Racheal Kundananji da ta koma Shanghai Shengli na China kan fan 740,000 a watan Maris na 2024.











