Shin tawagar ƙwallon mata ta Najeriya ta fi ta maza ƙoƙari?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da aka fara Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata (Wafcon) a ƴan kwanakin nan, mutane da dama na ganin duk da cewa sauran ƙasashe sun ƙara ƙarfi, Najeriya na cikin waɗanda suka fi damar lashe gasar kasancewar ta lashe kofin sau tara a baya.
Bayan wasanni biyu a cikin rukunin B, Super Falcons ta samu gurbin zuwa matakin gaba na zagayen ƴan 16 bayan doke Tunisia da Botswana kuma zuwa yanzu ba a zura mata ƙwallo ko ɗaya a raga ba.
Kocin tawagar Justine Madugu ya ce tawagar na cikin waɗanda suka fi ƙarfi a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya.
Justine ya ce "Muna ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi ƙarfi a Afirka da ma duniya gaba ɗaya idan aka duba rawar da muka taka tsawon shekaru, kuma muna ƙoƙarin ɗorawa a kai".
Rawar da tawagar ke takawa a gasar zuwa yanzu na bai wa ƴan Najeriya farin ciki yayin da ƴan wasa kamar Chinweze Ihezuwo da Rinsola Babajide ke haskawa.
Mun kwatanta rawar da tawagar Super Falcons ke takawa da ta tawagar maza Super Eagles a halin yanzu da ma tarihi?
Nasarorin Super Falcons

Asalin hoton, Getty Images
Super Falcons ta fara fice ne a shekarar 1991 a lokacin da aka ƙaddamar da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata wadda Najeriya ta fara lashewa a tarihi.
Bayan lashe kofin a 1991, tawagar ta ci gaba da lashe shi har karo bakwai cikin takwas da aka gudanar daga farko.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Super Falcons ta lashe kofin karo na tara a shekarar 2018 lokacin da ta doke Afirka ta Kudu da ci 4-3 a bugun fanariti a wasan ƙarshe na gasar.
A shekarar 2025 tawagar na neman lashe kofin karo na goma a gasar da ake gudanarwa a Morocco.
Lashe kofin duniya ya kasance abu mai wuya ga ƙasashen Afirka amma dai Super Falcons ba ta taɓa gaza samun gurbin zuwa gasar ba – ta je gasar karo tara da aka gudanar a tarihi. Ita ce ƙasar Afirka da ta fi zuwa gasar kofin duniya ta mata.
Baya ga samun gurbin gasar, Super Falcons ce kaɗai daga Afirka da ta taɓa zuwa matakin kwata fainal, a shekarar 1999.
A gasar Olympics, nisan da Super Falcons ta fi yi a tarihi shi ne zuwa matakin kwata fainal a 2004 a ƙasar Girka.
Sai dai, a karo takwas da aka gudanar da gasar, sau huɗu kawai tawagar ta samu damar zuwa.
Ƴan wasan Super Falcons ne suka mamaye kyautar ƴan wasan Afirka mafi hazaƙa a bangaren mata da ake bayarwa duk shekara yayin da Asisat Oshoala kaɗai ta lashe sau shida.
Sauran da suka lashe sun haɗa da Perpetua Nkwocha da ta lashe sau huɗu, da Cynthia Uwak da ta lashe sau biyu, sannan Mercy Akide da ta lashe sau ɗaya.
Hakan na nufin ƴar Najeriya ta lashe kyautar sau 13 a tarihi.
Nasarorin Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar ƙwallon ƙafar mazan Najeriya, Super Eagles ta lashe kofin gasar nahiyar Afirka ta maza ne sau huɗu a tarihi, wanda na baya-bayan nan shi ne 2013 a Afirka ta Kudu. Ta lashe sauran biyun ne a 1980 da 1994.
Ita ce ta uku a jerin ƙasashen da suka fi lashe kofin Afcon a tarihi kuma tana yawan yin nisa a gasar yayin da ta gama ta biyu a gasar sau biyar a tarihi, ta kuma zama ta uku sau takwas. Ana iya cewa tana taka rawa a gasar.
Super Eagles ta samu gurbin zuwa gasar Kofin Duniya sau shida a tarihi, yayin da ba ta buga gasar ba a 1966 saboda ƙasashen Afirka sun ƙi buga gasar domin nuna ɓacin ransu game da wariya da take zargin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya na nuna mata.
A gasanni biyar da ta buga, Super Eagles ta kai zagayen ƴan 16 sau biyu yayin da aka fitar da ita tun daga matakin rukunni sau uku a gasar.
Super Eagles ce kaɗai daga nahiyar Afirka da ta taɓa lashe gasar ƙwallon ƙafa ta Olympics a tarihi bayan doke Argentina a wasan ƙarshe a 1996.
Haka zalika ta zo ta biyu a 2008 - babu wata ƙasa a Afirka da ta taɓa zama ta biyu - inda Argetina ta doke ta a wasan ƙarshe a shekarar.
Sannan a 2016 kuma ita ta kasance ta uku a gasar da aka gudanar a Brazil.
Ƴan wasan Najeriya shida ne suka taɓa lashe kyautar ɗan wasa mafi hazaƙa a nahiyar Afirka: Ademola Lookman da Victor Osimhen da Nwankwo Kanu (sau biyu) da Emmanuel Amunike da Victor Ikpeba da kuma Rashidi Yekini.
Hakan na nufin ɗan Najeriya ya lashe kyautar sau bakwai a tarihi.
Kwatanta nasarorin tawagogin biyu
Tawagar mata ta Najeriya Super Falcons ta fi Super Eagles yawan cin kofin nahiyar Afirka yayin da matan suka lashe sau tara mazan kuma sau uku. Matan ne suka fi yawan kofin a Afirka yayin da mazan ne na huɗu a jerin waɗanda suka fi yawan kofunan.
A gasar Kofin Duniya tawargar matan ba ta taɓa gaza samun gurbin zuwa gasar ba yayin da mazan suka gaza sau tara. Matan sun buga gasar sau tara a tarihi yayin da mazan sau biyar kaɗai.
Mataki mafi nisa da matan suka taɓa kai wa a gasar Kofin Duniya shi ne kwata fainal yayin da mazan kuma zagayen ƴan 16.
A gasar Olympics dai mazan sun taɓa lashe gasar tare da zuwa na biyu sau ɗaya da na uku sau ɗaya, ita kuwa Super Falcons ba ta taɓa lashe gasar ba kuma ba ta taɓa wuce kwata fainal ba.
Maza shida ne suka taɓa lashe kyautar ɗan wasa mafi hazaƙa a Afirka yayin da mata kuma uku ne, amma idan aka haɗa yawan kyautar tsakaninsu, maza sun lashe bakwai yayin da matan suka lashe 13.
Alƙaluman za su iya nuna cewa tawagar mata ta Najeriya Super Falcons ta fi ta mazan Super Eagles cimma nasarori, amma wasu na ganin cewa ba a yi adalci ba kasancewar ƙwallon ƙafar maza ta fi wahala a idon mutane.











