Ta yaya za a samu ƙasar da za ta wakilci Afirka a wasan cike-gurbi na Kofin Duniya?

Ɗan bayan JD Kongo Chancel Mbemba, golan Kamaru Andre Onana, ɗan gaban Najeriya Victor Osimhen da ɗan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasa ɗaya ce kawai za ta samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2026 tsakanin JD Kongo, da Kamaru, da Najeriya da kuma Gabon
Lokacin karatu: Minti 6

A wannan mako ne za a yi wasannin cike gurbi na neman shiga gasar Kofin Duniya tsakanin ƙasashen Afirka.

A waɗannan wasannin ƙasa ɗaya ce kawai za a zaɓa don gasar ta cin Kofin Duniya ta 2026.

Bayan da ƙasashen huɗu - Kamaru, da Najeriya, da JD Kongo da Gabon, suka kasa samun nasara a gurbi tara na samun zuwa gasar kai tsaye, za su tafi Moroko, inda za su fafata a gasar da ƙasa ɗaya kawai za a zaɓa, ita ce wadda ta yi galaba a tsakaninsu.

To amma kuma fa har bayan fafatawar a Moroko, ya danganta da matsayin ƙwazon ƙasar da ta yi nasara, a jadawalin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa, ƙasar za ta sake wasa ɗaya ko biyu kafin ta samu gurbin zuwa gasar ta duniya, wadda za a yi a ƙasashen Kanada da Mexico da kuma Amurka.

BBC ta yi bayanin yadda wannan mataki yake, da kuma abin da za a yi nan gaba.

Ta yaya ƙasashen suka kai wasan cike-gurbi na Afirka?

Ƙasashen huɗu sun kai wannan matsaki ne kasancewar su ne suka fi ƙwazo a matsayin na biyu a rukuni tara na ƙasashen Afirka na neman zuwa gasar ta duniya.

Ba a yi la'akari da sakamakon ƙasa ta shida a rukunai takwas na gasar ba, saboda Eritrea ta janye a ranar jajiberin gasar, inda ta bar rukuninsu na biyar (Group E) da ƙasashe biyar kawai.

Gabon ta fi kowace ƙasa a tsakaninsu, sai JD Kongo sai kuma Kamaru.

Najeriya ta samu kutsawa gasar ne a sanadiyyar bambancin yawan ƙwallaye, bayan da Frank Onyeka ya ci wa Najeriyar ƙwallo a minti na 91, a wasan da ƙasar ta doke Benin da ci 4-0, inda ta kawar da Burkina Faso da ƙwallo ɗaya.

Yaya aka yi jadawalin na ƙasashen Afirka?

An yi amfani da matsayin kowace ƙasa a jerin bajintar hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa, wajen haɗa yadda ƙasashen za su fafata a wasan kusa da na ƙarshe, inda ƙasashen da suka fi matsayi za su fafata da waɗanda suke na ƙasa.

A dalilin haka Najeriya ( wadda take matsayi na 41 a duniya ) za ta kara da Gabon (ta 77) a ranar Alhamis (ƙarfe 5:00 na yamma a gogon Najeriya), kafin Kamaru (ta 54) ta kara da JD Kongo (ta 60) duka a wannan rana (ƙarfe 8:00 na dare)

Waɗanda suka yi nasara a wasan kusa da ƙarshe za su kara ranar Lahadi ( ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya), domin samun damar zuwa gasar ta duniya da za a yi a shekara mai zuwa.

Za a yi dukkanin wasannin uku a babban birnin Moroko, Rabat.

Me zai faru ga wadda ta yi nasara?

Ɗanwasan New Caledonia, Joris Kenon da na Bolivia Enzo Monteiro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, New Caledonia da Bolivia na daga cikin ƙasashen da waɗanda suka yi nasara daga Afirka za su ya haɗuwa da su
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wadda ta yi nasara a tsakanin ƙasashen Afirka za ta ƙara gaba inda za ta haɗu a wata gasar ta ƙasashe shida daga nahiyoyi daban-daban, inda za a yi karawar a watan Maris, inda daga nan ne za a samu ƙasashe biyu da za su je gasar ta Kofin Duniya.

A cikin ƙasashen shida, bayan ta Afirka, biyu za su fito ne daga yankin Amurka ta Arewa, da ta Tsakiya da kuma Karebiyan, sannan za a zaɓo ɗai-ɗai daga Asiya da Oceania da kuma Latin Amurka.

Za a raba waɗannan ƙasashe shida zuwa gida biyu.

Za a ware ƙasashe biyu da suke kan gaba a bajinta a jadawalin Fifa, don kada su haɗu da juna a matakin farko, inda za su kai matakin wasan ƙarshe kai tsaye a rukuninsu, inda su kuma ƙasashe huɗu da suke ƙasa a bajinta za su haɗu a wasan kusa da ƙarshe.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Iraqi za su fafata domin neman gurbin nahiyar Asiya, yayin da Bolivia ke wakiltar Latin Amurka, sai New Caledonia da ke wakiltar Oceania.

Kasancewar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ita ce ta 76 a duniya, yayin da Iraqi take ta 150, wannan zai ƙarfafa damar ƙasar da za ta yi nasara daga Afirka, ta je wasan ƙarshe kai tsaye kawai.

Za a yi wasannin na raba-gardama ne sili-ɗaya-ƙwale kawai - wato karawa ɗaya kuma duk wadda aka ci an yi waje da ita.

Idan wasan ya ci tura za a ƙara lokaci, har ma a kai ga bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida (fanareti).

Wa za su kara da shi a gasar ta Duniya?

Za a fitar da jadawalin gasar ta cin Kofin Duniya ta 2026, a ranar Juma'a, 5 ga watan Disamba, inda za a rarraba ƙasashen 48 zuwa gida 12, kowanne da ƙasashe huɗu.

A lokacin fitar da jadawalin za a san ƙasashe 42 da za su je gasar.

Waɗanda za su rage da ba a sansu ba a lokacin su ne, biyu da za su yi gasar raba-gardama daga nahiyoyi, da kuma guda huɗu na Turai da su ma za su yi wasan raba-gardama.

Saboda haka, ƙasar Afirka da za ta je gasar ta raba-gardama ta nahiyoyi a shekara mai zuwa, za ta iya sanin kusan dukkanin ƙasashen da za ta iya haɗuwa da su a wasan rukuni na gasar cin Kofin Duniya.

Wace ƙasa ce za ta iya fitowa daga Afirka?

Kociyan Najeriya Eric Chelle

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kociyan Najeriya Eric Chelle na shan matsin lamba ya kai ƙasar gasar Kofin Duniya

Wannan tambaya ce mai wuyar amsa lalle.

A takarda dai Najeriya ce ta fi wannan dama, bisa jadawalin Fifa, to amma kuma a duka tsakanin ƙasashen huɗu ita ce ta fi rashin taɓuka abin-a-zo-a-gani a wasannin rukuni na neman gurbin gasar.

Najeriya ta yi masu horarwa uku a lokacin waswanninta na rukuni na uku (Group C), kuma ba ta ƙoƙari a lokacin da Victor Osimhen yake jinya, inda ta samu maki huɗu kawai daga cikin 15 ba tare da tauraron ba.

Amma duk da haka ba a doke ƙasar ba a wasanninta shida na gasa a ƙarƙashin mai horarwa Eric Chelle.

Kamaru ma wata babbar ƙasa ce a tsakanin ƙasashen na Afirka, wadda ba ta yi ƙoƙari ba, inda ta kammala ta maki huɗu a bayan Cape Verde a rukuni na huɗu (Group D).

Tawagar ta Kamaru - (The Indomitable Lions) ta yi nasara ne a wasa ɗaya daga cikin biyar na waje, wanda hakan ba wata alama ce ta ƙoƙari ba idan ta je wata ƙasa wasa a wannan watan.

Kamaru ta kasance ƙasar da ta fi zuwa gasar Kofin Duniya a Afirka, to amma tana buƙatar ta ƙara himma domin zuwa gasarta ta tara.

Hoton Yoane Wissa na JD Kongoder

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, JD Kongo za ta kasance ba tare da ɗan gabanta ba na Newcastle, Yoane Wissa a wasan na raba-gardama

JD Kongo wadda ta taɓa zuwa gasar Kofin Duniya sau ɗaya tilo a lokacin tana

Zaire a 1974, ta gama da maki biyu ne a bayan Senegal a rukuni na biyu (Group B).

Tawagra ta kongo (The Leopards ) ta yi sakaci a gidanta, inda ta bari Senegal ta farke ƙwallo biyu da ta zura mata har ma baƙin suka ƙara ta uku aka tashi 3-2 a watan da ya wuce.

Har yanzu tauraron ɗan wasan gaban Kongon na Newcastle Yoane Wissa yana jinya, amma kuma Cedric Bakambu na kan ganiyarsa a lokacin wasannin neman gurbin inda ya ce ƙwallo huɗu.

Gabon, wadda ke neman zuwa gasar ta Duniya a karon farko ta kammala wasannin rukunin a bayan Ivory Coast ta ɗaya da bambancin maki ɗaya a rukuni na shida (Group F).

Gabon na alfahari da taurarin 'yan wasa na gaba - Denis Bouanga, wanda ya ci ƙwallo 8, da Pierre-Emerick Aubameyang, da ya ci 7, a wasannin rukuni.

Yawancin ƙwallayen da Aubameyang ya ci ya zura su ne a lokacin da ya ɗaga ragar Gambia sau huɗu a watan da ya wuce kafin daga bisani alƙalin wasa ya kore shi, kodayake yanzu ya dawo daga hukuncin.