Abin da ya kamata ku sani kan Fifa Club Wold Cup 2025

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Fifa za ta gabatar da gasar cin kofin duniya na ƙungiyoyin tamaula su 32 da aka zaɓo daga nahiya shida da za a gudanar a Amurka, a wani sabon tsari da ya bambanta da na baya.
Nahiyoyin sun haɗa da Asia da Afirka da Arewa da tsakiyar Amurka da yankin Caribbean da Kudancin Amurka da Oceania da kuma Turai.
An tsara fara wasannin da Amurka za ta karɓi baƙunci daga 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin 2025 a filaye 12 a faɗin ƙasar.
Karon farko da aka sauya fasalin gasar da ƙungiya 32 za ta yi tataburza, har da guda huɗun da suka lashe Fifa Club World Cup a baya.
Manchester City ce mai riƙe da kofin, wadda ta ɗauka a karon farko da ta buga gasar a 2023 lokacin tsohon fasali.
Tun cikin watan Maris din 2019 aka sanar da sabunta tsarin yadda za ake buga Fifa Club World Cup, kuma China aka tsara za ta fara shirya wasannin a 2021 daga baya aka soke shirin, saboda ɓullar cutar Korona.
Daga nan Fifa ta amince aka ƙara yawan ƙungiyoyin da za su buga gasar daga nahiyoyi shida a Fabrairun 2023, kuma wata hudu tsakani aka sanar da Amurka a matakin mai masauƙin baƙi a gasar 2025.
Tarihin Fifa Club World Cup

Asalin hoton, Getty Images
An fara gudanar da gasar a 2000 a Brazil kuma Corinthians ce ta fara lashe kofin, bayan nasara a kan Vasco da Gama 4-3 a bugun fenariti a wasan ƙarshe.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Necaxa ta Mexico ce ta uku, sakamakon doke Real Madrid 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a gasar da ƙungiyoyi takwas suka kece raini.
Sai dai ba a ci gaba da wasannin ba daga tsakanin 2001 zuwa 2004, bayan durku shewar kamfanin da Fifa ke haɗakar tallata gasar wato International Sport and Leisure (ISL).
An ci gaba da wasannin a duk shekara tun daga 2005 har zuwa 2023 daga nan aka sauya fasalin gasar da cewar za rinƙa gudanar da ita duk shekara huɗu daga 2025.
Lokacin da aka fara wasannin a 2000 a Brazil ana kiran gasar da sunan Intercontinental Cup da ake yi tsakanin ƙungiyoyin nahiyar Turai da waɗanda suka yi abin kirki a Copa Libertadores, wato daga nahiyar Kudancin Amurka.
A shekarar 2005 aka haɗe wasannin Intercontinental Cup da Fifa Club World Cup Championship daga nan aka sauya sunan gasar zuwa Fifa Club World Cup a 2006.
Daga lokacin duk ƙungiyar da ta zama gwarzuwa, sai a bata kofin Fifa Club World Cup da takardar shaidar Fifa World Champions.
Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe kofin inda ta ɗauka har sau biyar a tarihi a gasar da Corinthians ta fara lashewa a 2000 a Brazil.
Ƙungiyoyin Sifaniya sun ɗauki kofin sau takwas, sai guda huɗu a Ingila da suka lashe Fifa Club World Cup da suka hada da Manchester United da Chelsea da Liverpool da kuma Manchester City.
Manchester City ce ke riƙe da kofin, wadda ta doke Fluminense 4–0 a wasan ƙarshe a 2023.
Ƙungiyoyi da za su buga FIFA Club World Cup 2025

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiya 32 ne za su buga FIFA Club World Cup 2025 a Amurka
Jerin ƙungiyoyin da za su kara a Fifa Club World Cup 2025
- Al Ahly FC (MASARA) – Ta lashe Caf Champions League a 2020/21 da 2022/23 da kuma 2023/24.
- Wydad AC (MOROCCO) – Ta ɗauki Caf Champions League a 2021/22
- Espérance Sportive de Tunis (TUNISIA) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Afirka.
- Mamelodi Sundowns FC (RSA) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Afirka.
- Al Hilal (SAUDIYYA) – Ta lashe kofin Champions League na Asia a 2021.
- Urawa Red Diamonds (JAPAN) – Ta lashe kofin Champions League na Asia a 2022.
- Al Ain FC (HADADDIYAR DAULAL LARABAWA) - Ta lashe kofin Champions League na Asia a 2023/24.
- Ulsan HD (KORIYA) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Asia.
- Chelsea FC (INGILA) – Ta lashe UEFA Champions League a 2020/21.
- Real Madrid C. F. (SIFANIYA) – Ta lashe UEFA Champions League a 2021/22 da kuma a 2023/24.
- Manchester City (INGILA) – Ta lashe UEFA Champions League a 2022/23.
- FC Bayern München (JAMUS) – Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Turai.
- Paris Saint-Germain (FARANSA) – Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Turai.
- FC Inter Milan (ITALIYA) – Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Turai.
- FC Porto (PORTUGAL) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Turai.
- SL Benfica (PORTUGAL) – Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon kungiyoyin Turai.
- Borussia Dortmund (JAMUS) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Turai.
- Juventus FC (ITALIYA) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Turai.
- Atlético de Madrid (SIFANIYA) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Turai.
- FC Salzburg (AUSTRIA) - Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Turai.
- CF Monterrey (MEXICO) – Ta lashe Concacaf Champions Cup a 2021
- Seattle Sounders FC (USA) – Ta lashe Concacaf Champions Cup a 2022
- CF Pachuca (MEXICO) - Ta lashe Concacaf Champions Cup a 2024
- Auckland City FC (NEW ZEALAND) – Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Turai a Oceanic.
- SE Palmeiras (BRAZIL) – Ta lashe Copa Libertadores 2021.
- CR Flamengo (BRAZIL) – Ta lashe Copa Libertadores 2022.
- Fluminense FC (BRAZIL) – Ta lashe Copa Libertadores 2023.
- Botafogo (BRAZIL) - Ta lashe Copa Libertadores 2024.
- CA River Plate (ARGENTINA) - CONMEBOL Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Kudancin Amurka.
- CA Boca Juniors (ARGENTINA) - CONMEBOL Ta samu maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Kudancin Amurka.
- Inter Miami CF (AMURKA) - Mai masaukin baki.
- LAFC (AMURKA) - FIFA Club World Cup wasan cike gurbi.
Yadda aka zaɓo ƙungiyoyin da za su buga FIFA Club World Cup 2025

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiya 32 ne za su kece raini a sabuwar gasar Fifa Club World Cup 2025, an kuma auna ƙwazon ƙungiyoyin da kofunan da suka lashe daga 2021 zuwa 2024 ta hakan aka samu wadanda za su fafata a wasannin a Amurka a 2025.
Nahiyar Afirka - Guda huɗu (CAF). Guda uku sun ɗauki CAF Champions League da daya da ta haɗa maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Afirka.
Nahiyar Asia - Guda huɗu (AFC). Guda uku sun lashe AFC Champions League da ɗaya wadda ta haɗa maki mai yawa a jerin jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin Asia.
Nahiyar Turai - Guda 12 (UEFA). Huɗun da suka lashe UEFA Champions League da kuma takwas da suke kan gaba a yawan haɗa maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin nahiyar.
Yankin Arewa da tsakiyar Amurka da yankin Caribbean - Guda huɗu (Concacaf) Dukkansu huɗun sun samu damar lashe kofin nahiyar na Concacaf.
Yankin Oceania - Guda ɗaya (OFC). Ƙungiyar da ta fi kowacce samun maki a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin a nahiyar.
Yankin Kudancin Amurka - Guda shida (CONMEBOL) Guda huɗu da suka lashe kofin Libertadores sai biyu da suke da maki mai yawa a jadawalin ƙwazon ƙungiyoyin nahiyar.
Mai masaukin baki - Kungiya ɗaya.
Rukunin ƙungiyoyin da za su buga FIFA Club World Cup 2025

Asalin hoton, Getty Images
Group A
- SE Palmeiras (BRAZIL)
- FC Porto (PORTUGAL)
- Al Ahly FC (MASAR)
- Inter Miami CF (AMURKA)
Group B
- Paris Saint-Germain (FARANSA)
- Atlético de Madrid (SIFANIYA)
- Botafogo (BRAZIL)
- Seattle Sounders FC (AMURKA)
Group C
- FC Bayern München (JAMUS)
- Auckland City FC (NEW ZEALAND)
- CA Boca Juniors (ARGENTINA)
- SL Benfica (PORTUGAL)
Group D
- CR Flamengo (BRAZIL)
- Espérance Sportive de Tunis (TUNISIA)
- Chelsea FC (INGILA)
- Los Angeles FC (AMURKA)
Group E
- CA River Plate (ARGENTINA)
- Urawa Red Diamonds (JAPAN)
- CF Monterrey (MEXICO)
- FC Internazionale Milano (ITALIYA)
Group F
- Fluminense FC (BRAZIL)
- Borussia Dortmund (JAMUS)
- Ulsan HD (KORIYA)
- Mamelodi Sundowns FC (AFIRKA TA KUDU)
Group G
- Manchester City (INGILA)
- Wydad AC (MOROCCO)
- Al Ain FC (HADADDIYAR DAULAL LARABAWA)
- Juventus FC (ITALIYA)
Group H
- Real Madrid C. F. (SIFANIYA)
- Al Hilal (SAUDIYA)
- CF Pachuca (MEXICO)
- FC Salzburg (AUSTRIA)
Filayen da za a buga FIFA Club World Cup 2025

Asalin hoton, Getty Images
Kimanin filin wasa 12 ne za a gudanar da wasa 63 a gasar ta Fifa Club World 2025 a faɗin Amurka.
Za a fara da bikin buɗe gasar a filin da ake kira Hard Rock dake Miami, sannan a buga karawar karshe a filin wasa da ake kira MetLife dake New York a New Jersey.
Jerin fili 12 da za a buga Fifa Club World Cup 2025:
- Mercedes-Benz – Atlanta, GA
- TQL – Cincinnati, OH
- Bank of America – Charlotte, NC
- Rose Bowl – Los Angeles, CA
- Hard Rock – Miami, FL
- GEODIS Park – Nashville, TN
- MetLife – New York New Jersey
- Camping World – Orlando, FL
- Inter&Co – Orlando, FL
- Lincoln Financial Field – Philadelphia, PA
- Lumen Field – Seattle, WA
- Audi Field – Washington, D.C.
Kofin da za a lashe a gasar FIFA Club World Cup

Asalin hoton, Getty Images
Za a lashe kofin Fifa Club Worl Cup a 2025, wanda aka sauya masa fasali da za a fara a Amurka a cikin watan Yuni, an kuma gabatar da kofin a Nuwambar 2024, domin duniya ta sheda.
Fifa ce ta samar da kofin da aka kera tare da haɗin gwiwar global luxury jeweller Tiffany & Co..
Za kuma a bai wa duk ƙungiyar da ta lashe kofin a ranar 13 ga watan Yuli a filin wasa na Metlife dake birnin New York New Jersey.
Yadda za a buga FIFA Club World Cup 2025
An raba ƙungiyoyi 32 zuwa rukuni takwas ɗauke da ƙungiya huɗu kowanne.
Duk biyun da suka samu maki mafi yawa a kowanne rukuni, bayan wasa uku-uku, sune za su kai zagaye na biyu, wato su 16.
Daga nan za a fara zagayen ziri ɗaya kwale tsakani ƙungiya 16, wato duk wadda aka ci za ta koma gida, wadda ta yi nasara ta kai zagayen gaba.
Kenan za a samu guda takwas da za su kai zagayen gaba.
Tsakanin kungiya takwas za a yi wasannin kwata fainal, inda za a tantance huɗun da za su kai zagayen gaba na daf da karshe.
Daga cikin huɗun za a buga karawar daf da karshe, wato za a fitar da biyun da za su fafata a zagayen karshe.
A gasar ta Fifa Club World Cup 2025, ba batun buga wasan neman mataki na uku da na huɗu.
Kenan wasan karshe za a buga daga nan a bai wa wadda ta zama zakara kofin Fifa Club World Cup 2025 a karon farko, wanda aka sauya masa fasali..
Ladan da za a bai wa waɗanda za su buga Fifa Club World Cup
Za a raba jimilla ƙudi biliyan ɗaya na dalar Amurka (US$1 billion) tsakanin kungiya 32 da za su buga Fifa Club World Cup 2025.
Wasannin cikin rukuni (kowacce ƙungiya za ta yi wasa uku: Duk wadda ta ci wasa dalar Amurka miliyan biyu ($2.0 million), idan aka yi canjaras dalar Amurka miliyan ɗaya ($1.0 million)
Zagayen ƴan 16: Dalar Amurka miliyan bakwai da ɗari biyar ($7.5 million).
Zagayen kwata fainal: Dalar Amurka miliyan 13 da dubu ɗari da ashirin da biyar ($13.125 million).
Zagayen daf da karshe: Dalar Amurka miliyan ashirin da ɗaya ( $21.0 million)
Wasan karshe: Dalar Amurka miliyan 30 ( $30.0 million).
Wadda ta lashe kofin: Dalar Amurka miliyan arba'in ( $40.0 million).
Haka kuma za a raba dalar Amurka miliyan ɗari biyar da ashirin biyar (US$525 million): tsakanin ƙungiya 32 da za su kara a wasannin.
Sai dai rabon ya banbanta tsakaninin nahoyiyin duniya shida.
Turai: Daga dalar Amurka miliyan sha biyu da dubu ɗari takwas da goma zuwa dalar Amurka miliyan talatin da takwas da ɗari da casa'in ($12.81–38.19 million)
Kudancin Amurka: Dalar Amurka miliyan sha biyar da dubu ɗari biyu da goma ($15.21 million)
Arewa, tsakiyar Amurka da yankin Caribbean: Dalar Amurka miliyan tara da dubu ɗari biyar da hamsin ($9.55 million).
Asia: Dalar Amurka miliyan tara da dubu ɗari biyar da hamsin ($9.55 million).
Afirka: Dalar Amurka miliyan tara da dubu ɗari biyar da hamsin ($9.55 million).
Oceania: Dalar Amurka miliyan uku da dubu ɗari biyar da tamanin ($3.58 million).
Ronaldo ba zai buga Fifa Club World Cup ba

Asalin hoton, Getty Images
Tun farko shugaban Fifa, Gianni Infantino ya e suna tattaunawa kan Ronaldo ko zai buga Fifa Club World Cup.
Ƙungiyar da Ronaldo ke buga wa tamaula, Al-Nassr ta Saudiyya ba ta samu damar shiga gasar ba, sai dai Infantino ya y karin haske cewar watakila ƙyaftin ɗin Portugal ya buga wasannin, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a karshen kakar bana.
To sai dai Ronaldo bai amince da tayin da aka yi masa ba na buga gasar, wanda ya ce zai tsawaita kwantiraginsa a Al-Nassr ta Saudiyya.
Tuni kuma Fifa ta amince ta buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo daga 1 zuwa10 ga watan Yuni, domin ƙungiyoyin da za su buga Fifa Club World Cup su samu damar yin cefane, saboda su taka rawar gani a gasar.
Haka kuma watakila a fuskanci juna tsakani wa da kani, Jude Bellingham na Real Madrid da kaninsa, Jobe Bellingham na Borussia Dortmund, wanda ta ɗauka daga Sunderland, bayan kammala gasar Championship ta Ingila.
Koda yake Real Madrid da Borussia Dortmund ba sa rukuni ɗaya, watakila idan kowacce ta sa ƙwazo su haɗu a wasannin gaba a gasar.










