Wa zai lashe kofin duniya na 2026?

Asalin hoton, Getty Images
An fitar da jaddawalin yadda ƙasashe za su kara a gasar cin kofin duniya ta 2026, wani abu da ke nuni da kusantowar gasar da za a yi Amurka da Canada da kuma Mexico.
Babu shakka jaddawalin ya ɗauki hankali kuma ya bayar da mamaki ga wasu masu nazarin wasanni.
Amma waɗanne ƙasashe ne masana da masu sharhi ke hasashen za su iya lashe gasar?
Akwai sauran gurabe shida da ake jira kafin a kammala jaddawalin matakin rukuni na gasar, kuma za su samu ne bayan an gama wasannin cike gurbi da za a yi a cikin watan Maris.
Amma mun yi nazari kan ƙasar da za ta iya ɗaukar kofin na 2026 a birnin New York.
Jamus da Sifaniya da kuma Belgium ne suka faɗa a rukuni mafi sauƙi a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya ta 2026, ta la'akari da matsayin ƙasashen a jerin waɗanda suka fi iya taka leda na duniya da Fifa ta wallafa.
Netherlands da Faransa ne suka faɗa a rukuni mafi wahala a gasar idan aka yi amfani da wancan ma'auni na jerin ƙasashen Fifa.
Waɗanne ƙasashe ke tashe a yanzu?
Ingila ta lashe dukkan wasanninta na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 ba tare da an zura mata ƙwallo ko ɗaya ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta zo ta biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai biyu da suka gabata, kuma ta kai matakin quarter finals a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar shekaru uku baya, wani abu da ya sa ake ganin tawagar 'Three Lions' ƙarƙashin sabon koci Thomas Tuchel na cikin masu iya lashe gasar.
Masu sharhi da dama na sa ran Ingila ta yi abin gani a gasar ta bana, inda mafi yawansu ke sanya ta a mataki na biyu bayan Sifaniya a jerin ƙasashen da za su iya lashe gasar.
Zakarun Turai, Sifaniya sun kusa bin sahun Ingila wajen lashe dukkan wasanninta na sharar fage amma sai ta buga canjaras 2-2 da Turkiyya a wasan ƙarshe da suka buga.
Sifaniya ta lashe Euro 2024 cikin ruwan sanyi bayan doke Ingila a wasan ƙarshe, inda matashin ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin gwarzayen gasar.
Bayan doke su da Portugal ta yi a bugun penalty a gasar Nations League a watan Yuni, Sifaniya ba ta yi rashin nasara ba yi rashin nasara ba tun wasan da ta yi da Scotland a watan Maris ɗin 2023.
Faransa wadda ta zo ta biyu a Qatar 2022, tana cikin ƙasashen da ake ganin za su shana a gasar mai zuwa, bayan ta kammala wasannin neman gurbi ba tare da an doke ta ba a ƙarƙashin kocinta, Didier Deschamps.
Opta supercomputer ya ce ƙasashen Turan uku kan gaba cikin waɗanda ake sa ran za su iya lashe gasar, inda Sifaniya ke da maki 17%, Ingila ke da 11% ita kuma Faransa ke da 14.1% na hasashen iya lashe gasar.
Jamus wadda aka doke a wasan farko na neman gurbin shiga gasar, amma ta lashe sauran wasanninta biyar tana cikin waɗanda masana ke ganin za ta iya lashe gasar, yayin da su ma Switzerland da Netherlands da Belgium da Croatia da kuma Norway duk suka kammala wasannin neman gurbi ba tare da an doke su ba.
Brazil ba ta tashe sosai, inda ta ƙare a mataki na biyar a jerin ƙasashen kudancin Amurka, kuma ta sha kayi a wasanni shida daga cikin 18 da ta buga. Sai dai duk da haka masu nazari na sanya ta a jerin ƙasashen da za su taka rawar gani a gasar cin kofin duniya, inda ake ganin tana a matsayi na huɗu a cikin ƙasashen da za su yi nasara a gasar. Amma Opta ya sanya ta a matsayi na bakwai ne.
Argentina wadda ke kare kambunta a gasar ta zamo zakara a jerin ƙasashen da suka buga wasannin neman gurbi daga kudancin Amurka, inda ta bai wa Equador da ta zo ta biyu, tazarar maki tara.
Brazil ce kaɗai ƙasar da ta taɓa lashe gasar sau biyu a jere, a 1958 da kuma 1962, amma tunda ana sa ran Lionel Messi zai buga, Argentina za ta shiga jerin waɗanda ake ganin suna iya lashe gasar.
Japan ce ta yi zarra a wasannin neman gurbi daga Asia, kuma sau ɗaya kacal aka doke ta a wasannin.
Wadda ta yi ba-zata wajen kaiwa wasan dab da na ƙarshe a gasar da aka yi a Qatar, Morocco ta lashe dukkan wasannin ta na neman gurbi daga nahiyar Afirika kuma ana hasashen za ta iya zama barazana ga manyan ƙasashen Turai, yayin da su ma Masar da Senegal da Ivory Coast da kuma Tunisia duk suka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniyan ba tare da an doke su ko sau ɗaya ba. were also unbeaten.
Sai dai za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirika a watan nan, kuma ana hasashen cewa buga gasa biyu a cikin watanni shida zai gajiyar da ƴan wasan Afirika.
Cristiano Ronaldo ya ce wannan ce gasar cin kofin duniya ta ƙarshe da zai halarta, kuma ana ganin tawagarsa ta Portugal a cikin waɗanda za su iya bayar da mamaki, yayin da Italiya da ta lashe gasar Euro 2020 ke jiran amfana da tanadin sharar fage domin shiga gasar, amma duk da haka ana ganin za ta iya nuna bajinta.
Ya tasirin yanayin da za a yi gasar?
Ana ƙorafi a kan yadda za a gudanar da gasar cin kofin duniya ta 2026 a cikin yanayi na tsananin zafi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Daga cikin masu ƙorafi game da buga gasar a cikin wannan yanayi akwai ɗan wasan tsakiyar Chlesea, Enzo Fernandez, wanda ya ce yana jin jiri ida ya shiga ''zafi mai hatsari sosai.''
Wani bincike da jami'ar Queen ta Belfast ta jagoranta ya gano cewa ma'aunin zafi da aka yi hasashen zai riƙa kai maki 14 da 16 a filayen wasan gasar cin kofin duniya ta 2026 yana da haɗari sosai.
Akwai ƙasashen da za su iya taka leda a cikin wannan yanayi, amma wasu ƙasashen Turai za su wahala sosai, inda tuni Ingila ta nemi a riƙa buga wasanni da dare domin gudun tsananin zafi.
Yanayin zai iya yi wa ƙasashen Kudancin Amurka da kuma na Afirka daidai, amma babu ƙasar da ta taɓa lashe gasar daga Afirika.
Mai masaukin baƙi na da dama kasancewa za ta buga wasanni a gida, amma yadda filayen wasan suke a wurare daban-daban zai iya zamo mata ba cikin daɗi ba.
Daga cikin gasar kofin duniya 11 da aka buga a Turai, ƙasashen Turai ne suka lashe 10, amma labarin na canzawa a duk lokacin da aka buga gasar a Amurka.
Daga cikin gasar bakwai da aka buga a can, ƙasashen kudancin Amurka ke lashewa, baya ga wanda Jamus ta lashe a 2014, kuma Argentina ta yi nasarar lashe gasar da aka yi a Qatar, inda ke da tsananin zafi.
Sifaniya ce ƙasar Turai da ta taɓa lashe gasar kocin duniya a wajen Turai, inda ta ɗaga kofin da aka buga a Afirika ta Kudu a 2010.
Me masu sharhi ke cewa?
Da yake sharhi kan rukunin da Ingila ke ciki a wata hira da BBC Radio 5, tsohon ɗan wasan gaban ƙasar Dion Dublin ya ce: "A kullum ina fargabar Croatia. Ina ganin suna da ƙwarewa sosai kuma za su iya taɓuka abin kirki.
"Ghana za ta yi ƙoƙari. Suna da ƙarfi sosai don haka ina tsoron abin da za su iya yi.''
Ɗanjarida mai sharhi kan ƙwallon ƙafa a Turai, Julien Laurens ya ce: "Ina sane cewa Sifaniya ta yi rashin nasara a hannun Portugal a wasan ƙarshe na Nations League, amma tawagar tana ƙoƙari sosai tun bayan da sabon kocin ta Luis de la Fuente ya fara aiki.
"Mu [Faransa] mun dogara kan Mbappe, kuma bana zaton muna da nakasu a tawagarmu.''
Da ya ke magana a kan Jamu, Laurens ya ƙara da cewa: "A yanzu ba za ka iya yanke hukuncin ko wane irin wasa Jamus za ta buga ba.
"Har yanzu suna da ƙarfi kuma Jamal Musiala zai dawo taka leda a watan Janairu kuma daga nan za mu fahimci ko zai iya zuwa gasar. Kuma idan Florian Wirtz na shanawa, a lokaci guda kuma Musiala na tashe, ga kuma with Nick Woltemade da Kai Havertz lallai akwai tawaga mai kyau.
"Bana da tabbacin yadda bayan tawagar zai kasance dai.
Ɗanjarida daga kudancin Amurka Tim Vickery ya ce: "Brazil ana murna da yadda aka raba ƙasashen.
"Wasanin su a New Jersey, Boston, Philadelphia, Miami, da kuma Atlanta, kuma akwai AC a filayen kuma Carlo Ancelotti na fatan wasannin su zasu zamo wasannin dare ne don haka yana cikin murna.
"Idan Ancelotti zai iya gyara ƴan wasan gabansa su riƙa cin ƙwallaye sosai, kamar yadda suka yi a wasu wasannin sada zumunci da suka buga, to ana iya cewa Brazil za ta yi ba zata.''
Dangane da Argentina, Vickery ya ce: "Suna ƙoƙarin yin abin da ba a taɓa yi ba, babu ƙasar da ta taɓa lashe gasar cin kofin duniya biyu a jere ba a nahiyarta ba.
"Abubuwa na tafiya masu yadda suke so tun bayan lashe gasar. Sun cinye duk wata gasa da suka buga.
"Sun samu gurbin shiga gasar bayan jan ragamar ƙasashen kudancin Amurka kuma sun rage yadda suke dogaro a kan Lionel Messi.''
Rukunnan gasar cin kofin duniya ta 2026
Rukunin A: Mexico, South Africa, South Korea, Winner of Uefa play-off D*
Rukunin B: Canada, Winner of Uefa play-off A*, Qatar, Switzerland
Rukunin C: Brazil, Morocco, Haiti, Scotland
Rukunin D: USA, Paraguay, Australia, Winner of Uefa play-off C*
Rukunin E: Germany, Curacao, Ivory Coast, Ecuador
Rukunin F: Netherlands, Japan, Winner of Uefa play-off B*, Tunisia
Rukunin G: Belgium, Egypt, Iran, New Zealand
Rukunin H: Spain, Cape Verde, Saudi Arabia, Uruguay
Rukunin I: France, Senegal, Winner of Fifa play-off 2*, Norway
Rukunin J: Argentina, Algeria, Austria, Jordan
Rukunin K: Portugal, Winner of Fifa play-off 1*, Uzbekistan, Colombia
Rukunin L: England, Croatia, Ghana, Panama
*Uefa play-off A: Italy, Wales, Bosnia-Herzegovina or Northern Ireland
*Uefa play-off B: Ukraine, Poland, Albania or Sweden
*Uefa play-off C: Turkey, Slovakia, Kosovo or Romania
*Uefa play-off D: Denmark, Czech Republic, Republic of Ireland or North Macedonia
*Fifa play-off 1: DR Congo, Jamaica or New Caledonia
*Fifa play-off 2: Iraq, Bolivia or Suriname











