Waɗanne ƙasashen Afirka ne ke da damar zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 6
A yanzu da ake ƙoƙarin ƙarƙare wasannin neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026, har yanzu akwai sauran gurabu guda bakwai.
A yanzu da ya rage wasanni biyu da za a buga a ranar Laraba 8 da Talata 14 ga watan Oktoba, ƙasashe tara da suke saman teburin rukuninsu kaɗai suke da tabbacin shiga gasar.
Yanzu dai Moroco da Tunisia ne suka samu tikitin shiga gasar ta 2026 da za a yi a ƙasashen Amurka da Mexico da Canada.
Cape Verde na neman maki uku ne kacal domin shiga gasar a karon farko a tarihinta, sannan Masar da Algeria ma neman maki uku kawai suke nema a wasanni biyu da suka rage musu.
Ƙasashe huɗu da suka fi ƙoƙari a cikin waɗanda suka ƙare a mataki na huɗu za su fafata wasannin raba-garbada, sai waɗanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu ƙasashen waje.
A yanzu da manyan ƙasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Najeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, sashen wasanni na BBC ta rairayo wasu ƙasashe da take gani suna da sauran damar zuwa gasar.
Rukunin A - Masar na gab a samun gurbi
Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti a ranar Laraba, shikenan ta samu tikiti.
Ita kuma ƙasar Djibouti tana can ƙarshen teburi ne, domin maki ɗaya tak take da shi a wasa takwas da ta buga.
Idan ma Masar ta yi rashin nasara a wasan, za ta fatata da Guinea-Bissau a ranar Lahadi.
Burkina Faso kuma wadda take ƙoƙarin zuwa ta biyu za ta buga wasa ne da ƙasar Saliyo sai kuma ƙasar Habasha, amma tana buƙatar samun nasara a wasannin kafin samun gurbin buga wasannin raba-gardama.
Ƙasashen da za su iya samun nasara a rukunin: Masar da Burkina Faso
Rukinin B – Senegal ce jagora
Nasarar da Senegal ta samu a kan DR Congo ce ta ba ta damar ɗarewa teburin rukunin, inda yanzu ta ba da tazarar maki ɗaya.
Tawagar ta Teranga Lions za ta je wasa da Sudan ta Kudu wadda ke ƙarshen teburi, sai ta buga wasan ƙarshe da Mauritania, inda take buƙatar nasara biyu domin samun shiga gasar.
DR Congo dai na fatan Senegla ta yi rashin nasara, ita kuma ta samu nasara a wasannin biyu a gidan Togo da kuma Sudan a gida.
Sudan na buƙatar nasara a duka wasanninta, sannan Senegal ta yi rashin nasara wasanninta biyu domin samun gurbin zama ta ɗaya a teburi, amma tana da damar zuwa ta biyu idan ta doke Congo.
Ƙasahen da za su samu nasara: Senegal da DR Congo da Sudan
Rukunin C – Benin ta samu dama bayan hukuncin FIFA kan Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
A wannan rukunin kuma bayan hukuncin da FIFA ta ɗauka a kan ƙasar Afirka ta Kudu na cire mata maki uku saboda sanya ɗanwasan da bai cancanta ba a wasanta da ƙasar Lesotho.
Yanzu Benin ce kan gaba a rukunin, inda take saman Afirka ta Kudu da bambancin ƙwallaye, sai Najeriya da Rwanda suke da maki da na huɗu, amma duk suna da damar samun gurbi.
Benin na da wasa a gidan Rwanda da Najeriya, sai tawagar Bafana za ta buga da Zimbabwe sai Rwanda a gidanta.
Najeriya tana da wasa a gidan Lesotho sai Benin, kuma dole ne ta ci wasanninta guda biyu, amma ko da ta lashe wasannin, sai yadda ta wakana a sauran wasannin kafin sanin matsayarsa.
Dukkan ƙasashen rukunin na da damar samun gurbi
Rukunin D - Cape Verde na yunƙurin kafa tarihi

Asalin hoton, Getty Images
Nasarar da Cape Verde ta samu a kan Kamaru da ci ɗaya mai ban haushi a watan jiya ta sa ƙasar ta kama hanyar kafa tarihin zuwa gasar cin Kofin Duniya na farko a tarihinta.
Yanzu ƙasar na buƙatar nasara ɗaya kacal a wasanta da Libya a ranar Laraba ko kuma a wasanta a gida da ƙasar da ke ƙarshen teburi Eswatini.
Kamaru za ta iya samun nasara da bambancin zura ƙwallaye idan ta doke Mauritus da Angola, ita kuma Cape Verde ta yi canjara a wasannin biyu, ko kuma idan Kamaru ta samu maki huɗu a wasannin biyu, ita kuma Cape Verde ta yi rashin nasara.
Sai kuma Libya ce ta uku, kuma maki uku ne tsakaninta da Kamaru, kuma za ta iya bayar da mamaki.
Ƙasashen da za su iya samun gurbi: Cape Verde da Kamaru da Libya
Rukunin E – Fafutikar zama ta biyu
Ƙasar Morocco ta riga ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniyar.
Tanzania da Nijar da Zambia ne sauran ƙasashen da ke rukunin, kuma yanzu suna ta fafatawa ne domin samun gurbi na biyu.
Ta gaba a rukunin ita ce Morocco wadda ta riga ta samu gurbi
Rukunin F – Tawagar Elephants na gaba

Asalin hoton, Getty Images
Ivory Coast na gaba da Gabon da maki ɗaya bayan canjaras da ta yi da ƙasar Gabon a Franceville a watan Satumba.
Ƙasar za ta je gidan Seychelles a ranar Juma'a, sai kuma ta fafata da Kenya a ranar Talata.
Gabon za ta je gidan Gambia, sai kuma Burundi ta baƙunce ta.
Ƙasashen da za su iya samun gurbi: Ivory Coast da Gabon
Rukunin G – Algeria na gab da samun tikiti
Algeria ita ma ta ba da tazarar maki huɗu a saman teburi, kuma tana buƙatar maki uku ne a wasanta da ƙasar Somalia wadda ta riga ta fita ko kuma ta biyu Uganda zai ta ba gurbi.
Uganda ta zarce Mozambique ne kawai da bambancin zura ƙwallo a matakin na biyu.
Ƙasashen da za su iya samun gurbi: Algeria da Uganda da Mozambique
Rukunin H – Namibia na neman zama ta biyu
Tunisia ta riga ta tsallake bayan samun gurbi duk da cewa akwai sauran wasa biyu da za ta buga, inda ita kuma Namibia ta dage wajen neman zama ta biyu a rukunin.
Namibia za ta je gidan Liberia a ranar Alhamis kafin ta ƙarƙare a birnin Tunis.
Tunisia ta riga ta samu gurbi
Rukunin I – Ghana ta yi kaka-gida a sama

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashe uku ne ke fafutikar samun gurbin na kai-tsaye, amma Ghana ce a sama da tazarar maki uku a saman Madagascar da Comoros.
Ghana za ta samu gurbi idan ta yi nasara sannan Madagascar ta gaza samun maki uku.
Wasan ƙarshe na Ghana shi ne a gida da Comoros, ita kuma Madagacar za ta je gidan Mali a wasan na ƙarshe.
Ƙasashen da za su iya samun gurbi: Ghana da Madagascar da Comoros
Wasannin raba-garama
Ƙasashe huɗu da suka fi maki a cikin ƙasashen da suka ƙare a na biyu daga rukunoni tara ɗin ne za su fafata wasannin raba-gardama a watan Nuwamba.
Zuwa yanzu dai Gabon da Madagascar da DR Congo da Burkina Faso ne a gaba a cikin tawagogi na biyu.
Sakamakon za su iya canjawa bayan wasanni biyu na ƙarshe, sannan kuma ba a riga an sanar da tsarin wasannin na raba-gardama ba.
Amma ƙasashen da suka samu nasara a wasannin na raba-gardama ne za su sake fafatawa a wasanin na raba-gardama da wasu ƙasashen na duniya kafin samun gurbi a gasar ta duniya.











