Tsakanin Turai da Kudancin Amurka wa ya fi ƙwarewa a taka leda?

Usman Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Gasar Fifa Club World Cup da ake yi a Amurka ta yi nisa, domin an kusa kammala wasannin rukuni daga nan a fara zagayen ƴan 16.

Duk da cewa ana samun ƙorafe-ƙorafe a gasar da suka haɗa da rashin cika sitadiya da zafin rana da sauransu, hakan bai hana ƙungiyoyin da suke buga gasar sun taka leda mai ƙayatarwa ba.

A karon farko ƙungiya 32 ke fafatawa a sabon fasalin Club World Cup da ya haɗa da 12 daga Nahiyar Turai da shida daga Kudancin Amurka da biyar daga Arewacin Amurka da huɗu daga Afirka da huɗu daga Asia da ɗaya daga Nahiyar Oceania.

Tun farko an yi hasashen cewar ƙungiyoyin Turai ne za su mamaye wasannin, saboda ƙarfin tattalin arzikin gasannin da suke bugawa da ingancinsu da fitattun ƴan ƙwallon da take da su.

To sai dai ba haka abin yake ba, bayan da aka yi wasa bibiyu a cikin rukuni, an samu sakamakon da suka bayar da mamaki.

Daga ciki, akwai ƙungiyar Botafogo ta Brazil da ta yi nasara a kan Paris St German mai riƙe da Champions League da 1-0.

Chelsea, wadda ta kashe kusan €1.5 billion a kaka ukun da suka gabata ta sha kashi a hannun ƙungiyar Rio de Janiero wato Flamengo, inda ƙungiyar ta Brazil ta doke mai buga Premier League da ci 3-1.

Haka kuma an ci gaba da samun sakamakon ban mamaki da ƙungiyoyin Kudancin Amurka ke samu a Fifa Club World a Amurka, hakan ya sa ake ta tafta muhawara kan wacce Nahiya ce kan gaba wajen iya taka leda tsakanin Turai da Kudancin Amurka?

Da farko dai ana kashe ɗan karen ƙudi wajen sayen ƴan wasa da gudanar da gasar ƙasashen Turai da ladar da ƙungiya za ta samu da kuma ingancin wasannin da yake burge masu bibiya sau da kafa.

Idan aka auna a matsakaicin ƙudin da ƙungiya ke biyan ƴan wasa daga 12 da suke buga Club World Cup ya kai €737 million.

Babu wata Nahiyar da ta kusan kamo Turai a yawan kashe ƙudi haka a harkar tamaula.

Sai Kudancin Amurka mai €154m, sannan Asia mai €60m, Arewacin Amurka ya kai €58m, Afirka kuwa ya kama daga €30m, yayin da Oceania, wadda take da ƙungiya, Auckland City matsaikaicin kuɗin da take biyan ƴan wasa ya kama €5m.

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

To sai dai ana bibiyar tamaula tsakanin magoya baya a Nahiyar Turai da Kudancin Amurka, sannan kowacce takan samar da fitattun ƴan wasan da suke fice a nahiyar da kuma duniya a fannin taka leda.

Wannan yana biyo bayan zuba hannun jari da bunƙasa wuraren wasan tamaula da gasa mai inganci da kayatarwa musamman a Nahiyar Turai.

Ga wasu jerin hujjoji a ƙwazon tamaula tsakanin Nahiyar Turai da ta Kudancin Amurka

Wasu abubuwan da Nahiyar Turai take bugun ƙirji da su

Yawan lashe gasar Kofin duniya:

Nahiyar Turai ta lashe kofin duniya guda 12, idan ka kwanta da tara da Kudancin Amurka ta ɗauka a tarihi.

Karfin kungiyoyi:

Ƙungiyoyin Turai, musammam masu buga gasar English Premier League da Spanish La Liga da Bundesliga ko Serie A, sune suka mamaye lashe Champions League da kuma Club World Cup a tarihi.

Zuba jari da bunƙasa wasan tamaula:

Nahiyar Turai tana zuba kuɗi da hannun jari a fannin cin gaban ƙwallon kafa ta matasa tun daga tushe, hakan ya sa ƙungiyoyinsu ba sa rasa ƴan wasan da za su buga musu tamaula, kuma masu inganci da ƙwarewa a manyan ƙungiyoyi.

Babbar gasa mai matsayi da daraja:

Gasar wasan Turai uana da yanayi mai ƙarfi a wasannin da ake yi, wanda mutane da yawa suka yi imanin tana da inganci da ƙayatarwa, hakan ya kan sa tawagar ƙasa kan yi ƙoƙari, duk lokacin da ta je babbar gasar tamaula ta duniya.

Abin da Kudancin Amurka ke tunƙaho da su

Tana da tarihin tamaula mai ƙarfi:

Kudancin Amirka na da tarihin ƙwallon ƙafa, tare da fitattun ƴan wasa irin su Pele da Maradona da Messi da sauransu da suka fito daga Kudancin Amurka.

Ana matukar ƙaunar tamaula a Ƙudancin Amurka:

Kaunar ƙwallon kafa a Kudancin Amurka kamar alada ce mai karfi, yadda ake kishin kulob da yadda ake ciki filayen wasa da samar da yanayi mai kayatarwa a lokacin da ake manyan wasanni.

Samar da ƴan wasa masu hazaka:

Kudancin Amurka na ci gaba da samar da ƴan wasa masu hazaka na musamman, amma yawancin 'yan ƙwallon suna ƙaura zuwa Turai tun suna ƙanana, suna yin tasiri mai ƙarfin a wasannin Turai, yayin da ake rashi daga Kudancin Turai.

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Idan za mu yi lissafin yawan samun maki a Club World Cup da ake bugawa a Amurka, Kudancin Amurka ce kan gaba da wasa bibbiyun da aka buka daga lokacin da aka haɗa wannan rahoton.

Mai biye da ita sai Nahiyar Turai, sannan sauran da suka bi baya a yawan haɗa maki a Club World Cup a bana.

Tsakanin ƙungiya shida daga Kudancin Amurka, Botafogo ta samu maki shida, Flamengo maki shida, Fluminense maki huɗu, River Plate maki huɗu, Palmeiras maki huɗu da kuma Boca Juniors mai maki ɗaya, kenan jimilla maki 4.1.

Duk da Nahiyar Turai tana da ƙungiya 12 dake wakiltarta, tana da maki 48, idan kayi jimilla zai kai 4.00, kenan Kudancin Amurka ce kan gaba.

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ke nan za a samu ƙungiyoyin Kudancin Amurka da yawa da za su kai zagayen ƴan 16, in ban da Boca Junior da ba ta yin ƙoƙari daga cikinsu.

Afirka ce ta uku a ƙoƙari a Club World Cup mai matsakaicin maki 1.75, inda Mamelodi Sundowns ta hada maki huɗu, sai Esperance Tunis mai maki uku da Al Ahly da Wydad Casablanca da ba su sami maki ko ɗaya ba daga wasa biyu a cikin rukuni.

Nahiyar Kudancin Amurka mai ƙungiya biyar ta samu matsaikacin maki 1.20, inda ƙungiyar Lionel Messi, Inter Miami ta samu maki uku daga shidan da suke kasa.

Nahiyar Asia ce ta biyar da maki 0.50, inda ƙungiyar Saudiyya, Al-Hilal ta samu maki biyu daga karawa biyu.

Ta karshe ita ce Nahiyar Oceania mara maki, wadda aka ɗurawa ƙungiyar New Zealand ƙwallo 16.

Daga karshe: Yayin da Kudancin Amirka ke da al'adar son ƙwallon ƙafa sau da kafa da kuma samar da 'yan wasa na musamman ƴan baiwa, Turai a halin yanzu tana kan gaba ta fuskar ingancin gasa, mai ɗan karen farin jini da kayatarwa.