Ciwon hanta da hanyoyin kamuwa da shi

Hanta
Lokacin karatu: Minti 3

Yau ce ranar yaƙi da cutar ciwon hanta ta duniya, kuma hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane da dama ne ke ɗauke da wannan cuta wadda a Turance ake kira Hepatitis, amma ba tare da sun sani ba.

Alƙaluma sun nuna cewa, miliyoyin mutane ne cutar ta Hepatitis ke hallakawa a faɗin duniya.

An dai ware wannan rana ne domin jawo hankali ga illar wannan cutar, da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin shawo kanta.

Likitoci na shawartar al'umma da su rinƙa zuwa gwajin cutar domin ba kasafai take nuna alamu ba kafin ta yi tsanani.

Mene ne ciwon hanta?

"Duk wata larura da za ta janyo lahani ga hanta ita ce ake kira da ciwon hanta," in ji Dr Yusuf Shehu Umar, ƙwararren likitan sassan da suka jiɓanci cikin ɗan'adam a asibitin ƙwararru na Murtala da ke Kano.

Me ke haddasa ciwon hanta?

Ƙwayar cutar hanta

Asalin hoton, Getty Images

Dr Yusuf Shehu Umar, ƙwararren likitan sassan da suka jiɓanci cikin ɗan'adam a asibitin ƙwararru na Murtala da ke Kano, a kwanakin baya ya shaida wa BBC Hausa wasu daga cikin manyan dalilan da ke sa mutane kamuwa da cutar hanta kamar haka:

  • Ƙwayoyin cuta na virus ko bacteria
  • Magungunan gargajiya ko na bature
  • Shan barasa da kayan maye
  • Yawaitar kitse a jikin ɗan'adam

Hukumar insorar lafiyar Burtaniya ta tabbatar da cewa aƙalla mutum 3,000 a ƙasar suka kamu da cutar HIV da ta hanta nau'in C sakamakon ƙarin jini da aka yi musu a lokutan agajin gaggawa.

Baya ga ƙarin jini, a kan iya ɗaukar cutar hanta ta hanyar jima'i sannan uwa ka iya bai wa jaririnta da ke ciki da dai sauransu.

Nau'in ciwon hanta

Ciwon hanta ko kuma Hepatitis na da nau'i da yawa kuma ta kasu kamar haka:

  • Ciwon hanta ajin A
  • Ciwon hanta ajin B
  • Ciwon hanta ajin C
  • Ciwon hanta ajin D
  • Ciwon hanta ajin E

Sai dai kuma Dr Yusuf Umar ya ce nau'in da suka fi illa da haɗari su ne ajin A da na B.

"Ita ciwon hanta ajin B wato Hepatitis B tana da rigakafi. Amma ita Hepatitis C ba ta da rigakafi amma kuma maganinta na warkarwa ɗari bisa ɗari."

Ciwon hanta ajin B

Bincike ya nuna cewa ciwon hanta nau'in B wato Hepatitis B ya fi yawa a tsakanin al'umma, inda mutum fiye da miliyan 300 ke ɗauke da cutar sannan kuma tana kashe mutum sama da miliyan ɗaya a duk shekara.

Dangane kuma da girman cutar hanta nau'in B a Najeriya, Dr Yusuf Shehu Umar ya ce fiye da kaso 8 na ƴan ƙasar na fama da wannan cuta.

"Bisa binciken da gwamnatin tarayya ta yi shekara uku zuwa huɗu da suka wuce, fiye da kaso 8.2 na yawan al'ummarmu na fama da wannan cuta."

Alamomin cutar hanta

Dr Shehu Yusuf Umar ya ce mafi yawancin masu ɗauke da cutar ba sa nuna alama da farko har sai bayan da cutar ta yi nisa tukunna sai alamu su bayyana. Ga kaɗan daga cikin alamomin cutar:

  • Yawan ciwon ciki
  • Kumburin ciki
  • Sauyawar launin ido zuwa rawaya
  • Yawan zazzaɓi
  • Kumburin ciki (idan cutar ta yi tsanani)
  • Kumburin ƙafa(idan cutar ta tsananta)
  • Aman jini (lokacin da cutar ta tsananta)
  • Sambatu (bayan tsanantar cutar)