Ƴanwasan Premier biyar da kwalliya ta biya kuɗin sabulu a cinikinsu

....

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da aka rufe kasuwar musayar ƴanwasa da aka buɗe gabanin fara gasar Club World Cup, ƙungiyoyi da dama da za su halarci gasar sun yi sayayya domin tunkarar gasar.

A tarihin ƙwallon ƙafa akan samu sayayyar da kwalliya ke biyan kuɗin sabulu, yayin da wasu kuma take kasa biya.

Lokaci zuwa lokaci akan bude kasuwar musayar ƴanwasa domin ƙungiyoyi su zaɓa su darje, iya kuɗinka iya shagalinka.

Kan haka ne muka zaƙulo muku wasu sayayya da aka taɓa yi a gasar Premier da kwalliyarsu ta biya kuɗin sabulu, kuma har yanzu ake tunawa da su.

...

Asalin hoton, Getty Images

Robinho (Real Madrid zuwa Manchester City)

Robinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Robinho

Manchester City ba za ta taɓa mantawa da sayen wannan ɗan wasa ba.

Ƙungiyar Chelsea ta jima tana hanƙoron ɗan wasan wasan gaban na Brazil da Real Madrid, to amma Manchestre City ta yi nasarar ɗaukarsa kan fam miliyan 32.5, a matsayin ɗan wasa mafi tsada da aka saya a Birtaniya a lokacin.

Ɗan wasan ya zura ƙwallonsa ta farko a Premier a karawarsa ta farko da Chelsea.

Andriy Shevchenko (AC Milan zuwa Chelsea)

Andriy Shevchenko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Andriy Shevchenko

A lokacin da Chelsea wadda ta lashe Premier karo biyu a jere a 2006 ta ɗauki Andriy Shevchenko, ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴanwasan gaba mafiya ƙwazo a duniya.

Ɗan wasan ya taimaka wa Chelsea wajen samun nasarori masu yawa, a lokacin da ya taka mata leda.

To amma duk da wasansa na faro a ƙungiyar ya ci ƙwallo a wasansu da Liverpool a gasar Community Shield, Shevchenko ya fuskanci tarin ƙalubale daga takwaransa na ɗan wasan gaban ƙungiyar na lokacin, Didier Drogba

Alan Shearer (Blackburn Rovers zuwa Newcastle United)

Alan Shearer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alan Shearer

Alan Shearer ya lashe takalmin zinare a 1995 lokacin da ya zura ƙwallo 34 tare da taimaka wa Blackburn Rovers lashe kofin a shekarar.

Daga nan Newcastle ta saye shi kan fam miliyan 15, inda kuma ya zama wanda ya fi kowa zura ƙwallo a tarihin ƙungiyar, to amma duk da haka bai taɓa ɗauar kofi a ƙungiyar ba.

Mesut Ozil (Real Madrid zuwa Arsenal)

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mesut Ozil

Kasancewa ya gina kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan tsakiya mafiya kyau a duniya a Real Madrid, Mesut Ozil ya ja hankalin Arsenal, wadda ta ɗauke shi kan fam miliyan 42.

Ɗan wasan ɗan asalin Turkiyya ya taka muhimmiyar rawa a Arsenal, sai dai bayan tafiyar Arsen Wenger a 2018, ɗan wasan ya fara samun saɓani da ƙungiyar.

Wayne Rooney (Everton zuwa Manchester Utd)

Wayne Rooney

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wayne Rooney

Wayne Rooney ya kasance matashin da ya bayar da mamaki tun a gasar Euro ta 2004, inda ya ƙara kan ƙoƙarin da yake yi a Everton a lokacin yana shekara 16.

Daga nan ƙungiyoyi suka fara rububinsa, sai dai a ƙarshe Machester United ta samu nasarar mallakarsa kan fam miliyan 27, kudi mafi tsada da aka sayi matsahin ɗan ƙwallo a lokacin.

Rooney ya taimaka wa United lashe kofunan Premier biyar da na Gasar Zakarun Turai, kafin a 2017 ya zama wanda ya fi kowa cin ƙwallo a United bayan da ya zura 253.