Shin kuɗi ne ke sa ƴan ƙwallo komawa Saudiyya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
A ƴan shekaru da suka gabata ne fitattun ƴan wasa da ke taka leda a Turai suka fara komawa Saudiyya.
Cikin taurarin da suka koma akwai matasa, da waɗanda shekarunsu suka ja, da waɗanda ma ke kan ganiya a Turai - kamar Benzema da ya koma can shekara ɗaya bayan lashe Ballon d'Or.
Hankalin mutane ya karkata zuwa ƙwallon ƙafar Saudiyya ne bayan Cristiano Ronaldo ya koma Al Nassr a 2022, inda yake karɓar albashin aƙalla dala miliyan 200 kowace shekara – kuɗin da babu wata ƙungiya da ta taɓa biyansa a Turai.
Baya ga Ronaldo, albashin da ƙungiyoyin Saudiyya ke bai wa ƴan wasan da suka sauya daga Turai kan ninka abin da suke ɗauka a ƙungiyar da suka bari, kuma dokar haraji a ƙasar ba mai tsauri ba ce.
A lokuta da dama, burin ɗan wasa shi ne ya buga gasannin da suka fi fice kamar Gasar Zakarun Turai da Gasar Premier da La Liga.
A yanzu dai, da zarar ɗan wasa ya koma wata ƙungiya a Saudiyya, mabiya ƙwallon ƙafa musamman a shafukan sada zumunta na saurin cewa ya fifita kuɗi kan sha'awar buga gasannin da ma sha'awar ƙwallon ƙafa gaba ɗaya.
Sai dai idan aka ji daga bakin ƴan wasan da kan su, da yawan su kan ce ba haka ba ne gaskiyan lamarin.
A baya-bayan nan, mai tsaron ragar Al Ahli Edouard Mendy ya ce ya koma ƙungiyar ne domin ya lashe kofuna, kuma lashe kofin Zakarun nahiyar Asiya da ƙungiyar ta yi a shekarar nan ta shaida aniyarsa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Wasu mutane na saurin yin magana su ce na koma Al Ahli ne saboda kuɗi. Tun lokacin da na bar Chelsea na ce na bar ta ne, na koma ƙungiyar da zan iya lashe kofuna, abin da ba zan iya yi ba a Chelsea a wannan lokacin". in ji Mendy.
Haka zalika, a baya Ronaldo ma ya ce ba don kuɗi ya koma Saudiyya ba, har ma ya ce ƙwallon ƙafa a Saudiyya ta fi wasu manyan gasannin Turai, kuma duk wanda ke kushe shi don yana buga ƙwallo a Saudiyya ya zo ya buga a ƙasar a ga abin da zai yi.
Ronaldo ya ce: "Gasar Saudi Pro League ta fi ta Ligue 1, ba wai ina faɗin haka don a nan nake bugawa ba, su zo nan su gwada bugawa su gani, su yi gudu cikin yanayin zafin rana a nan su gani."
Shi ma Neymar a lokacin da ya koma Saudiyya a shekarar 2023, ya ce ya koma ne don yana neman yin fice a faɗin duniya, don haka komawa wannan yankin na iya ƙara masa suna.
Saɓanin ra'ayoyin waɗannan ƴan ƙwallo, wasu ƴanwasan na cewa maƙudan kuɗaɗen da ake yi musu tayi ne ke sa su komawa ƙasar domin taka leda.
Ɗan wasan Najeriya Odion Ighalo na daga cikin waɗanda suka ce samun kuɗi domin kula da iyali ya fi musu muhimmanci a wannan lokaci na rayuwarsu.
Bayan komawa Saudiyya a 2023, Ighalo ya ce "Idan kana matashi za ka yi ƙwallo ne don sha'awa, ba za ma ka damu da kuɗi sosai ba, amma a shekaru na, na kusan yin ritaya''.
''Ba zan fito na ce ''don sha'awa nake ƙwallo yanzu ba, kuɗi nake nema", in ji shi.
'Da wuya a guje wa kuɗi'
Huɗu daga cikin jerin ƴan wasa 10 da suka fi albashi a duniya a 2024 da mujallar Forbes ta fitar na taka leda ne a Saudiyya a lokacin.
Ƴan wasan su ne Ronaldo da Benzema da Neymar da kuma Sadio Mane.
A baya-bayan nan dai Bruno Fernandes da Kevin De Bruyne suka fifita zama a Turai.
Yayin da Bruno ya tsaya a Manchester United shi kuwa Kevin De Bruyne ya koma Napoli ne, duk da tayin maƙudan kuɗaɗen da aka yi musu a Saudiyya.
Sai dai masana harkokin wasa kamar tsohon ɗan wasan Liverpool Jamie Carragher ya ce ƙungiyoyin Saudiyyan na yi wa ƴan wasa tayin kuɗaɗen da ba za su iya kawar da kai ba.
"Ba wai ina ƙasƙanta ƙwallon Saudiyya ba ne, amma ina tunanin kuɗin ne ke sa ƴan wasa ke komawa ƙasar kuma abu ne da kowa ya sani". in ji Carragher.
Carragher ya ce Saudiyya na da arziƙin ɗaukar kowane ɗan wasa da take sha'awar ɗauka.











