Mun ƙagu mu kai Najeriya gasar Kofin Duniya ta 2026 - Osimhen

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Oluwashina Okeleji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Marubucin Wasanni
- Lokacin karatu: Minti 3
Ɗanwasan gaba na Najeriya Victor Osimhen ya ce tawagar Super Eagles za ta zaƙu sosai don ganin ta yi nasara a wasannin neman gurbin gasar Kofin Duniya ta 2026.
Ɗanwasan na ƙoƙarin ya samu buga gasar a karon farko bayan Najeriya ta gaza samun gurbi a gasar ta 2022 da Qatar ta karɓi baƙunci.
Sai dai Najeriya ba ta ci wasa ko ɗaya ba a Rukunin C, inda ta yi canjaras a wasanta uku na farko kuma Osimhen bai buga ko ɗaya daga ciki ba saboda rauni.
"Burin kowane ɗanwasa ne ya buga gasar Kofin Duniya, ganin matsayinmu a rukuni kuma yanzu ya sa na zaƙu kamar sauran 'yanwasan don na samu gurbi a 2026," kamar yadda Osimhen ya shaida wa BBC Sport Africa.
"Mun fuskanci ƙunci a a 2022 kuma ba zai yiwu mu sake bari haka ta faru ba gare mu da ma wannan ƙarnin namu.
"Ba za ka so ka gama sana'ar ƙwallo ba kana nadamar rashin taka leda a gasar Kofin Duniya. Ba abin da nake so wa kaina kenan ba."
Najeriya tana mataki na biyar da tazarar maki huɗu tsakaninta da Rwanda ta ɗaya, kuma za ta ziyarce ta a Kigali ranar 21 ga watan Maris kafin ta karɓi baƙuncin Zimbabwe kwana huɗu bayan haka.
Sabon koci Eric Chelle zai buƙaci kyakkyawan sakamako da gaggawa a matsayinsa na koci na uku da ya jagoranci Eagles ɗin a wasannin neman gurbin tun daga watan Nuwamban 2023.
Jose Peseiro ne ya fara buga canjaras biyu a wasan Lesotho da Zimbabwe, sai Finidi George ya yi rashin nasara a hannun Benin da kuma canjaras da Afirka ta Kudu.
'Kurakuran baya'

Asalin hoton, Getty Images
Osimhen mai shekara 26 kuma gwarzon ɗanƙwallon Afirka na 2023, ya ce tawagar da ke da manyan 'yanwasa kamar Lookman, da Simon, da Bassey, da Iwobi dole ne ta samu gurbin shiga Kofin Duniya da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Sau biyu kacal Najeriya ta kasa zuwa gasar tun bayan da ta fara buga ta a shekarar 1994.
"Mutane kan ce muna ƙwararrun 'yanwasa, amma kuma za mu iya tabbatar da ƙwarewarmu ne kawai idan muka je Kofin Duniya kamar waɗanda suka buga kafinmu," in ji Osimhen.
"Na ji ɓacin rai sosai kamar sauran abokan wasana bayan mun kasa zuwa Qatar, su kansu magoya baya ba su san irin yadda hakan ya girgiza mu ba.
"Wannan ta sa dole mu gyara kurakuran da muka yi a baya ta hanyar hidimta wa ƙasarmu, da sabon kocinmu, sannan mu nuna cewa mun cancanta."

Asalin hoton, Getty Images











