PSG ta ajiye Dembele a wasan da za ta fuskanci Arsenal a Emirates

Asalin hoton, Getty Images
Paris St Germain ta ajiye Ousmane Dembele a Champions League da za ta kara da Arsenal a Emirates ranar Talata.
Ɗan wasan tawagar Faransa ya ci ƙwallo huɗu a wasa shida a Ligue 1 a PSG a bana, ya buga wasan da suka ci Girona 1-0 a Champions League.
Wasu rahotannin na cewar ɗan wasan mai shekara 27 ya nuna fushinsa ga koci, Luis Enrigue, bayan da aka sauya shi a wasan da PSG ta doke Rennes 3-1 ranar Juma'a.
''Duk wanda ba zai yadda da abinda aka yi ba ko ba zai martaba abinda ake bukata daga wajensa ba, kenan bai shirya buga mana tamaula ba,'' in ji Enrigue.
''Ina son dukkan ƴan wasa na su kasance kan ganiya, saboda haka na ɗauki matakin ajiye shi, ya zama ladabtarwa, wannan yana daga cikin aiki na, domin samun nasarori.''
''Irin wannan matakin yana da wuya, amma ya zama wajibi, kuma na amince da ɗaukar wannan hukuncin, domin shi ne ci gaban PSG.''
Dembele tsohon ɗan wasan barcelona shi ne fitatce a PSG, wanda ya maye rawar da Kylian Mbappe ke takawa a ƙungiyar, wanda ya koma Real Madrid a bana.
Wasa da aka buga tsakanin Arsenal da PSG:
A kakar 2016/2017
Champions League ranar Laraba 23 ga watan Nuwambar 2016
- Arsenal 2 - 2 Paris St-Germain
Champions League Tu 13Sep 2016
- Paris St-Germain 1 - 1 Arsenal
A kakar 1993/1994
Euro Cup Winners Cup ranar Talata 12 ga watan Afirilun 1994
- Arsenal 1 - 0 Paris St-Germain
Euro Cup Winners Cup Tu 29Mar 1994
- Paris St-Germain 1 - 1 Arsenal
Wasannin Champions League da za a kara ranar Talata:
- Red Bull Salzburg da Brest
- Stuttgart da Sparta Prague
- Arsenal da PSG
- Barcelona da Young Boys
- Bayer Leverkusen da AC Milan
- Borussia Dortmund da Celtic
- Inter Milan da Red Star Belgrade
- PSV da Sporting
- Slovan Bratislava da Manchester City










