Arsenal ta fara zawarcin Barcola, Tottenham na neman Eze

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan gaban Paris St-Germain ɗan ƙasar Faransa Bradley Barcola, mai shekara 22, wanda Bayern Munich da Liverpool ke nema. (L'Equipe)
Tottenham za ta nemi ɗaukar ɗan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 26, bayan da ta yi rashin nasara a zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo sakamakon tayin sama da fam miliyan 60 da Manchester United ta gabatar a kan ɗan wasan mai shekara 25. (Talksport)
Ɗan wasan bayan Liverpool ɗan ƙasar Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa, ya ki amincewa da sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta gabatar. (Guardian)
Newcastle na tattaunawa da Burnley kan cinikin golan Ingila James Trafford mai shekara 22. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan Borussia Dortmund ɗan ƙasar Ingila Jamie Gittens yana jan hankalin Bayern Munich duk da cewa ɗan wasan mai shekara 20 ya ƙulla yarjejeniyar fatar baki da Chelsea. (Sky Germany)
Juventus ta shirya miƙa dan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25, da kuma ɗan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 27, a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan Ingila Jadon Sancho mai shekara 25 daga Manchester United. (Gazzetta dello Sport)
Barcelona na daf da kammala cinikin ɗaukar matashin ɗan wasan gaban FC Copenhagen ɗan ƙasar Sweden Roony Bardghji, mai shekara 19 a kan farashin fam miliyan biyu. (Sky Sports)
Har yanzu Monaco ba ta cimma yarjejeniya da tsohon ɗan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 32 ba, duk da rahotannin da wasu ke yaɗawa cewa an cimma matsaya. (Sky Sports)
Ɗan wasan baya na ƙasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21, zai kammala gwajin lafiyarsa ranar Talata kafin ya koma Liverpool daga Bournemouth.(Athletic)
Real Madrid za ta buƙaci sama da fam miliyan 77 kan ɗan wasan Brazil Rodrygo, mai shekara 24, wanda ake alakanta shi da komawa gasar Premier League ta Ingila. (Cadena Ser)
Nottingham Forest ta cimma yarjejeniya ta kusan fam miliyan 19 da Juventus kan ɗan wasan gaban Amurka Timothy Weah mai shekara 25 da kuma ɗan ƙasar Belgium Samuel Mbangula, mai shekara 21. (ESPN)
Hamshaƙin ɗan kasuwan nan John Textor, wanda yanzu haka ya sayar da hannun jarinsa na kashi 43% a Crystal Palace kan kuɗi fam miliyan 190, yana tunanin siyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sheffield Wednesday. (The Star)










