Wa zai lashe takalmin zinare a matakin mafi cin ƙwallaye a Turai a bana?

Golden Shoe

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tuni an lashe kofuna a wasu gasar Turai a bana, an fayyace waɗanda suka yi ban kwana da wasannin kakar nan, an samu wasu da za su buga Champions League a badi.

Kenan abin da ya rage shi ne wanda zai lashe ƙyautar takalmin zinare a matakin wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a kakar nan.

Lokiacin da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ke kan ganiya suke taka leda a Turai, sun karɓi ƙyautar a karo da yawa, haka kuma Thierry Henry da Luis Suarez da kuma Robert Lewandowski duk sun lashe ƙyautar.

Harry Kane ya zama na biyu ɗan Ingila da ya lashe ƙyautar a bara, wanda ya zura ƙwallo 36 a kakarsa ta farko a Bayern Munich, amma zai yi wuya ya ɗauki na biyu a jere a bana.

Tuni an kammala gasar lik a wasu ƙasashen Turai, yayin da saura karawa ɗaya a ƙarƙare gasar Ingila da Sifaniya da Italiya.

Me ake nufi da ƙyautar takalmin zinare?

Ƙyautar takalmin zinare, wadda ake kira a turance, European Golden Boot, ana bayar da ita a duk ƙarshen kaka ga wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a gabaɗayan Turai.

A kan bai wa wanda ya lashe ƙyautar takalmin zinare da aka sassaka. Tun farko ana kiran sunan ƙyautar da Soulier d'Or - a Faransanci ana nufin Golden Shoe - wadda aka kirkira a 1967-68.

Jaridar Faransa ce L'Equipe ta fara gabatar da ƙyautar ta takalmin zinare tun daga kakar 1996-97.

Idan aka ci ƙwallo a manyan gasar Turai biyar, wato Premier League da La Liga da Bundesliga da Serie A da kuma Ligue 1 - ana bayar da maki biyu.

Idan aka zura ƙwallo a raga a matakin gasa ta shida zuwa ta 22 a Turai da ta haɗa har da ta Portugal wato Primeira Liga, ana bayar da maki ɗaya da rabi.

Ana kuma bayar da maki ɗaya da zara an ci ƙwallo a sauran gasar da darajarta ba ta kai ta sauran ba a nahiyar Turai

Su waye ke takara a bana?

Golden Shoe

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙyaftin ɗin tawagar Ingila, Kane zai kawo ƙarshen wa'adinsa a ƴan kwanakin nan, bayan da ya ci ƙwallo 26 a bana a Bundesliga, kenan yana da maki 52 a matakin na huɗu a cikin ƴan takara.

Watakila za a samu sabon ɗan wasan da zai lashe ƙyautar bana a karon farko da ya haɗa da Viktor Gyokeres da Kylian Mbappe da kuma Mohamed Salah da ke ƴan ukun farko.

Ɗan ƙwallon Sporting, Gyokeres zai iya zama gwarzo a bana a matakin na farko ba daga cikin masu buga manyan gasar Turai biyar ba tun bayan 2002.

Ɗan wasan ya ci ƙwallo 39 a kakar nan, shi ne kan gaba da maki 58.5 a gasar tamaula ta Portugal - shi ya sa Arsenal ke zawarcin ɗan ƙwallon.

To sai dai ɗan wasan Sweden ya gama cin ƙwallaye, sakamakon da aka ƙare gasar Portugal - yayin da saura wasa ɗaya ya rage a gaban ɗan ƙwallon Real Madrid da na Liverpool, Salah da za su buga.

Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa yana da maki 58, zai iya haura Gyokeres da zarar ya ci ƙwallo a karawar da Real Madrid za ta karɓi bakuncin Real Sociedad ranar Asabar a La Liga.

Shi kuwa ɗan wasan tawagar Masar, Salah yana da maki 56, idan kuma yana son shan gaban Mbappe, yana bukatar zura ƙwallo biyu ko fiye da haka a raga.

Ranar Lahadi, Liverpool za ta kari bakuncin Crystal Palace a gasar Premier League.

Su waye suka lashe ƙyautar a baya?

Golden Shoe

Asalin hoton, Getty Images

Tun lokacin da aka kirkiri ƙyautar kusan shekara 60, kusan fitattun ƴan wasa ne ke lashe takalmin zinaren.

Mai Ballon d'Or karo takwas, wato Lionel Messi ya ɗauki ƙyautar karo shida, shi kuwa abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo ya lashe karo huɗu.

Ɗan wasan tawagar Portugal, Eusebio shi ne ya fara karɓar ƙyautar a 1968, bayan da ya zura ƙwallo 42 a Benfica, sai ya kara lashewa a mataki na biyu cikin kaka biyar.

Ian Rush shi ne ɗan Ingila na farko da ya lashe ƙyautar, sakamakon da ya ci ƙwallo 32 a Liverpool a kakar 1983/84

A kakar 1996/97 ɗan wasan Brazil, Ronaldo ya karɓi ƙyautar, kuma na farko a kasar da ya yi wannan bajintar.

Ya zura ƙwallo 34 a Barcelona, kenan da maki 68 ya zama zakara.

A shekara 11 tsakani, Ronaldo da Messi suka fara mamaye ƙyautar, inda Ronaldo ya fara shiga tarihi a Manchester United a 2008, shi kuwa Messi ya fara ɗauka kaka biyu tsakani..

A karin wata kaka 11 tsakani ƴan wasan biyu sun lashe ƙyautar ta takalmin zinare karo takwas a tsakaninsu.

A kakar nan ana ganin sabon ɗan wasa ne zai lashe ƙyautar bana.