Me ya sa ƙungiyoyin Brazil ke taka rawar gani a Club World Cup?

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Miliyoyin magoya bayan ƙwallon kafar Brazil suna cikin farin cikin bibiyar yadda wasa ke wakana a Club World Cup, bayan da ƙungiyoyinsu huɗu na ƙasar suka kai zagaye na biyu wato Botafogo da Flamengo da Fluminense da kuma Palmeiras.

Dukkansu huɗun da suke wakiltar Brazil sun kai zagayen ƴan 16, bayan da suka taka rawar gani a wasannin cikin rukuni.

Tuni wasu ke hasashen cewar wataƙila wata ƙungiya daga Brazil ce za ta lashe Club World Cup a karon farko tun bayan 2012.

Botafogo ta caskara mai rike da champions League, Paris St-Germain, Flamengo kuwa ta yi nasara a kan Chelsea da cin 3-1, duk da ita aka fara ci.

Ita kuwa Fluminense ta riƙe Borussio Dortmund duro, kamar yadda Palmeiras ta yi da Porto.

Ƙasar Amurka ce za ta karɓi baƙuncin yawancin wasannin gasar kofin duniya da za ta yi haɗaka da Canada da Mexico a 2026 da tawagar 48 za ta ɓarje gumi.

Falmeras

Asalin hoton, Getty Images

Me ya sa ƙungiyoyin Brazil ke taka rawar gani?

Tuni dai Atletico Madrid da Porto daga Nahiyar Turai suka yi ban kwana da Club World Cup, yayin da ƙungiyar ƙwallon kafa ta Boca Juniors da kuma River Plate - suka yi ban kwana da wasannin daga Kudancin Amurka.

Sai dai ƙungiya huɗu daga Brazil sun kai zagaye na biyu, ke nan aƙalla ɗaya daga ciki za ta kai zagayen kwata fainal.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Saboda an haɗa wasa tsakanin Palmeiras da Botafogo dukansu daga Brazil da za su fafata a zagaye na biyu ranar Asabar a Philadelphia.

Ita kuwa Flamengo za ta fafata da Bayern Munich ranar Lahadi, yayin da Fluminense za ta fuskanci Inter Milan ranar Litinin.

Ɗaya daga dalilin da ƙungiyoyin Brazil ke taka rawar gani a Amurka shi ne yana yin ƙasar da ake buga gasar, wanda ya yi daidai da yanayin da suke taka leda a ƙasarsu.

Su dai ƙungiyoyin Turai kakawa suke yi da irin zafin da ake yi a Amurka, wanda ba su saba da shi ba.

Har ma kociyan Chelsea, Enzo Maresca da na Manchester City, Pep Guardiola sun yi ƙorafi kan ɗan karen zafin da ake yi a Amurka tun daga ranar da aka fara Club World Cup.

Wani abin da ya sa ƙungiyoyin Brazil ke ƙoƙari shi ne, an fara kakar tamaula ta ƙasar daga watan Maris da ake sa ran ƙarƙarewa a cikin watan Disamba.

Ke nan suna buga wasannin a kan ganiya, yayin da na Turai suke hutu tun bayan kammala gasar ƙasashensu a cikin watan Mayu.

Wasan da PSG ta buga da Atletico Madrid a Pasadena ranar 15 ga watan Yuni, ta yi ne kwana 15 tsakani da ta doke Inter Milan 5-0 ta lashe Champions League a Munich.

Haka kuma da akwai masu horar da tamaula daga Portugal da Argentina da yawa a Brazil, ke nan suna da dabarun buga tamaula da yawa.

Idan ka duba koci ɗan ƙasar Brazil, Filipe Luis mai horar da Flamengo, dukkan masu taimaka masa daga Sifaniya suke, ke nan za a samu dabarun taka leda da yawa.

Ke nan wannan yanayin ya yi daidai da ƙungiyoyin Brazil kan yadda suke taka leda, kuma suna tsakaiyar kakar ƙasarsu da tuni ta yi nisa.

Haka kuma ƙungiyoyin sun riƙe wasu daga cikin fitattun ƴanwasansu, wasu kuwa sun ɗauki sabbin ƴanƙwallo, saboda tunkarar Club World Cup.

Misali, Flamengo ta ɗauki Jorginho, bayan da ya bar Arsenal da kuma Danilo da Alex Sandro daga Juventus da suka ƙungiyar.

Haka ita kuwa Botafogo ta riƙe mai ci mata ƙwallaye, Igor Jesus, wanda sai bayan kammala Club World Cup ta amince ya koma Nottingham Forest.

Flamengo

Asalin hoton, EPA

Ko hakan na nuna cewar Brazil za ta yi abin kirki a gasar kofin duniya?

Dubban magoya baya daga Brazil, sun je Amurka domin su marawa ƙungiyoyinsu baya a Club World Cup.

Haka kuma su ne suka fi yawa da suka je Amurka, inda suke sowa da tafi domin ƙara wa ƙungiyoyinsu ƙwarin gwiwa a lokacin da suke buga wasanni.

Tuni dai Brazil ta samu tikitin shiga gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a 2026 karkashin Carlo Ancelotti.

Wasu na ganin rawar da ƙungiyoyin Brazil ke takawa a Club World Cup, ƴar manuniya ce cewar tawagar Brazil za ta iya yin abin kirki a gasar.

Ƙungiyar Brazil da dukkansu suka kai zagaye na biyu sun haɗa da Palmeiras da Botafogo da Flamengo da kuma Fluminense...a lot of their best players are not Brazilians.

To sai dai yawanci ba waɗanan ƴanwasan ne za su wakilci Brazil a gasar ta kofin duniya da za a buga a baɗi, amma dai idan kasar ta taka rawar gani ba abin mamaki bane.

Kuma kungiyoyin Turai sun farko da yadda na Brazil ke taka leda, hakan ne yasa duk lokacin da suka zo yin wasa suke ankarewa da duk wadda suka haɗu daga Kudancin Amurka.

Waɗanne ne ƙungiyoyin Brazil ɗin?

Fifa Club World Cup

Asalin hoton, Reuters

Flamengo:

Ƙungiyar Brazil ta shiga gasar a lokacin da take kan ganiya, wadda ta ja ragamar babbar gasar tamaula ta Brazil.

Ta kuma samu damar shiga Club World Cup, bayan lashe Copa Liberatodores a 2022, kuma na uku jimilla.

Ta doke Chelsea 3-1 kuma ita ce ta ja ragamar rukunin ba tare da an doke ta ba.

Fluminense:

Ƙungiyar ta Brazil tana yin abin kirki a fannin tamaula, wadda ta ɗauki Copa Libertadores a 2023 kuma a karon farko.

A bara da ƙyar ƙungiyar ta ci gaba da buga babbar gasar tamaula ta Brazil, wadda ta kusan faɗuwa daga wasannin.

Kaɗan ya rage ta wakilci Brazil a Club World Cup a matakin mai buga karamar gasar tamaula ta biyu ta Brazil

A kakar nan tana mataki na shida, bayan wasa 11, kuma tsohon ɗan wasan Chelsea, Thiago Silva shi ne ƙyaftin ɗin ƙungiyar.

Haka kuma suna da ɗan wasan da yake da shekaru mafi yawa a gasar ta Club World Cup, wato mai tsaron raga, Fabio mai shekara 44.

Palmeiras:

Ɗaya daga fitatciyar ƙungiyar ƙudancin Amurka, wadda ta daɗe tana samun nasarori a fannin tamaula a shekara 115 da aka kafa ta.

Ta lashe kofi 57, ciki har da Copa Libertadores uku - kofin da yake da daraja iri ɗaya da Champions League na Turai.

Ita ce suka lashe babban kofin gasar kasar Brazil a 2023.

Daga cikin fitattun ƴanwasan ƙungiyar har da matashi mai shekara 18, Estevao, wanda zai koma Chelsea da zarar an kammala gasar da ake a Amurka.

Haka kuma ƙungiyar ce ta sayar da Endrick ga Real Madrid.

Botafogo:

Ƙungiyar nan ta bayar da mamaki a wasannin da ake yi, bayan da ta doke mai rike da Champions League na Turai, Paris St Germain a karawar cikin rukuni.

Ta mamaye gasar Kudancin Amurka a 2024, wadda ta lashe Copa Libertadores da kuma Brazilian championship.

Sai dai tana fuskantar kalubale a kakar bana, bayan da aka sayi wasu daga cikin fitattun ƴan wasan ƙungiyar.

Koda yake mai ci musu ƙwallaye, Igor Jesus yana ƙungiyar, amma ana cewa zai koma Nottingham Forest da zarar an kammala Club World Cup.