Me ya hana Lamine Yamal lashe kyautar Ballan d'Or?

Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Matashin ɗanwasan Barcelona, Lamine Yamal na dab da sauya tarihin ƙwallon ƙafar duniya.

Yamal mai shekara 18 shi ne ya zo na biyu a takarar kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafar duniya ta Ballon d'Or.

In da a ce ya lashe kyautar a bikin da aka yi a nirnin Paris a farkon makon nan, da ya zama ɗan wasa mafi ƙanƙantar shekaru da ya lashe gasar.

Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele - na PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin ɗan wasa na Ballon d'Or karo ne biyu a jere.

Lamine Yamal, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya ƙwallon ƙafa, musamman matasa.

Me ya sa Yamal ke da farin jini?

Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Cikin gomman shekaru, duniya ta ɗauka cewa zama fitacce a fagen ƙwallon ƙafa na buƙatar jajircewa da sadaukarwa.

A wani jawabi da ya yi bayan lashe kyautar Ballon d'Or, Lionel Messi ya ce ''sakamkon aiki tare ne''.

Haka shi ma Cristiano Ronaldo ya ce jajircewa da sadaukarwa ce ta kai shi ga matsayin.

Sai dai saɓanin waɗannan, duk da nuna ƙuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen ƙwallon ƙafa ba.

A baya ya bayyana cewa: "Ina da burin samun Ballon d'Or masu yawa. Kuma idan har an same su ba, to sai in ni na so."

Wannan ba irin ƙoƙarin Messi ko jarumtar Ronaldo ba ne. Wani abu ne daban, wanda za iya cewa ƙaddararsa ce a haka.

'Rayuwar shaƙatawa'

Lamine Yamal ya je hutun bazararsa a Monaco, tare da gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa, sannan ya ziyarci hutun shaƙatawa tare da Neymar - ɗan wasan da a baya shi ma ya samu farin jini da soyayyar magoya bayansa.

Ƴan wasan biyu sun ce shaƙatawa ba laifi ba ne, matsawar suna aikinsu yadda ya kamata, ba tare da tarnaƙi ba.

A lokacin waɗannan bukukuwan, Lamine Yamal ya fi kama da mawaƙi, maimakon ɗan wasan ƙwallon ƙafa.

Yana rayuwa lokaci guda da fitaccen marubucin waƙoƙin nan Ba'amurke, Sombr, wanda ke dandalin TikTok ya ɗaga darajar waƙoƙinsa.

Tasirin shafukan sada zumunta

Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Bayyanar Lamine Yamal a lokacin da shafukan sada zumunta ke tsaka da tashe ya taimaka masa wajen ɗaga sunansa a duniya.

Yakan yawaita wallafawa abubuwan da suka shafi rayuwarsa a shafukansa na sada zumunta, lamarin da ya sa magoya bayansa ke jin sun san shi abubuwa da dama game da shi fiye da fili.

Wannan abu ya sa ya zama abin koyi ga matasan Kataloniya, saboda yadda yake kafa tarihi.

Sannu a hankali matashin ɗan wasan na ci gaba da samun karɓuwa tsakanin matasa a faɗin duniya.

Me ya hana Yamal lashe kyautar Ballan d'Or?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matasa da dama sun so Yamal ya lashe Ballon d'Or a wannan shekara, musamman irin ƙoƙarin da ya yi a bara, da kuma lashe kyautar gwarzon matashin ɗan'wasa da ya yi a bara.

Kuma rashin samun kyautar ba ta yi wa matasa da dama daɗi ba, to ko me ya hana shi lashe kyautar?

Bashir Hayatu Jantile mai sharhi ne kan al'amuran wasanni ya kuma ce abin da ya sa ɗan wasan bai lashe kyautar ba shi ne rashin yin abin da zai ba shi damar lashe kyautar.

''Idan ka duba har yanzu akwai sauran tafiya a gabansa, yanzu ya fara, yanzu ya shigo, yanzu kuma yake ƙoƙari'', in ji shi.

Masanin wasanin ya ce har yanzu ɗan wasan na ciin rukunin yarinta, kuma har yanzu bai cika mizanin da zai sa ya samu kyautar ba.

Jantile ya ce duka da cewa Yamal na kan hanyar lashe kyautar, ya lissafo wasu abubuwan da suka hana shi lashe kyauta a bana kamar haka:

  • Cin Kofin Duniya
  • Cin Kofin Zakarun Turai
  • Ɗaukar Kofin yankin ƙasashe
  • Cin ƙwallaye masu yawa
  • Taimaka wa a ci ƙwallaye masu yawa

Jantile ya ce cikin duka waɗannan babu ɗaya da Yamal ya samu a wannan shekara, amma dai ya ce yana kan turbar samun hakan.

Me ya kamata Yamal ya yi don lashe Ballon d'Or?

Bashir Jantile ya ce abin da ya kamata ɗan wasan ya mayar da hankali a kan don lashe kyautar a nan gaba.

Masanain wasannin ya zayyano wasu abubuwan da ya ce dole Yamal ya kula da su idan har yana son lashe kyautar kamar haka:

  • Ya ƙara ƙwazo a kan wanda yake yi a baya.
  • Ya kasance mai haƙuri, da kwantar da hankali
  • Ya sanya a ransa cewa ba a hanzari wajen lashe kyautar

Bashin Jantile ya ce Ronaldo sai da ya buga wa ƙungiyoyi daban-daban, sannan ya shafe shekaru masu yawa yana jagorantar Portugal.

''Ya yi Manchester United da Real Madrid da Juventus sannan ya sake komawa United kafin yanzu ya koma Al Nassr ta Saudiyya, sannan ya shafe kusan shekara 10 yana jagorantar Portugal'', in ji shi.

Spain ko Barcelona: Ina ne zai fi ba shi damar lashe kyautar?

Masanin harkokin wasannin ya ce taka leda a Sifaniya ne zai fi ba shi damar lashe kyautar fiye da ƙungiyarsa ta Barcelona.

Akan fifita nasarar da ɗan wasa ya yia ƙasarsa fiye da ƙungiyar da yake taka wa leda, kuma a bayyane take Kofin Duniya na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da zai sa mutum ya lashe kyautar.

Bashir Jantile ya ce idan har Sifaniya ta lashe Kofin duniya a 2026, Yamal zai iya samun kyautar Ballon d'Or.

''Kasancewar a yanzu yadda yake da cikakken gurbi a tawagar ƙasar, babu yadda za a yi Sifaniya ta ci kofin ba tare da ƙwallayensa ba'', in ji shi.

Masanin wasannin ya ce ba shakka ɗan wasan zai iya samun kyautar idan har ya mayar da hankali.