'Babu riba, amma na kasa dainawa' – Matashin da cacar ƙwallo ta hana sakat

Asalin hoton, Getty Images
Kullum yana cikin tashin hankali da damuwa da lissafin yadda zai samu nasarar cinken da ya yi na wasannin ƙwallon ƙafa da ake bugawa domin ya samu kuɗaɗen kashewa, Musa yanzu ya fara zama abin dariya da tausayi a unguwar da yake zama a birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Ga duk wani dangin da suke da ɗan'uwa matashi wanda ya taso cikin ƙwarewa wajen iya murza leda, babban burinsu shi ne wata rana su kalle shi a talabijin, lamarin da ke jefa farin ciki da alfahari.
A arewacin Najeriya da zarar matashi ya tafi kudancin ƙasar, akan fara tunanin cewa ya fara taka matakin cikar burinsa.
Sai dai ba haka lamarin yake ba a wajen Musa, wanda maimakon zuwan Legas ya kusantar da shi zuwa ga zama ƙwararren ɗanwasa da ƴan'uwansa za su yi alfahari, sai wata ƙaddarar ta riga fata, wadda yanzu haka ta jefa shi cikin da-na-sani da damuwa.
Musa ya taso ne da iya ƙwallon ƙafa, har aka yi tunanin zai zama fitaccen ɗan ƙwallo da za a riƙa gani a duniya. Hakan ya sa ya koma jihar Legas da ke kudancin ƙasar domin cigaba da buga ƙwallo, da tunanin daga can zai bar ƙasar domin cika burinsa.
Amma maimakon samun ƙarin ƙwarewa da damar tafiya ƙasar wajen, sai ya koyo yadda ake buga cacar ƙwallon ƙafa, harkar da a cewarsa, "asara ta fi yawa a ciki." Yanzu Musa ya zama fitacce kuma babban ɗan cacar ƙwallon ƙafa, wanda duk da bai cika ci ba, ya kasa bari.
Ya ce shi dai ya shiga, amma ko maƙiyinsa ba zai masa fata ya shiga harkar ba, "domin akwai wahalar dainawa idan aka fara."
Fara cacar ƙwallo
A game da yadda ya shiga harkar cacar ƙwallon ƙafa, Musa ya ce, "ni ɗan ƙwallon ƙafa ne sosai. Domin a unguwar da na taso, ina cikin zaratan matasan da ake nunawa ake tunƙaho da su idan ana maganar murza leda.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
“Na yi tunanin ƙwallo ce za ta canza rayuwata, sai na tsinci kaina a cacar ƙwallon, maimakon bugawa," in ji shi.
Ya ce wani abokinsa ya shigar da shi harkar a wasu shekarun da suka gabata lokacin yana ganiyarsa a buga ƙwallon ƙafa, inda saboda ƙwarewarsa tun yana ƙarami ya fara zuwa jihohin Najeriya.
"Har Jamhuriyar Nijar na je buga ƙwallon ƙafa. Amma a jihar Legas na koya buga cacar ƙwallo. Watarana wani abokina ya ce in raka shi wani shago, muna isa sai aka ba shi kuɗi naira 14,000, na tambaye shi, sai ya ce ai cacar ƙwallo ya buga, sai na ce masa yaya ake yi? sai ya faɗa min zan cinki yadda za ta kaya ne a wasanni, idan na yi daidai sai a ba ni kuɗi."
Ya ce tun a lokacin ne abokin nasa ya faɗa masa cewa idan ya fara akwai wahalar dainawa, amma Musa ya ƙeƙashe ƙasa cewa shi dai allambaran zai riƙa bugawa yana samun ƴan kuɗaɗe.
Musa ya ce a lokuta da dama mutane suna fara shiga cacar da sa'a, domin, "nima kuwa sai na fara da sa'a. A shekarar 2009 na fara, inda na samu naira 18,000 a karon farko, na biyu kuma na samu naira 6,000, na uku kuma na samu naira 1,000, daga nan kuma sai da na daɗe ban ci ba," in ji Musa wanda ya yi zargin cewa yawancin mutane idan suka shiga harkar suna fara ci, amma da zarar sun fara shiga dumu-dumu, sai su daina ci.
Riba ko asara?
Musa ya ce bayan ya koma jihar Kaduna sai ya cigaba da bugawa, wani lokacin ya ci, wani lokacin kuma bai ci ba.
Ba Musa ba ne kaɗai wannan lamari yake ci wa tuwo a ƙwarya, domin cacar tana cinye kuɗaɗen matasa.
Shi ma wani wanda ake kira Ƴanbiyu, ya daɗe yana buga cacar, inda ya ce lamarin ya masa katutu, amma ya kasa dainawa.
Ya ce, "duk da cewa ba wani riba muke samu ba, na kasa fahimtar me ya sa na kasa dainawa. Amma ina addu'ar na kusa dainawa.
Bayan shiga damuwa da rashin tabbas da cacar ke jefa matasa, har ƙuncin rayuwa da ke iya jawo kashe kai cacar na jawowa.
Musa ya ce asarar ta fi yawa, sannan matsalar da ta jefa shi tana da yawan gaske.
"Cacar ta kusa kashe min aurena. Na sha yunƙurin dainawa, amma abin ya ci tura. Har rantsuwa na sha yi cewa zan daina, amma sai in koma."
Ya ce lokacin da yake neman aure an faɗa wa iyayen matarsa cewa yana caca, "amma da ƙyar na samu na tsallake wannan. Sannan bayan mun yi aure na taɓa mantawa da tikiti a aljihuna, matata ta gani, ta je ta faɗa a gidansu. Nan ma muka zauna na ce na daina na ba su haƙuri. Amma gaskiya ban daina ba."
Amma ya ce yanzu a kullum idan zai je buga cacar, yana tunawa da nasihar mahaifinsa, wanda hakan ya sa, "nake roƙon Allah ya ba ni ikon dainawa."
Cacar ta game duniya
A wata ƙididdiga da aka yi game da irin kuɗaɗen da aka kashewa a duk shekara duniya, an gano cewa biliyoyin fam ne suke yawo a harkar caca.
Duk da cewa ana cacar a wasu wasannin daban a duniya, yanzu cacar ta fi ƙamari a ƙwallon ƙafa, lamarin da ke barazana ga nishaɗin da ake samu a ƙwallon, sannan masana suke fargabar hakan na sa ƴanwasa da ƙungiyoyi suna aikata abin da ƴan cacar suke so.
Daraktan ƙididdigar cacar wasanni a cibiyar Sportradar, Darren Small ya bayyana a wani rahoton BBC cewa ana hada-hadar kuɗi tsakanin $700bn zuwa $1tn (wato £435bn zuwa £625bn) a duk shekara a cacar wasanni.
Kuma kashi 70 na hada-hadar a ƙwallon ƙafa ake yi, kamar yadda rahoton ya nuna.










