Napoli za ta gana da Man Utd kan Garnacho, Arsenal ta kwaɗaitu da Mitoma

Daraktan ƙungiyar Napoli Giovanni Manna na shirin ganawa da Manchester United kan yiwuwar cimma yarjejeniya kan ɗan wasan Argentina mai shekara 20, Alejandro Garnacho, wanda ya yi watsi da tayin fam miliyan 40 a watan Janairu daga ƙungiyar ta Italiya. (i paper)
Arsenal ta bi sahun Bayern Munich a farautar ɗan wasan Brighton mai shekara 28 daga Japan Kaoru Mitoma. (Sky Germany)
Ɗan wasan gaba a Sweden, Viktor Gyokeres zai yi bankwana da Sporting a wannan kaka. Matashin mai shekara 26 ana alakanta shi da Arsenal da Chelsea kuma akwai yarjejeniyar ba zai bar ƙungiyar da yake ba kan kasa da fam miliyan 84. (Sky Sports)
Arsenal na son mai tsaron ragar Aston Villa da Argentina, Emiliano Martinez mai shekara 32, domin ya koma ƙungiyar, yayin da ita ma Real Madrid ta kwaɗaitu.(Sun)
Mataimakin manaja a Tottenham, Ryan Mason na cikin wadanda ake fatan ganin ya maye gurbin kocin West Brom. (Talksport)
Leicester City ta cimma yarjejeniya kan ɗan wasan gaba a Faransa mai shekara 18 daga Guinea, Abdoul Karim Traore. (Foot Mercato - in French)
Arsenal na son ɗan wasan Ghana mai buga tsakiya, Thomas Partey ya ci gaba da zama da ita idan kwantiragin da yake kai ya kare, duk da cewa yana samun tayi daga ƙungiyoyi irinsu, Real Sociedad. (football.london)
Napoli ta gabatar da tayin albashin fam miliyan 23 kan ɗan wasan Belgium mai shekara 33, Kevin de Bruyne a yarjejeniyar shekara uku, bayan barinsa Manchester City a wannan kaka. (Fabrizio Romano)
Shugaban Napoli, Aurelio de Laurentiis ya tabbatar da cewa su na farautar De Bruyne. (II Mattino, via Mirror)
Daraktan wasanni a Arsenal, Andrea Berta ya tatauna da ɗan wasan AC Milan, Rafael Leao, mai shekara 25, a kokarin kawo shi Emirates a wannan kaka. (TeamTalk)
Norwich City ta tuntubi kocin Bristol City, Liam Manning kan yiwuwar daidaitawa da shi a sabuwar kaka. (Telegraph - subscription required)
Arsenal ta gabatar da tayin saye ɗan wasan nan mai shekara 21 daga RB Leipzig, Benjamin Sesko. (Fichajes - in Spanish)










