Mene ne raunin ACL da ke addabar ƴan wasa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Jonty Colman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, BBC Sport
- Lokacin karatu: Minti 4
Anterior Cruiciate Ligament (ACL) wani ɓangaren gwiwar mutum ne da ke haɗe ƙasusuwan gwiwar tare da haddasa motsi.
Idan ACL ya samu rauni, hakan na iya janyo zafi da kumburi, sannan mutum zai rasa ƙarfi a gwiwa - lamarin da zai sa mutum ya kasa ɗora nauyi a ƙafar ko ya iya yin wani abun motsa jiki – musamman wasanni.
Abubuwan da suka fi haddasa ciwon ACL a ƙwallon ƙafa sun haɗa da sauya motsin jiki da sauri cikin wasa ko kuma yadda ƴan wasa ke sauka bayan yin tsalle.
Idan ACL ɗin ɗan wasa ya yage kaɗan ko ya tsinke gaba ɗaya, zai iya jinyar tsawon lokaci da zai iya kai wa kakar wasa guda, domin yana buƙatar kulawar watanni shida zuwa tara.
A wasu lokuta ma jinyar na iya fin haka daɗewa kamar yadda Tyrone Mings da Emiliano Buendia suka yi jinyar fiye da shekara guda.
A halin yanzu ma akwai yiwuwar ƴan wasan Ingila James Maddison da Levi Colwill ba za su buga gasar Premier ba sakamakon wannan raunin.
A wasu lokuta ƴan wasa ba sa iya dawowa ganiyarsu saboda tsananin ciwon da muka tsoron sake jin raunin.
Me ya sa jinyar ACL ke ɗaukar lokaci?

Asalin hoton, Getty Images
Warkewa daga ciwon ya danganta da shekarun ɗan wasa da tsananin ciwon da kuma yadda jikin ɗan wasan yake bayan yi masa tiyata.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ben Warburton – likitan gashin ƙashi wanda yana da sabo da ciwon ACL, sakamakon aiki a ƙungiyar wasan Rugby na Cardiff City da ƙungiyar Scarlets da kuma tawagar wasan Rugby na Wales.
Warburton ya ce ɗan wasa na buƙatar aƙalla wata shida bayan tiyata kafin yakoma taka leda.
"Idan aka yi maka tiyata, an shafi abubuwa da yawa a cikin gwiwar," ya bayyana. "Idan waɗannan suka warke, dole ka bi a hankali tsawon watanni uku. Bayan nan za ka iya atisaye.
"Sannan a zo batun dawowa ganiya da atisaye, da kuma dawo da ƙarfin ƙafa da kuma yin guje-guje da kuma buga wasanni. Shi yasa yake ɗaukar lokaci."
Warburton ya ce ƴan wasan da suka dawo wasa wata shida bayan tiyatar ACL sun fi yiwuwar sake jin ciwon fiye da waɗanda suka kwashe watanni tara.
"Za ka iya yin wasa ma kafin wata shida ya cika, amma dai caca ce", Warburton ya ƙara.
"Ba da yawan likitoci ne za su shawarci haka ba. Ana dai yi kuma a samu nasara amma wannan babban caca ce"
"A lokuta da dama ana duba ɗan wasan ma", in ji shi
"Idan ɗan wasa ne mai matuƙar muhimmanci a ƙungiya za a fi yin sauri da shi. Idan matashi ne tun da yana da lokaci a gaba, za ka ba shi aƙalla wata tara."
Ko ciwon ACL na iya sa ɗan wasa jingine takalmi?

Asalin hoton, Getty Images
Shekara 10 da suka gabata, ciwon ACL yana tilasta wa ƴan wasa yin ritaya.
Amma Warburton ya ce a zamanain yanzu, ƴan wasan da aka yi musu tiyata na da yiwuwar kashi 90 zuwa 95 cikin 100 na dawowa taka leda.
Hakan ya faru ne saboda ci gaban fasaha da bincike na taimakawa wajen kula da ciwon ACL, musamman salon yin tiyata.
Likitoci na da sabbin kayan aiki da salon aiki na yin tiyatar ACL, ciki har da yin amfani da ƙashin gudunmawa da wasu ɓangarori ma.
"Akwai gwaji da yawa da muke yi wa ƴan wasa da a baya, kamar shekara 10 da suka gabata babu fasahar yin su".
Akwai yiwuwar sake jin ciwon ACL bayan tiyata cikin watanni 12 na farko bayan dawowa yin wasa.
"Abin da ke faruwa shi ne suna dawo wa ne kuma kulawarsu zai ragu sannan su riƙa atisaye da buga wasanni. Wasu lokuta suna rasa ƙarfin ƙafarsu kuma akwai gajiya".
"Dole ka yi a hankali a watanni shida zuwa shekara ɗaya na farko bayan dawowa. Idan ka wuce wannan lokacin to ba ka da matsala da yawa".
Ko mata na jin raunin ACL?

Asalin hoton, Getty Images
Bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar sau biyu zuwa shida cewa maza za su ji ciwon ACL fiye da mata.
A 2022 ƴan wasan Arsenal Leah Williamson da Beth Mead da Vivianne Miedema sun ji ciwon ACL,
Har yanzu dai ana binciken dalilin da ya sa mata suka fi jin ciwon amma ana tunanin yanayin jikinsu na taka rawa.
A farkon shekarar 2025 hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ta bayar da kuɗin bincike domin gano idan al'adda na iya shafar yiwuwar jin ciwon ACL a mata.











