'Yanƙwallon Afirka da za su ɗauki hankali a Premier League ta 2025-26

Mohammed Kudus da Bryan Mbeumo sun tsinci kan su a wasu ƙungiyoyin daban na gasar Premier League ta bana, yayin da Habib Diarra zai fara buga gasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohammed Kudus da Bryan Mbeumo sun tsinci kan su a wasu ƙungiyoyin daban na gasar Premier League ta bana, yayin da Habib Diarra zai fara buga gasar
    • Marubuci, Rob Stevens
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kakar 2025-26 ta gasar Premier League ta Ingila za ta ci gaba a ranar Juma'a, inda Liverpool za ta fara kare kambinta a gida a wasa da Bournemouth.

Tauraron ɗanwasan Masar Mohamed Salah, shi ne gwarzon ɗanwasan gasar kuma zai yi yunƙurin lashe takalmin zinare na biyar a sana'arsa yayin da zai fara taka leda da sababbin 'yanwasa Hugo Ekitike da Florian Wirtz.

Wasu 'yanwasan Afirka da dama sun samu komawa manyan ƙungiyoyi, akwai kuma wasu sababbi a gasar daga ƙasashen Kongo, da Morocco, da Mozambique, da Senegal.

A gefe guda kuma, 'yanwasan nahiyar kusan 50 ne za su bar wasannin gasar zuwa gida domin karawa a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025 (Afcon 2025) da za a yi daga 21 ga watan Disamba zuwa 18 ga Janairu.

Mun yi duba kan wasu 'yanwasa da suka koma sabbin ƙungiyoyi da ke neman nuna kan su a sabuwar kakar Premier League ta 2025-26.

Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta?

Ɗan ƙasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a 'yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga Brentford.

Ɗanƙwallon mai shekara 25 ya ci ƙwallo 20 a gasar da aka kammala da kuma bayarwa a ci bakwai.

United na tsaka da sake gina ƙungiyar ƙarƙashin mai horarwa Ruben Amorim bayan gama gasar a mataki na 15, wanda shi ne mafi muni a tarihin ƙungiyar na Premier League.

Mbeumo zai fuskanci matsi nan take domin ya nuna ƙwarewarsa tare da Matheus Cunha da Benjamin Sesko.

Ko Kudus zai zama cikakken makwafin Son?

Kudus ne ɗanwasa na farko da ya bar Wst Ham zuwa Tottenham kai-tsaye tun daga 2011

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kudus ne ɗanwasa na farko da ya bar Wst Ham zuwa Tottenham kai-tsaye tun daga 2011

Wani babban cinikin da aka yi shi ne wanda Mohammed Kudus ya kawo karshen zaman shekara biyu da ya yi a West Ham kuma ya koma Tottenham kan fan miliyan 55.

Ɗanwasan na Ghana ya taka rawa sosai a West Ham a kakar farko, amma bai yi kokari ba a kaka ta biyu saboda yadda ya yi fama da salon wasa na mai horarwa Graham Potter.

Irin ƙoƙarin da mai shekara 24 ɗin ya yi a Jax ne ya sa ƙungiyoyi suka dinga nemansa, kuma yanzu Spurs za ta so ya nemo wannan bajintar tasa domin taimaka mata a sabuwar kaka.

Saboda samun damar buga gasar zakarun Turai ta Champions League na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ya koma Tottenham.

Yayin da tauraron ɗanwasa Son Heung-Min ya bar ƙungiyar, da kuma James Maddison da ya ji rauni, Kudus zai iya zama mai muhimmancin gaske tun daga farkon kaka.

Ko Ait-Nouri zai taimaki Man City dawo da martabarta?

Rayan Ait-Nouri na cikin 'yanwasan Man City da suka yi rashin nasara a gasar Club World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rayan Ait-Nouri na cikin 'yanwasan Man City da suka yi rashin nasara a gasar Club World Cup

Bayan komawa mataki na uku da kuma kammala kakar 2024-25 ba tare da wani kofin kirki ba, Manchester City za ta danno da ƙarfinta domin ɗaukar kofi.

City ta shiga kasuwa da wurwuri domin ɗaukar ɗanwasan baya daga ɓangaren hagu Rayan Ait-Nouri, kuma ɗanwasan mai shekara 24 ya fara taka mata leda a gasar Club World Cup da ba ta je ko'ina ba.

Ɗan ƙasar Aljeriyan ya koma City ne daga Wolves kan fan miliyan 31.

Ait-Nouri ya nuna barazanar kai hari sosai daga gefensa duk da yadda Wolves ta sha fama a kakar bara, inda ya ci ƙwallo huɗu da kuma bayar da bakwai a zira a raga.

Bayan ya samu wuri a City, tabbas mai horarwa Pep Guardiola zai so sabon mutumin nasa ya ƙara wuta wajen jawo ƙwallo daga baya zuwa gaba.

Adingra a Sunderland

Simon Adingra ne ya shirya ƙwallo biyu da ƙasarsa Ivory Coast ta ci a wasan ƙarshe na Afcon 2023 da ta karɓi baƙunci amma kuma bai samu buga wasanni ba a ƙungiyarsa ta Brighton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Simon Adingra ne ya shirya ƙwallo biyu da ƙasarsa Ivory Coast ta ci a wasan ƙarshe na Afcon 2023 da ta karɓi baƙunci amma kuma bai samu buga wasanni ba a ƙungiyarsa ta Brighton

Ƙungiyar Sunderland ta dawo buga gasar Premier League a karon farko tun 2017, kuma tuni ta karaɗe kasuwar sayen 'yanwasa, har ma ta sayi 11.

Shida daga cikinsu 'yan Afirka ne. Ta kashe kuɗi mafi yawa a tarihinta fan miliyan 30 kan ɗan ƙasar Senegal Habib Diarra, da ɗaukar Arthur Masuaku da Noah Sadiki 'yan ƙasar Kongo, da ɗan Mozambique mai suna Reinildo, da Chemsdine Talbi na Morocco.

Simon Adingra da ya ci kofin Afcon 2023 da ƙasarsa Ivory Coast na cikin mutanen da ya sauya sheƙa daga kudu zuwa arewaci bayan fara wasa 12 kacal a kakar bara.

Yayin da yake cikin 'yanwsan da suka san Premier League, ɗanƙwallon mai shekara 23 zai so ya taimaka wa Sunderland cigaba da zama a gasar.

'Yanwasan da ka iya motsawa...

Duk da cewa Nicolas Jackson ya ci kofin Club World Cup tare da Chelsea, akwai yiwuwar zai bar filin wasa na Stamford Bridge

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duk da cewa Nicolas Jackson ya ci kofin Club World Cup tare da Chelsea, akwai yiwuwar zai bar filin wasa na Stamford Bridge

Har yanzu West Ham za ta ci gaba da aiki da ɗan Afirka bayan ta biya fan miliyan 19 wajen ɗaukar El Hadji Malick Diouf daga Slavia Prague.

Kociya Potter ya ce ɗanwasan Senegal ɗin mai shekara 20 "na da yunwar tamaula da kuma buri mai yawa".

Ɗanwasan Kongo Aexel Tuanzebe zai so ya sake guje wa barin gasar ta Premier a karo na biyu bayan ya koma Burnley daga Ipswich Town.

Ganin cewa sai a ranar 1 ga watan Satumba za a rufe kasuwar saye da musayar 'yanƙwallon, akwai 'yanwasan Afirka da za su motsa a bana zuwa Premier.

Ɗanwasan Senegal da Nicolas Jackson ya samu izinin barin Chelsea a kasuwar nan, yayin da shi ma na Kongo Yoane Wissa ke shirin barin Brentford.