Najeriya ta lashe kofin ƙwallon mata na Afirka karo na 10

Lokacin da ƴan wasa mata na Najeriya suka ɗaga kofin da suka lashe na gasar ƙallon ƙafa ta mata da aka yi a Morocco, ranar 26 ga watan Yulin 2025

Asalin hoton, X/CAFonline

Bayanan hoto, Lokacin da ƴan wasa mata na Najeriya suka ɗaga kofin da suka lashe na gasar ƙallon ƙafa ta mata da aka yi a Morocco, ranar 26 ga watan Yulin 2025
Lokacin karatu: Minti 3

Najeriya ta lashe kofin ƙwallon Afirka na mata karo na 10 bayan ta doke mai masaukin baƙi Morocco a wasan ƙarshe da aka buga na gasar ta shekara ta 2024, wadda aka jinkirta har ta shigo wannan shekara ta 2025.

Wasan ya tashi ne Najeriya tana da ci uku yayin da Morocco ke da biyu.

Morocco ce ta fara shiga gaba a wasan inda ta zura ƙwallo biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci ta ƙafar ƴan wasanta Ghizlane Chebbak da kuma Sanaa Mssoudy.

Sai dai bayan komawa daga hutun rabin lokaci Najeriya ta farke ƙwallon farko ta ƙafar ƴar wasa Esther Okoronkwo kafin daga bisani Folashade Ijamilusi ta zura ƙwallo ta biyu.

Jennifer Echegini ce ta ci wa Najeriya ƙwallonta ta ƙarshe wato ta uku a minti na 88, wadda ta sa ƙasara ta yi nasara.

Wannan ya nuna cewa Najeriya ta ci gaba da riƙe kambinta a matsayin wadda ta fi nuna bajinta a tarihin gasar.

Karawar ƙarshen ta wakana ne a filin wasa na Olympic Stadium mai cin ƴan kallo 21,000 da ke birnin Rabat.

A shekara ta 2022, Morocco ta zo ta biyu a gasar a wannan filin bayan ta sha kashi a hannun Afirka ta kudu.

Tawagar Morocco da ke ƙarkashin jagorancin mai horaswa Jorge Vilda, ta so ta ɗauki kofin a karon farko a tarihi, sai dai hakan bai yiwu ba.

Najeriya, wadda take ta ɗaya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe.

A yanzu za a iya cewa Najeriya ta cimma burinta na 'Mission X', wato lashe kofin a karo na 10.

....

Asalin hoton, Backpage Pix

Najeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya.

A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Najeriya ce ta lashe kyautar ƴar wasa mafi ƙwazo a gasar ta 2024.

Ƴar wasar Morocco Ghizlane Chebbak ce ta zama wadda ta fi kowa zura ƙwallo a gasar, inda ta zura ƙwallo biyar.

Mai tsaron raga ta Najeriya Chiamaka Nnadozie ce ta karɓi kyautar gola mafi ƙwazo, inda aka zura ƙwallo a ragarta sau uku kacal tun bayan fara gasar ta wannan shekara.

....

Asalin hoton, X/CAFonline

Ita kuwa Esther Okoronkwo ta zama gwarzuwar karawar, wannan ba abin mamaki ba ne ganin irin gudumawar da ta bayar wajen samun nasara Najeriya.

Ta zura ƙwallo ɗaya sannan ta taimaka aka ci sauran biyun.

Baya ga kofin, Najeriya za ta koma gida da ladan kuɗi dala miliyan ɗaya.