Ƴanwasan Najeriya mata biyar da tarihi ba zai manta da su ba

Perpetua Nkwocha, Asisat Oshoala da Francisca Ordega

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Abu na farko da mutum zai fara ji game da tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya shi ne ta lashe kofin ƙasashen Afirka sau 10, mafi yawa kenan a tarihin gasar.

Hakan ta sa dole ake cewa tawagar ta Super Falcons ce mafi hazaƙa a nahiyar Afirka saboda sauran nasarori da ta samu tun daga kafa ta a shekarun 1990.

Gabanin gasar kofin Afirka ta 2024 a Morocco, Super Falcons ta samu gurbi ne da gagarumar nasara gida da waje a kan Cape Verde da ci 5-0 da kuma 2-1.

'Yanmatan sun lashe kofin Afirka na Wafcon karon farko a 1998, kuma karo na ƙarshe da suka yi hakan shi ne a 2018 - kafin su lashe na ranar Asabar.

Hakan na nufin sun lashe gasar sau 10 cikin 13 da suka halarta.

Wannan maƙala ta yi duba kan zaƙaƙuran 'yanwasa biyar da suka taka muhimmiyar rawa a tawagar tun daga kafa ta zuwa yanzu.

Perpetua Nkwocha

Perpetua Nkwocha gab da za ta karbi takalmin zinare na wadda ta fi zura kwallo a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata, bayan karawar karshe tsakanin Ghana da Najeriya ranar 11 ga watan Nuwamban 2026

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Perpetua Nkwocha gab da za ta karbi takalmin zinare na wadda ta fi zura kwallo a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata, bayan karawar karshe tsakanin Ghana da Najeriya ranar 11 ga watan Nuwamban 2026

Perpetua Ijeoma Nkwocha 'yawasan tsakiya ce da ta yi ritaya daga tawagar ta Super Falcons a 2012.

Ita ce kan gaba a ci wa tawagar ƙwallaye da 80 da ta zira a raga cikin wasa 99 da ta buga.

An haife ta a shekarar 1976 kuma ta ci wa Najeriya ƙwallo huɗu a wasan ƙarshe na gasar kofin Afirka ta mata ta 2004, inda suka doke Kamaru.

Ta lashe kyautar gwarzuwar 'yarƙwallon Afirka har sau huɗu: a 2004, da 2005, da 2010, da kuma 2011.

Daga cikin kulob-kulob da ta taka wa leda akwai Sunnanå SK ta Sweden, da kuma Clemensnäs IF inda a yanzu take horar da 'yanwasan ƙungiyar bayan ta yi ritaya.

Asisat Oshoala

Asisat Oshoala na murnar cin kwallo a karawar Najeriya da Australia a birnin Brisbane a gasar kofin duniya ta mata wadda Australia da New Zealand suka karbi bakunci a 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Asisat Oshoala na murnar cin kwallo a karawar Najeriya da Australia a birnin Brisbane a gasar kofin duniya ta mata wadda Australia da New Zealand suka karbi bakunci a 2023

'Yarƙwallon da ake yi wa kallon ɗaya daga cikin mafiya hazaƙa a tarihin Afirka, Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar Afirka sau shida.

'Yarwasan gaban mai shekara 30 ta fara buga wa Najeriya wasa a watan Satumban 2013.

Ta ci kofin Afirka na mata a 2014, da 2016, da 2018. A 2014, ta zama gwarzuwar gasar kofin duniya ta 'yan ƙasa da shekara 20 kuma wadda ta fi zira ƙwallaye a gasar.

Ta taka leda a ƙungiyoyi da dama, waɗanda suka haɗa da Liverpool, Arsenal, Barcelona, da Dalian Quanjian. Yanzu tana buga wa kulob ɗin Bay FC na Amurka.

Daga cikin kyautukan da ta ci akwai gwarzuwar 'yarƙwallon Afirka a shekarun 2014, 2016, 2017, 2019, 2022, 2023.

Rasheedat Ajibade

Rasheedat Ajibade a lokacin karawar Najeriya da Ingila a gasar cin kofin duniya ta mata da aka yi a Australia da Switzerland, ranar 7 ga watan Agustan 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rasheedat Ajibade a lokacin karawar Najeriya da Ingila a gasar cin kofin duniya ta mata da aka yi a Australia da Switzerland, ranar 7 ga watan Agustan 2023

'Yar ƙwallon da ke taka wa ƙungiyar Atletico Madrid ta Sifaniya leda, Rasheedat Ajibade ce kyaftin ɗin tawagar Najeriya yanzu haka.

Mai shekara 25 ɗin tana da ƙwarewar buga lambobi da dama, ciki har da gefen hagu ko dama ko kuma tsakiya.

Ta wakilci Najeriya a tawagar matasa ta 'yan ƙasa da shekara 17, da 20, kuma ta ci kofin ƙasashen Afirka na mata a 2018.

An zaɓe ta matashiyar 'yarwasa mafi hazaƙa a Najeriya a 2018.

Mercy Akide

Ƴar wasan Najeriya Mercy Akide a gasar cin kofin duniya ta mata lokacin karawar da aka yi tsakanin Amurka da Najeriya a Philadelphia cikin watan Satumban 2003

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴar wasan Najeriya Mercy Akide a gasar cin kofin duniya ta mata lokacin karawar da aka yi tsakanin Amurka da Najeriya a Philadelphia cikin watan Satumban 2003

Mercy Joy Akide Udoh tsohuwar 'yarwasa ce da ta fara taka wa Najeriya leda a 1994.

Mai shekara 49 ɗin 'yarwasan tsakiya ce da ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen Afirka karo uku a 1998, da 2000, da kuma 2002.

Haka nan, ta lashe kyautar gwarzuwar 'yarƙwallon Afirka a 2004.

Francisca Ordega

Francisca Ordega a wata karawa da Najeriya ta yi da tawagar mata ta Amurka a ranar 16 ga watan Yuni, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Francisca Ordega a wata karawa da Najeriya ta yi da tawagar mata ta Amurka a ranar 16 ga watan Yuni, 2021

Francisca Ordega mai shekara 31 na taka leda a ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya a matsayin 'yarwasan gaba.

Ta taka wa Najeriya leda a dukkan tawagogi tun daga 'yan ƙasa da shekara 17, inda ta buga kofin duniya a tawagar manya a 2011, da 2015, da 2019.

Tana cikin tawagar Super Falcons da ta lashe kofin Afirka na 2010 da 2014.