Afcon 2025: Abin da kuke son sani kan gasar da za a yi a Morocco

Asalin hoton, Getty Images
Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin tamaula na Afirka.
Wannan shi ne karon farko tun bayan 1988 da Morocco za ta karɓi baƙuncin wasannin babbar gasar tamaula ta duniya da take fatan gudanar da bikin da zai ƙayatar da duniya.
A wannan lokacin hankulan masu bibiyar tamaula zai koma kan ƙasar da take Arewacin Afirka, wadda take cikin haɗakar gasar kofin duniya a 2030.
Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025 na tattare da ƙalubale, fiye da waɗanda aka yi daga shekara 10 zuwa 15 baya, inda tawaga 24 za ta kece raini a filayen wasa tara cikin biranen ƙasar shida.
A baya ana buga gasar tsakanin Yuni zuwa Yuli, amma a gasar bana za a yi ne cikin watan Disamba, saboda wasannin gasar kofin duniya da za a yi a 2026 daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Amma dai gasa biyu an yi tsakanin Janairu zuwa Fabrairu, amma wadda za a gudanar a 2025, an tsara yi daga Disamba zuwa Janairun 2026.
Kuma wannan shi ne a karon farko da za a yi gasar cin kofin Afirka a lokacin da ake bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Asalin hoton, Getty Images
Matakan da za a bi don gudanar da gasar
Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a kara tsakanin tawaga 24 da aka raba rukuni shida ɗauke da hurhuɗu kowanne.
Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta ɗaya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ƴan 16 da kuma huɗun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa.
Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri ɗaya ƙwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida.
Gabaki ɗayan gasar wasa 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da huɗu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman mataki na uku da kuma wasan karshe.
Su waye a cikin kowanne rukunni?
An raba tawaga 24 da za ta buga gasar kofin Afirka zuwa rukuni shida ɗauke da hurhuɗu kowanne.
Rukunin A : Morocco, Mali, Zambia, Comoros
Rukunin B : Masar, Afirka ta Kudu, Angola, Zimbabwe
Rukunin C : Najeriya, Tunisia, Uganda, Tanzania
Rukunin D : Senegal, Jamhuriyar Congo, Benin, Botswana
Rukunin E : Algeria, Burkina Faso, Equatorial Guinea, Sudan
Rukunin F : Ivory Coast, Kamaru, Gabon, Mozambique
Wa ake hasashen za ta lashe kofin?

Asalin hoton, FMFR Morocco
Morocco
Ita ce ta farko daga Afirka da ta kai zagayen daf da ƙarshe a tarihi a Gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Saboda haka tana sahun gaba da ake gannin za ta iya lashe kofin Afirka da take karɓar baƙunci.
Rabon da ƙasar ta lashe kofin tun 1976, saboda za ta yi fatan ɗaukar karo na biyu.
A gasar da aka yi a 2024, an yi waje da Morocco a zagaye na biyu wato ƴan 16
Senegal
Mai riƙe da kofin 2022 za ta buga wasannin da ƙwarin gwiwa mai tarin fitattun ƴan wasa da ke taka leda a faɗin duniya ƙarƙashin Pape Thiaw, wanda ya maye gurbin Aliou Cissé.
Senegal tana tare da tsoffin ƴan wasanta da kuma matasan da suka haɗa da Sadio Mané da Kalidou Koulibaly da Edouard Mendy da Gana Gueye da Nicolas Jackson da Pape Matar Sarr da Habib Diarra da kuma Iliman Ndiaye.
Kawo yanzu Senegal ce kan gaba a yawan wasa ba tare da rahin nasara ba a duniya guda 25 sai Afirka ta Kudu da 23 da kuma Sifaniya mai wasa 22,

Asalin hoton, Getty Images
Masar
Masar mai kofin Afirka bakwai tana cikin waɗanda za su iya lashe kofin, wadda take ƙarƙashin Hossam Hassan ta yi wasa 12 a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba.
Mohamed Salah yana daga fitattun ƴan wasan tawagar da ake sa ran za su nuna kansa a wasannin.
Algeria
Kociya, Vladimir Petkovic yana ta ƙoƙarin ganin ya mayar da kasar kan ganiya, mai fitattun ƴan wasa Mahrez da Slimani da kuma matasa Mohamed Amoura da Anis Hadj Moussa.
Bayan da aka yi waje da Algeria karo biyu a jere bayan wasannin cikin rukuni, kasar na fatan yin abin kirki a Morooco, kuma rabonta da kofin Afirka tun 2019.

Asalin hoton, Getty Images
Ivory Coast
Mai riƙe da kofin za ta yi ƙoƙarin ƙara lashe shi ƙarƙashin Emerse Faé.
Duk da cewar ta yi rashin nasara a hannun Saliyo da Zambia, tawagar za ta Morocco da fitattun ƴan wasa, illa dai akwai kalubale a matakin mai rike da kofin Afirka.
Ivory Coast ce ta ɗauki kofin karo biyu daga gasar takwas a gasar cin kofin duniya daga cikin tawagogin da za su kece raini a Morocco.
Nigeria
Najeriya wadda ta yi ta biyu a gasar da aka buga a Ivory Coast, za ta shiga wasannin da ƙwarin gwiwa.
Super Eagles na da fitattun ƴanwasa da suka haɗa da Osimhen da Lookman da Chukwueze da sauransu.
Yanzu dai hankali zai koma kan koci, Eric Chelle ko zai iya lashe kofin.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Waɗanda ba a sasu a lissafi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamaru
Kodayaushe ba tabbas a Kamaru, bayan rashin jituwa tsakanin shugaban hukumar ƙwallon kafar ƙasar, Samuel Eto da Marc Brys.
Sai dai Indomitable Lions ta yi wasa 12 ba tare da rashin nasara ba, kodayake ta yi tuntuɓe a hannun tsibirin Cape Verde.
Mai riƙe da kofin Afirka biyar tana da gogewa a wasannin.
Jamhuriyar Congo
Jamhuriyar Congo za ta yi fatan ɗaukar fansa a hannun Senegal, wadda ta doke ta 3-2 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a baɗi.
Tawagar da Yoane Wissa da Fiston Mayele ke jan ragama, za ta so ta nunawa duniya cewar ba kanwar lasa ba ce a fannin taka leda
Afirka ta Kudu
Bayan da Afirka ta Kudu ta taka rawar gani a wasannin da aka buga a 2023 da samun tikitin shiga gasar kofin duniya kai tsaye da za a yi a 2026.
Bafana Bafana na fatan nuna ƙwazo a wasannin da za ta fuskanta.
Kodayake yawancin ƴan wasanta na taka leda a gida daga Mamelodi Sundowns, duk da haka takan taka rawar gani da gagarar tawagogin da suke da fitattun ƴan ƙwallon.

Asalin hoton, Getty Images
Ina ne biranen da za a buga wasannin?
Za a buga gasar cin kofin Afirka a filaye tara cikin birane shida da suka haɗa da Rabat da Casablanca da Tangier da Agadir da Marrakech da kuma Fez.
Birnin Rabat yana da manyan filaye huɗu da suka haɗa da na Prince Moulay Abdellah Sports Complex, inda za a yi bikin buɗe gasar.
A Casablanca, filin Mohammed V da Wydad AC da Raja Casablanca ke wasanni, yana daga fitatcen filin da ake ji da shi a faɗin kasar.
Sauran biranen da za su karɓi baƙuncin wasannin sun haɗa da Tangier da Agadir da Marrakech da kuma Fez.

Asalin hoton, AFP
Filayen da za a buga gasar
- Prince Moulay Abdallah Sports Complex (Rabat)
- Crown Prince Moulay El Hassan Sports Complex (Rabat)
- El Barid Stadium (Rabat)
- Olympic Annex Stadium of the Moulay Abdellah Complex (Rabat)
- Mohammed V Stadium (Casablanca)
- Fez Sports Complex (Fez)
- Grand Stade de Tangier (Tangier)
- Grand Stade de Marrakech (Marrakech)
- Grand Stade d'Agadir (Agadir)
'Morocco ke ƙoƙarin mamaye ƙwallon kafar Afirka'

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Shekaru 20 da suka wuce, Maroko ta rungumi wasanni, musamman ƙwallon kafa, ginshiƙin da tasirinta a Afirka da fiye da hakan.
Ta hanyar karɓar baƙuncin gasar cin kofin Afirka, tana da niyyar ƙarfafa kimarta a matsayin ƙasa ta zamani mai kwanciyar hankali, kuma hangen nesa.
Nagartattun ababen more rayuwa na zamani ( filayen wasa da sufuri da otal-otal da dai sauransu) ba wai kawai alamar nasarar tattalin arziki ba da take da shi, tana kuma gudanar da mulki mai inganci da kishin nahiyar.
Maroko na son gabatar da kanta a matsayin cibiyar ƙwallon kafa ta Afirka, mai iya shirya wani babban wasanni na ƙasa da ƙasa mai inganci.
Batun karɓar baƙuncin gasar cin kofin Afrika ta 2025 a wuce wasanni.
Birnin Rabat, babban waje ne mai tasiri a harkokin diflomasiyya da ƙwallon ƙafa ya zama abin tasiri da alfahari a yankin.
Ƙasar ta riga ta zama hedkwatar ƙungiyoyin wasanni na Afirka da dama kuma ta ba da jari mai yawa a horo, ta hanyar Mohammed VI Academy ko kuma haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyin Afirka.
Haɗin gwiwar karɓar gasar cin kofin duniya da za a yi a 2030 tare da Spain da Portugal babu shakka ya nuna yadda ƙasar ke da tasiri a gudanar da manyan wasannin tamaula a duniya.











