Xavi Alonso: Shin Madrid ta yi wawan-kamu ko zaɓen tumun-dare ne?

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a duniyar ƙwallo a yanzu akwai komawa horas da ƴanwasan ƙungiyar Real Madrid da tsohon ɗanwasanta Xabi Alonso ya yi, wanda ya maye gurbin Ancelotti.
Wannan ya sa wasu suke ganin kamar Xavin bai kai ba musamman ganin yadda ƙungiyar ba ta kan ganiyarta a yanzu, a daidai lokacin da wasu suke ganin yanzu lokaci ne na matasan kociya a duniya, inda suke kwatanta shi da Zidane da Guardiola.
Alonso wanda ya buga wa Real ɗin wasa 236 a matsayin ɗanwasanta a baya, ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku.
Tsohon ɗan wasan na Liverpool da kuma Sifaniya, ya jagoranci ƙungiyar Bayer Leverusen lashe kofin Bundesliga a bara ba tare da an doke shi ko da wasa ɗaya ba - da kuma German Cup.
Alonso wanda yarjejeniyarsa za ta kai har 30 ga watan Yunin 2028, zai maye gurbin Carlo Ancelotti.
Ancelotti ya jagoranci wasansa na ƙarshe a Madrid a ranar Asabar, inda a yanzu zai zama sabon kocin ƙasar Brazil.
Xavi zai iya da Madrid?
Daga cikin tambayoyin da ake yi game da sabon kocin, akwai fargabar da wasu ke yi cewa ɗaukar Madrid za ta masa nauyi, lamarin da wasu ke cewa ba haka ba ne saboda ya san ƙungiyar, sannan ya horar da wata ƙungiya babba, kuma ya samu nasarori.
Alonso ya yi shekara shida a Real Madrid a matsayin ɗanwasa, sannan ya yi aikin horas da matasan ƴanwasan ƙungiyar a shekarar 2018, kafin ya koma Jamus da aikin kociyan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga cikin abubuwan da ya sa ake masa hasasshen samun nasara akwai irin horo da ya samu a lokacin da yake ƙwallo daga wasu ƙwararrun kociya.
Daga cikin masu horas da ƴanwasa da ya yi aiki da su lokacin da yake taka leda akwai: Pep Guardiola da Carlo Ancelotti da José Mourinho da Rafa Benítez.
Suma tsofaffin kociyansa, irin su Ancelotti da da Mourinho sun bayyana cewa Xavi Alonso jagora ne, wanda zai iya horas da ƴanwasa.
A watan Mayun da ya gabata ne da aka fara raɗe-raɗin Xavi Alonso zai maye gurbin Ancelottin, sai shi Ancelottin ya bayyana jin daɗinsa, tare da cewa Xavi zai iya aikin, domin "yana daga cikin ƙwararrun masu horaswa a yanzu."
Tun a shekarun baya Ancelotti ya taɓa cewa yana da burin ganin ɗaya daga ciki Xabi Alonso ko Raul ko Alvaro Arbeloa ya zama kocin Real Madrid.
Sai dai mai sharhn wasanni na BBC, Guillem Balague ya ce akwai aiki babba a gaban sabon kociyan.
Mai sharhin ya ce Alonso zai gaji ƴanwasa da suke buƙatar saiti, musamman a tsakanin ƴanwasan gaban ƙungiyar.
"Zai fuskanci ƙalubale wajen amfani da matasan ƴanwasa irin su Endrick da Arda Guler domin su maye gurbin waɗanda shekarunsu ya ja."
Haka kuma ya ce Alonso zai fuskanci ƙalubale daga magoya bayan Madrid, "waɗanda suka fi son ganin nasarori cikin sauri, da ma ƴanjarida da za su zura ido."
Wane ne Xavi Alonso?

Asalin hoton, Getty Images
An haifa Xabier Alonso a ranar 25 ga Nuwamban 1981, kuma ya fara taka leda ne a ƙungiyar Real Sociedad. Daga ƙungiyar ya koma Liverpool a shekarar 2004, inda ya lashe gasar Champions League a kakarsa ta farko.
A shekarar 2009ya koma Real Madrid, ina ya lashe La Liga da Copas del Rey biyu da Champions League, sannan ya koma Bayern Munich a shekarar 2014, inda ya lashe kofinBundesliga uku da sauransu, kafin ya yi ritaya a shekarar 2017.
Alonso ya lashe gasar Kofin Duniya a shekarar 2010, sannan ya lashe gasar Nahiyar Turai a shekarar 2008 da 2012.
Shi ma mahaifin mai suna Periko tsohon ɗanƙwallo ne, wanda ya taɓa lashe gasar La Liga guda uku - biyu a Real Sociedad, daya a Barcelona - sannan ya buga wakilci tawagar Spain a gasar Kofin Duniya ta 1982.
Tare suka fara ƙwallon layi da kocin Arsenal na yanzu, Mikel Arteta tun suna yara a ƙasar Spain, har suka girma.











