Ƙasashe biyar da za su iya lashe gasar Kofin Afirka ta bana

Kofin AFCON

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wa zai ɗaga kofin AFCON? Morocco da Ivory Coast da Senegal da Aljeriya da Masar ne ke aka fi kyautata wa zato.
    • Marubuci, Ousmane Badiane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
  • Lokacin karatu: Minti 7

Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2025, wadda aka shirya gudanarwa a Morocco daga ranar 21 ga watan Disamba, 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026, tana daga cikin gasannin da ba a iya hasashen wanɗanda za su lashe ba a tarihin gasar.

Tun da aka fara buga gasar a shekarar 1957 ba a taɓa samun gasar da ake hasashen ƙasashe biyar ko shida na iya lashewa ba kamar ta bana.

Baya ga Morocco mai masaukin baƙi, akwai wasu ƙasashe da dama da ake ganin suna kan gaba cikin jerin waɗanda ka iya nasara , wato Senegal da Masar da Ivory Coast da kuma Aljeriya, waɗanda tuni suka samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.

Ɗaya daga cikin abubuwan al'ajabi a gasar cin kofin nahiyar Afirka shi ne yadda ba a iya samun tabbacin ƙasar da za ta lashe ta. A karo na takwas na baya-bayan nan dai an samu zakaru bakwai daban-daban, inda Ivory Coast ce kaɗai ta samu kambi sau biyu daga cikin gasa biyar da suka gabata, a 2015 da 2024.

Morocco: Atlas Lions na neman kafa tarihi yayin karɓar baƙuncin gasar

Morocco

Asalin hoton, Pablo Morano/BSR Agency/Getty Images

Ƙarƙashin jagorancin Walid Regragui, Morocco, ƙasar da ke kan gaba a jerin ƙasashen Afirka a jadawalin FIFA, ta taka rawar gani a fagen ƙwallon ƙafa a duniya a shekarar 2022, inda ta zama tawagar Afirka ta farko da ta buga wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya.

Ba kasancewa a gida ba ne kaɗai abin da ke ƙara wa tawagar Atlas Lions ƙwarin gwiwa ba a gasar bana, amma tawagar na da babban buri na tabbatar da lashe gasar cin kofin ƙasashen Afirka karo na biyu tun shekarar 1976.

A gaban al'ummar ƙasarta, tawagar Morocco na da burin samun makoma irin ta Ivory Coast, wato nasara a gida amma ba tare da fargabar da ta fuskanta a zagayen farko ba.

Amma karɓar baƙuncin gasar ba lallai ba ne ya zame riba ba. A cikin karo 34 da aka gudanar da gasar tun daga shekarar 1957 (ciki har da gasar farko), sau 12 ne kacal ƙasar da ta karɓi baƙuncin gasar ta yi nasara, wato kusan kashi 35% cikin ɗari.

Tun daga 2000, Tunisia (2004), da Masar (2006) da Ivory Coast (2024) ne kawai suka yi nasara a gida.

Masar: Tawagar da aka saba kyautata wa zato

Égypt

Asalin hoton, Haykel Hmima/Anadolu Agency via Getty Images

Ƙasar da ta fi fice a Afirka na da burin lashe kambu na takwas don kawar da baƙin cikin kashin da ta sha a hannun Senegal a wasan ƙarshen gasar 2022.

Ƴan wasan tawagar Masar na da ta haɗin matasa da kuma gogaggu. Wannan garwayen ƴan wasan na ba ta damar taka muhimmiyar rawa a wasannin nahiyoyi a kusan kodayaushe.

Ƙarkashin jagorancin Hossam Hassan, Masar tana wasa da sauri, yayin da ta ci gaba da amfani da dabarun wasa da aka san ta da su.

Omar Marmoush da Mostafa Mohamed su ne misalan 'sabbin jini' a tawagar, yayin da suke ɗaukar darasi daga tauraron tawagar Mohamed Salah wanda ake hasashen zai taka muhimmiyar rawa a gasar bana a Morocco.

Ivory Coast: Elephants sun kama hanyar farfaɗowa

Côte d'Ivoire

Asalin hoton, Getty Images

Bayan da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a gida a shekarar 2024, tawagar Elepahants ta shiga gasar bana a matsayin mai riƙe da kambun gasar. Nan da nan wannan ya sanya ta zama cikin jerin waɗanda ake kyautatawa zaton lashe gasar, wadda ta taɓa lashewa sau uku, ciki har da sau biyu a gasanni biyar na baya bayan nan.

A ƙarƙashin jagorancin Emerse Faé, tawagar Elephants ta isa Morocco da burin ci gaba da riƙe kambunta. Amma akwai almun za ta fuskanci ƙalubale da dama daga wasu ƙasashen.

Tun lokacin da aka fara gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) a shekarar 1957, ƙasashe uku ne kawai suka iya kare kambunsu. Masar ta yi haka a shekarar 1957 da 1959, sannan kuma ta sake yi a 2006, 2008, da 2010. Ghana ta yi nasara a 1963 da 1965, Kamaru a 2000 da 2002.

Senegal, manyan ƴantakara

 Sénégal Pape Thiaw.

Asalin hoton, Getty Images

Senegal, wadda ta lashe kambunta na farko shekara huɗu da suka gabata bayan dogon jira da kuma rashin nasara biyu a matakin wasan ƙarshe (2002 da 2019), ta kasance ƴar takarar da za ta taka muhimmiyar rawa a gasar.

Bayan lashe gasar AFCON 2021, amma an fidda ta da wuri shekara biyu bayan haka, da alama ta fara samun daidaito a ƙarƙashin jagorancin Pape Thiaw, wanda ya gaji Aliou Cissé.

Yayin da tawagar ke ɗauke gogaggun ƴan wasa kamar Sadio Mane da Kalidou Koulibaly da Idrissa Gueye, Lions na Teranga za su iya yin la'akari da cewa ta na da matasan ƴan wasa masu hazaƙa da ke da gogewar yin nisa na gasar nahiyar.

Tawagar Senegal, da ta Morocco, su ne manyan tawagogin Afirka biyu a saman jadawalin FIFA, a matsayi na 18 da 12 bi da bi.

Senegal, wadda ta mamaye rukuninta na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026, za ta dogara kan ci gaban da ta ke samu ta fannin ƴan wasa da don maimaita nasarar da ta samu a 2022.

Algeria

l'Algérie

Asalin hoton, Billel Bensalem / APP/NurPhoto via Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan rashin nasara sau biyu a gasar AFCON na 2021 da 2023 inda aka fitar da ita a matakin rukuni, tawagar Fennecs na son buɗe wani sabon babi a tarihinta na gasar.

Bayan zamanin Belmadi, inda ta yi farin cikin nasara a 2019 sannan kuma ta yi rashin nasara biyu (CAN 2021 da Gasar Cin Kofin Duniya 2022), Algeria ta tunkari CAN 2025 da babban burin: sake kasancewa tawagar ƙwallon ƙafa da ke ƙololuwar wasa a nahiyar.

Domin cimma wannan burin, hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta dogara ga koci Vladimir Petković, ɗa ƙasar Serbia wanda ya yi suna bayan da ya horas da tawagar Switzerland da ta yi gogayya da manyan ƙasashen Turai.

Ƴan wasan da suka lashe gasar cin kofin Afrika a 2019 sannu a hankali sun dusashwewa, suna ba da dama ga sabbin matasan ƴan wasa da suka haɗa da Fares Chaïbi da Houssem Aouar da Rayan Aït Nouri, da Badredine Bouanani.

Aljeriya ta kasance babbar abokiyar hamayya ga tawagogin ƴan wasan nahiyar da dama, wadda za ta iya taɓuka abin kirki a kowace gasa. Idan Petkovic ya sami nasarar daidaita tawagarsa, Fennecs na iya sake zama kamar tawagar da ta mamaye fagen wasan ƙawallon ƙafan Afirka a 2019.

Wace rawa tawagar Najeriya za ta iya takawa a gasar?

Super Eagles

Asalin hoton, NFF/FB

Tawagar Najeriya ta tsinci kanta a rukunnin C a gasar bana inda za ta fafata da Tunisia da Uganda da kuma Tanzania.

Super Eagles dai za ta nemi kawar da baƙin cikin da ta fuskanta a wasan ƙarshen gasar da ta gabata inda ta yi rashin nasara a hannun Ivory Coast a wasan ƙarshe duk da cewa ita ta fara jefa ƙwallo a raga a wasan.

Ƙasar da ke da kambun AFCON guda uku, a shekarun 1980, 1994, da 2013, wanda hakan ya sanya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samun nasara a gasar ta Afirka.

Kasancewa tana da manyan ƴan wasa kamar su Victor Osimhen da Ademola Lookman da ke taka leda a manyan ƙungiyoyin ƙasashen Turai ana ganin cewa ƙasar za ta iya taɓuka abin a zo a gani a gasar bana, duk da cewa dai rashin nasarar da ta yi a yunƙurinta na samun gurbi a gasar cin kofin duniya na 2026 na sanya alamar tambaya kan rawar da za ta iya takawa.

Rahotanni na cewa koci Eric Chelle na shirin ƙara inganta tawagar tasa da wasu sabbin ƴan wasa guda huɗu ko biyar domin tabbatar da cewa ƙasar ta kai bante a Moroko.

Kan gaba cikin jerin sunayen sabbin ƴan wasan da za a iya kira shi ne ɗan wasan baya na Blackburn Rovers Ryan Alebiosu, wanda tsohon ɗan wasan ɓangaren matasa na Arsenal ne kuma a halin yanzu yana taka rawar gani a gasar Championship ta Ingila.

Wani sabon ɗan wasan da aka sanya wa ido shi ne dan wasan tsakiya Ebenezer Akinsanmiro da ke zaman aro a ƙungiyar Pisa daga Inter a gasar Serie A ta Italiya.

Rauni zai hana ɗan wasan Nottingham Forest Ola Aina buga gasar, yayin da Bright Osayi-Samuel ke fama da rashin tagomashi a kungiyarsa ta Birmingham City ta Ingila.

Amma duk da haka ba za a iya cire rai cewa Super Eagles za ta taka rawar gani a gasar ba, saboda ɗimbin tarihin da ta ke da ita a gasar, kuma ana ganin ƴan wasan za su zo da niyyar huce fushin rashin samun gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2026.