Ƴanƙwallon Najeriya da suka kusa lashe Ballon d'Or

Wasu ƴanwasan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

A jiya Litinin ne aka yi bikin karrama gwarzan ƴanƙwallon ƙafa na duniya na shekarar 2025, inda aka karrama fitattun ƴanwasa da suka nuna bajinta da ƙwarewa a ƙungiyoyi da ƙasashensu a kakar da ta wuce.

Kyautar Ballon d'Or, karramawa ce da take da matuƙar tasiri a ƙwallon ƙafa, inda duk da cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA tana karrama gwarazan da take gani su ne kan gaba a duniya, an fi kallo tare da amfani da karramawar ta Ballon d'Or a matsayin wadda ta fi daraja.

A taron na, fitaccen ɗanwasan ƙasar Faransa da ƙungiyar PSG, Ousmane Dembele ya lashe kyautar ta bana a bikin wanda aka yi a ɗakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a ƙasar Faransa.

Aitana Bonmati ce ta lashe Ballon d'Or ta ɓangaren mata, wanda shi ne karo na uku da ta lashe kyautar a jere.

Wani abu da ya ja hankalin masu bibiyar karramawar daga Najeriya shi ne yadda mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata wato Super Falcons, Chiamaka Ndanozie ta zo ta huɗu a cikin tsaro raga mata a duniya.

Wannan ya sa BBC ta kalato wasu fitattun ƴanwasan ƙwallon ƙafa ƴan Najeriya da suka kusa lashe kambun a tarihin karramawar.

Finidi George - 1995

Finidi

Asalin hoton, Getty Images

Finidi George ɗanwasan Najeriya ne da ya yi tashi sosai a shekarun baya a Najeriya da ƙungiyoyin turai.

Finidi ya samu shiga cikin zaratan ƴanƙwallon na duniya ne a shekarar 1995 bayan nasarar da ya samu a ƙungiyar Ajax ta Holland, inda ya samu shiga cikin jerin bayan an faɗaɗa karramawar zuwa ƙasahen da ba na turai ba.

A gasar Champions League ta shekarar, Finidi ya zura ƙwallo tara, sannan ya bayar aka zura ƙwallo 11.

A shekarar ne Ajax ta lashe gasar Champions League da gasar Eredivisie ta ƙasar Holland da wasu kofuna uku.

Finidi ya ƙare ne a na 21 a karramar ta shekarar 1995.

Nwankwo Kanu – 1996 da 1999

Kanu

Asalin hoton, Getty Images

Nwankwo Kanu na cikin zaratan ƴanƙwallo ƙafa ƴan Najeriya suka daɗe suna jan zarensu a harkar tamaula.

A shekarar 1996, Kanu ya samu ƙuri'a 14, inda ya zo na 11 bayan ya lashe kofin Olympic da aka buga a Atlanta, da kuma rawar da ya taka a ƙungiyar Inter Milan ta Italiya.

Haka kuma a lokacin da ya koma Arsenal, tsohon kyaftin ɗin na Najeriya ya sake samun shiga, inda a shekarar 1999 ya zo na 23 a duniya.

Sanan tsohon ɗanwasan ya lashe karramawar gwarzon ɗanƙwallon Afirka sau biyu a 1996 da 1999.

Victor Ikpeba – 1997

Victor

Asalin hoton, Getty Images

Victor Ikpeba, ɗan wasan Najeriya ne da ake yi wa laƙabi da suna "Prince of Monaco,"

Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimakawa ƙungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa.

Ɗanwasan ya samu ƙuri'a 2, inda ya ƙare a 32 a cikin jerin waɗanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997.

Asisat Oshoala – 2022 da 2023

Oshaola

Asalin hoton, Getty Images

Asisat ita ce ƴarƙwallon Najeriya mace da ta fi lashe kambun gwarzuwar ƙwallon ƙafa ta Afirka a nahiyar.

Ita ce mace ta farko daga Najeriya da ta fara shiga jerin waɗanda aka karrama a Ballon d'Or ta mata.

Bayan lashe gasar Champions League ne ta zama gwarzuwa ta 16 a duniya a shekarar 2022, sannan ta sake zuwa ta 20 a shekarar 2023.

Victor Osimhen – 2023

Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Ɗanwasan ƙwallon gaba na Najeriya wanda a yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Galatassary ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa ƙungiyar Napoli wajen lashe gasar Serie A karon farko a shekara 33, sannan ya lashe wanda ya fi zura ƙwallo a shekarar ta 2023.

A shekarar ce Osimhen ya zo na takwas a duniya.

Victor Osimhen ne ya lashe gwarzon ɗanƙwallon Afirka a shekarar 2023.

Ademola Lookman – 2024

Ademola

Asalin hoton, Getty Images

A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake taka leda a ƙungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar.

Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, ina ya zura ƙwallo uku rigis a raga, sanna ya taka rawar gani sosai a gasar cin kofin Afirka.

Chiamaka Nnadozie - 2025

Chiamaka

Asalin hoton, Getty Images

A bikin karramawar ta bana kuma, mai tsaron ragar ƙungiyar Brighton & Hove Albion ta Ingila, Chiamaka Nnadozie ce ta samu tagomahi, inda ta zo ta huɗu a cikin masu matsaron raga mata a duniya, wanda shi ne matsayi mafi girma da Najeriya ta taɓa samu a karramawar.

Chiamaka Nnadozie ta lashe kofin gasar cin kofin Afirka na mata sau biyu a 2018 da 2024.