Yadda aka zaƙulo ƙungiyoyin da za su fafata a Gasar Champions League ta baɗi

Zakarun turai

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Lahadin da ta gabata ce bayan fama da kwan-gaba-kwan-baya a sakamako, ƙungiyoyin Manchester City da Chelsea da Newcastle suka samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun turai ta baɗi.

A ranar Asabar, 31 ga watan Mayun shekarar 2025 ce za a fafata wasan ƙarshe na gasar ta bana, wato gasar ta 2024-2025, inda Inter Milan da PSG za su fafata domin lashe kofin mai matuƙar daraja.

A Ingila, bayan Man City da Newcastle da Chelsea ɗin, akwai Liverpool wadda ta lashe gasar premier league ta bana da Arsenal, sai kuma Tottenham wadda ta lashe gasar Europa, wanda hakan ya sa ƙungiyoyi shida ne za su wakilci ƙasar a gasar ta baɗi.

Daga ƙasar Spain kuwa, akwai ƙungiyoyin Barcelona da Real Madrid da Atletico Madrid da Athletic Club da Villarreal, wato ƙungiyoyi biyar.

A Jamus kuma akwai ƙungiyoyin Bayern Munich da Bayer Leverkusen da Eintracht Frankfurt da Borussia Dortmund, wato ƙungiyoyi huɗu ke nan daga ƙasar.

A ƙasar Italiya, akwai Napoli da lashe gasar Seria A sai Inter Milan da Atalanta da Juventus.

Guraben ƙasashe

Ƙungiyoyi 36 ne za su fafata a gasar ta baɗi daga ƙasashen nahiyar turai, inda wasu ke da wakilai da dama, kamar Ingila mai shida da masu ƙwaya ɗaya tal, da ma ƙasashen da dole sai ƙungiyar da ta lashe gasar ƙasar sai ta buga wasan cike-gurbi.

Ƙungiya ta farko a gasar ita ce Tottenham wadda ta lashe gasar Europa ta bana bayan doke ƙungiyar Manchester United a wasan ƙarshe, wanda ya ba ta gurbi kai-tsaye.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tottenham ta samu wannan nasarar duk da cewa ta ƙare kakar bana ne a matsayin ta 17 a teburin gasar Premier League ta bana.

Ƙungiyoyin da suke saman teburi daga ta ɗaya zuwa ta huɗu a gasar Premier League da La liga da Serie A da Bundesliga duk sun samu gurbi a gasar. Sai gurabe uku da aka ware wa Ligue 1 ta Faransa, da gurbi biyu ga gasar Eredivisie ta Netherland.

Portugal da Belgium da Turkiyya da Czech Republic duk gurbi ɗaya-ɗaya ake ba su domin shiga gasar.

Ƙungiyar da ta lashe gasar ta zakarun turai kuma na sake samun gurbi kai-tsaye. Amma kasancewar a kakar bana duk ƙungiyoyin da za su buga wasan na ƙarshe - Inter Milan da PSG- duk sun samu gurbi, sai aka ba Olympiacos gurbi kai-tsaye ba tare da buga wasan raba-gardama ba.

Haka kuma an ƙara wa ƙasashen da suka fi taka muhimmiyar rawa a gasannin nahiyar turai na bana gurbi. A kakar 2024-2025, Ingila da Spain ne suka fi taka rawar gai, wanda hakan ya sa da ƙungiyoyin da suka zo mataki na biyar a Premier da La liga ma za su samu shiga gasar.

Jimillar ƙungiyoyi 29 ke nan, sauran guraben guda bakwai kuma za a fafata wasannin cike-gurbi ne domin zama ƙungiyoyi 36.

Ƙungiyar Celtic da ta lashe gasar Scotland za ta buga wasan cike-gurbi ɗaya, Rangers da ta zo ta biyu za ta buga wasan raba-gardama uku.

Sai ƙungiyoyi da suka lashe gasannin ƙasashen Northern Ireland da Wales da Republic of Ireland za su fafata wasannin cike-gurbi guda huɗu.

Ƙungiyoyin da suka samu gurbi

Europa

Asalin hoton, Getty Images

  • Tottenham
  • Liverpool
  • Arsenal
  • Manchester City
  • Chelsea
  • Newcastle
  • Napoli
  • Inter Milan
  • Atalanta
  • Juventus
  • Barcelona
  • Real Madrid
  • Atletico Madrid
  • Athletic Club
  • Villarreal
  • Bayern Munich
  • Bayer Leverkusen
  • Eintracht Frankfurt
  • Borussia Dortmund
  • Paris St-Germain
  • Marseille
  • Monaco
  • PSV Eindhoven
  • Ajax
  • Sporting
  • Union Saint-Gilloise
  • Galatasaray
  • Slavia Prague
  • Olympiakos