Brazil za ta kara da Moroko, Faransa da Senegal a gasar Kofin Duniya ta 2026

Asalin hoton, Getty Images
An raba jadawalin ƙasashen da za su kara a gasar cin kofin ƙwallon ƙafar duniya ta FIFA, 2026 a bikin da aka gudanar a birnin Washington na ƙasar Amurka.
Mai kare kambin, wato Argentina ta tsinci kanta ne a rukunin J, inda za ta kara da Algeria da Austria da kuma Jordan.
Ingila da Ghana za su ɓarje gumi a rukunin L, tare da ƙasashen Croatia da kuma Panama.
Daga Afirka, zakarun nahiyar, wato Ivory Coast za ta kara da ƙasashen Jamus da Ecuador da kuma sabuwar zuwa Curacao a rukunin E.
Moroko wadda ita ma ke taka rawar gani a Afirka za ta haɗu da Brazil da Scotland da kuma Haiti a rukunin C.
An yi bikin raba jadawalin ne a Washington DC, duk da cewa birnin ba zai karɓi bakuncin wasa ko ɗaya ba.
Fifa ta yi amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa wajen fitar da taswirar yadda tawagogin za su yi tata ɓurza a gasar da za a gudanar a baɗi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Ga yadda jadawalin ya kasance
Rukunin A:
- Mexico
- Afirka ta Kudu
- Koriya ta Kudu
- Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin D
Rukunin B:
- Canada
- Qatar
- Switzerland
- Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin A
Rukunin C:
- Brazil
- Moroko
- Scotland
- Haiti
Rukunin D:
- Amurka
- Paraguay
- Australia
- Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin C
Rukunin E:
- Germany
- Ivory Coast
- Ecuador
- Curacao
Rukunin F:
- Netherlands
- Japan
- Tunisia
- Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin B
Rukunin G:
- Belgium
- Egypt
- Iran
- New Zealand
Rukunin H:
- Spain
- Saudi Arabia
- Uruguay
- Cape Verde
Rukunin I:
- France
- Senegal
- Norway
- Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 2
Rukunin J:
- Argentina
- Algeria
- Austria
- Jordan
Rukunin K:
- Portugal
- Uzbekistan
- Colombia
- Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 1
Rukunin L:
- England
- Croatia
- Panama
- Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanda suka jagoranci bikin sun haɗa da Heidi Klum da Kevin Hart da kuma Danny Ramirez.
Kafin a fara raba jadawalin an rakashe da wake-wake da raye-raye daga Andrea Bocelli da Robbie Williams da kuma Nicole Scherzinger.
FIFA ta karrama Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images
Wani babban abin da ya faru shi ne yadda aka karrama shugaban Amurka Donald Trump da lambar yabo ta zaman lafiya ta hukumar FIFA.
FIFA ta ce ta ba Trump wannan lambar yabo ne sanadiyyar rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.
An bai wa Trump lambar yabon mai launin zinare, hannuwa riƙe da duniya a sama.
Ƙasashen da har yanzu ba su kammala wasan cike gurbi ba
Har yanzu akwai wasanni cike gurbi da ba a kammala ba, balle a san takamaimai ƙasashen da za su fito.
Ƙasashen sun rabu zuwa rukuni shida:
Wasan cike gurbi na Uefa rukunin A: Italiya, Wales, Bosnia-Herzegovina, Arewacin Ireland
Wasan cike gurbi na Uefa rukunin B: Ukraine, Poland, Albaniya, Sweden
Wasan cike gurbi na Uefa rukunin C: Turkiyya, Slovakiya, Kosovo, Romaniya
Wasan cike gurbi na Uefa rukunin D: Denmark, Czech Republic, Republic of Ireland, North Macedonia
Wasan cike gurbi na Fifa rukunin 1: DR Congo, Jamaica, New Caledonia
Wasan cike gurbi na Fifa rukunin 2: Iraqi, Bolivia, Suriname

Asalin hoton, Getty Images











