Premier ko La Liga, waɗanne ƙungiyoyi ne suka fi taka rawa a Champions League ta bana?

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyin Ingila na yi wa sauran ƙungiyoyi fyaɗen ƴaƴan kaɗanya a gasar Zakarun Turai ta Champions League, bayan maƙudan kuɗaɗen da suka kashe wajen sayen ƴanwasa.
A yanzu dukkanin ƙungiyoyi shida daga Ingila na sama-saman teburin kungiyoyi 36 da ke fafatawa bayan rabin wasannin rukuni.
A wannan mako, a karo na biyu cikin zagaye uku, ƙungiyoyin Premier biyar sun yi nasara a karawarsu, babu wata ƙasar da ta samu yin hakan.
Hudu daga cikin ƙungiyoyin Ingila shida da ke fafatawa a gasar suna cikin ƙungiyoyi 8 na saman teburi, kuma idan aka ƙare a haka za su samu zuwa zagayen ƴan 16 kai-tsaye. Haka nan kuma dukkanin ƙungiyoyin 6 na cikin 12 da ke saman teburi.
A cikin wasanni 24 da suka buga jimilla, ƙungiyoyin na Premier sun yi nasara a 17 inda suka yi rashin nasara a wasa uku kacal.
Arsenal ce ta biyu a teburin na Champions League da maki 12, inda take biye wa Bayern Munich da bambancin ƙwallaye, kuma Arsenal ce ƙungiyar da har yanzu ba a zura mata ƙwallo ko ɗaya ba a gasar daga farkon wannan kaka.
Nasarar da Manchester City ta samu kan Borussia Dortmund 4-1 a ranar Laraba ne ta cilla ta zuwa matsayi na huɗu, yayin da Liverpool wadda ta yi nasara kan Real Madrid ranar Talata take a matsayi na 8.
Newcastle da ta doke Athletic Bilbao na a amatsayi na 6, inda yanzu ta ci wasanni uku a jere tun bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Barcelona a wasan farko.
Tottenham wadda ita kuma ba ta yi rashin nasara ba awasanninta tana a matsayi na 10 bayan ta lallasa FC Copenhagen da ci 4-0 inda ɗan wasa Micky van de Ven ya ci ƙwallo mai ban sha'awa.
Chelsea na a matsayi na 12 bayan yin canjaras da ƙungiyar Qarabaq ta Azerbaijan 2-2 a ranar Laraba, sai dai da alama ƙungiyoyin biyu za su iya fitowa ko da sun gaza kai wa mataki na gaba kai tsaye.
Saboda haka ba zai zama abin mamaki ba idan dukkanin ƙungiyoyin Ingilar 6 suka samu kai wa zagayen ƴan 16. Idan haka ta faru za su goge tarihin da ƙungiyoyin na Ingila suka kafa a 2017, lokacin da ƙungiyoyi biyar, wato Chelsea, Manchester City, Liverpool, Manchester United da Tottenham duk suka tsallake matakin rukuni.
Shi ne karon farko da ƙungiyoyi biyar daga ƙasa ɗaya suka kai matakin kifa-ɗaya-ƙwala a gasar Champions League.
Yadda ƙungiyoyin Premier suka yi wasa da kuɗi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A lokacin hada-hadar musayar ƴanwasa da ya gabata, ƙungiyoyin Premier sun kafa tarihin kashe maƙudan kuɗaɗe har fam biliyan uku, jimilla.
Kuɗin ya zarce wanda ƙungiyoyin Jamus da Spain da Italiya da Faransa suka kashe idan aka haɗa su kaf.
Wannan ya nuna yadda tallace-tallace da lasisin nuna wasa ke bai wa kungiyoyin na Premier damar samun maƙudan kuɗaɗen da suke kashewa wajen sayo ƴanwasan kece raini.
Matsakaicin kuɗin da ƙungiyar Premier ke samu a kakar wasa shi ne Yuro miliyan 367.7 a shekarar 2024. Inda ƙungiyoyin Bundesliga na ƙasar Jamus ke biye masu da kuɗin shiga kimanin Yuro miliyan 210.9.
Yayin da ake ƙoƙarin ganin an kauce wa haɗa ƙungiyoyin da suka fito daga ƙasa ɗaya su kara a matakin rukuni, ana ganin wannan abu ne da zai bai wa ƙungiyoyin na Premier dama.
Sai dai zai iya yiwuwa a haɗa su da juna idan aka je matakin ƴan 16, duk da dai za su iya kauce wa hakan idan dukkaninsu suka ƙare a cikin ƙungiyoyi takwas na saman teburin gasar ta Champions League a ƙarshen wasannin rukuni.
Haka nan kuma ana ganin cewa ƙungiyoyin Ingila ba su cika nuna ƙwanji ba a wasannin kifa-ɗaya-ƙwala, kamar yadda aka gani a kara da ta gabata, lokacin da Paris St Germaine ta fitar da ƙungiyar Liverpool da Aston Villa da kuma Arsenal kafin lashe kofin.
Manchester City kuma ta yi waje ne a wasannin neman samun gurbi bayan shan kashi a hannun Real Madrid.
Duk da maƙudan kudin da suke samu, ƙungiyoyi uku ne kacal daga Ingila suka lashe kofin Zakarun Champions League a kaka 13 da suka gabata, inda ƙungiyoyin Spain suka lashe sau bakwai.
Sannan idan aka yi la'akari da abin da ya faru a kakar da ta gabata, taka rawar gani a matakin rukuni ba zai kasance shaidar cewa ƙungiya za ta yi ƙoƙari ba a mataki na gaba.
Liverpool ce ta ƙare matsayi na ɗaya bayan kammala wasannin rukuni a kakar da ta gabata, sai ga shi PSG ta yi waje da ita a zagayen ƴan 16, duk kuwa da cewar ƙungiyar ta birnin Paris ba ta fara kakar da ƙafar dama ba, sai daga baya ta farfaɗo ta ƙarisa wasan rukuni a mataki na 15.
Akwai manyan ƙungiyoyin Turai da yawa da za su so samun irin sa'ar da PSG ta yi a bara domin kai wa matakin gaba a bana.
Har yanzu Benfica da Ajax Amsterdam ba su da maki ko ɗaya bayan wasa huɗu yayin da Juventus ke a can ƙasa bayan gaza lashe karawa ko ɗaya.











