Yaran da aka haifa da ƙwayoyin halittun mutum uku ba za su gaji cutuka ba

Ƙafar jariri

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, James Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 6

An haifi jarirai takwas a Birtaniya ta amfani da kwayoyin halitta daga mutum uku domin hana yaduwar cututtuka masu tsanani da ba su da magani, in ji likitoci.

Wannan hanya, wadda masana kimiyya na Birtaniya suka ƙirƙira, tana haɗe ƙwai da maniyyi daga uwa da uba da kuma ƙwai na biyu daga wata mata daban.

An halatta wannan tasari ne a ƙasar tsawon shekaru goma da suka wuce, amma yanzu ne aka samu tabbacin cewa tana taimakawa wajen haifar yara ba tare da gadon cutar mitochondria da ke shafar ƙwayoyin halitta da ba a warkewa ba.

Wannan cuta ana gadon ta ne daga uwa zuwa yaro, kuma tana hana jiki samun isasshen kuzari.

Wannan cuta na iya janyo nakasa mai tsanani, kuma wasu jarirai kan iya mutuwa cikin kwanaki kaɗan bayan haihuwa. Ma'aurata sun sn da cewa suna cikin haɗari idan suna da yara ko dangin da suka taba kamuwa da cutar, ko kuma idan uwarsu tana da ita.

Yaran da aka haifa ta hanyar amfani da wannan hanyar suna gadon mafi yawan kwayoyin halittarsu daga iyayensu na haihuwa, amma kuma suna gadon ƙwayoyin alitta ƙadan – kusan kashi 0.1 – daga macen ta biyu da ta ba da ƙwanta. Wannan sauyi yana yaɗuwa ne har zuwa yaran da za a haifa.

Dukkan iyalan da suka bi wannan hanyar wajen haifar ƴaƴansu basu fito fili sun yi magana ba domin kare sirrinsu, amma sun fitar da bayanai ta hanyar cibiyar haihuwa ta Newcastle Fertility Centre inda aka gudanar da ayyukan.

'Cike da godiya sosai'

"Bayan shekaru na rashin tabbas, wannan tsarin na amfani da ƙwayoyin halitta daga mutum uku ya kawo mana mafita – sannan ta hanayr tsarin ne muka haifi jaririyarmu," in ji mahaifiyar wata yarinya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ga yarinyar mu muna kallon ta cikin ƙoshin lafiya da fata, kuma muna cikin matuƙar godiya."

Uwar wani ɗa namiji ta ƙara da cewa "Ina matuƙar godiya ga wannan ci gaba mai ban mamaki da goyon bayan da muka samu, iyalinmu ya cika farin ciki yanzu.

An sauke nauyin damuwar cutar mitochondrial daga zuciyarmu, kuma abin da ya maye gurbinta shi ne fata da farin ciki, da godiya "

Cutar mitochondria ƙananan ƙwayoyin halitta ne da ke cikin kusan kowanne daga cikin ƙwayoyin jikinmu. Su ne suke sa mu numfashi saboda suna amfani da iskar oxygen don canza abinci zuwa kuzari wanda jikinmu ke amfani da shi.

Mitochondria masu lahani na iya sa jiki ya rasa isasshen kuzari don ci gaba da bugun zuciya, haka kuma suna iya haifar da lahani ga ƙwaƙwalwa da farfaɗiya da makanta da raunin tsoka, da gazawar wasu gaɓoɓin jiki.

Kusan ɗaya cikin jarirai 5,000 ne ake haifa da cutar mitochondria.

Ƙungiyar bincike a Newcastle na tsammanin akwai buƙatar haihuwar jarirai 20 zuwa 30 a kowace shekara ta hanyar amfani da wannan hanyar "ƙwayoyin halittar mutum uku."

Wasu iyaye sun sha wahala tare da rasa 'ya'yansu da dama sakamakon waɗannan cututtuka.

Mitochondria ana gadansu ne daga uwa zuwa ɗa. Don haka wannan sabon tsarin haihuwa yana amfani da kwayoyin halitta na iyaye biyu tare da ƙwan wata mace da da mitochondria ɗin ta bai da rauni.

An fara bincike kan wannan tsarin ne fiye da shekaru goma da suka wuce a Jami'ar Newcastle da Asibitocin Newcastle upon Tyne NHS Foundation Trust, sannan aka buɗe wani sabis na musamman kan wannan tsarin a cikin tsarin kiwon lafiya na gwamnatin Birtaniya (NHS) a shekarar 2017.

Wannan hoton na nuna matakan da ake bi wajen aiwatar da tsarin amfani da ƙwayoyin halitta uku domin samun haihuwa da kiyaye cutttuka.

Ana haɗa kwai daga uwa da kuma na macen da ta bayar da ƙwai da maniyyin uba a dakin gwaje-gwaje.

Ƙwayoyin halitta na Embriyo ɗin suna ci gaba da girma har sai DNA daga maniyyi da kwai sun samar da abubuwa biyu da ake kira "pro-nuclei". Waɗannan sune ke ɗauke da tsarin gina jikin ɗan adam, kamar launin gashi da tsayi jariri.

Ana cire pro-nuclei daga embriyo biyu, sannan a saka DNA na iyaye cikin embriyo da ke ɗauke da mitochondria mara rauni.

Jaririn da zai taso daga wannan tsarin yana da nasaba da iyayensa ta hanyar gado, amma ba zai kamu da cutar mitochondria ba.

Wani rahoto daga mujallar New England Journal of Medicine ya nuna cewa iyalai 22 ne suka bi wannan hanyar domin samun haihuwa a Cibiyar Haihuwar Newcastle. Wannan ya haifar da haihuwar yara takwas – maza huɗu da mata huɗu – ciki har da tagwaye guda ɗaya, tare da wata mata mai juna biyu d ta kusan haihuwa.

Farfesa Bobby McFarland, daraktan Hukumar NHS mai kula da cututtuka masu tsanani na mitochondria, ya shaida wa BBC cewa:

"Yana da matuƙar daɗi ganin farin ciki da jin daɗin iyayen waɗannan jarirai bayan dogon jiran lokaci da tsoron abin da zai iya faruwa. Abu ne mai ban sha'awa ganin waɗannan jarirai suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, suna girma da ci gaba yadda ya kamata."

An haifi dukkan jariran ba tare da cutar mitochondria ba

Ƙwallon ƙananan ƙwayoyin halitta masu siffar ƙwallo, guda shida ne kawai ake iya gani, waɗanda suke ƙunshe da farkon matakin embryo.

Asalin hoton, Getty Images

An sami wani lamari na cutar farfadiya, wanda ya warke da kansa, sannan wani yaro na da matsala ta zuciya da ba amma ana samun nasara wajen kula da shi.

Ba a ɗauka cewa waɗannan matsalolin suna da alaƙa da mitochondria masu lahani ba. Ba a san ko wannan wani ɓangare ne na haɗarin da aka sani na IVF (na'urar dasa ɗa), ko kuma wani abu na musamman da ya shafi hanyar haihuwar ta amfani da ƙwayoyin halittar mutum uku ba, ko kuma kawai an gano shi ne saboda ana sa ido sosai kan lafiyar duk jariran da aka haifa ta wannan hanyar.

Wani muhimmin tambaya da ke akwai shi ne, ko mitochondria masu lahani za su iya wucewa zuwa cikin ƙwayoyin halitta ta embryo mai lafiya, da kuma abin da hakan zai iya haifarwa.

Sakamakon ya nuna cewa a cikin shari'o'i biyar, ba a iya gano mitochondria masu lahani kwata-kwata ba. A sauran guda uku, tsakanin kashi 5% zuwa 20% na mitochondria aka samu suna da lahani a cikin samfurin jini da na fitsari.

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton mitochondrion da aka ɗauka da na'urar hangen ƙwayoyin halitta – ana iya samun ƙwai har zuwa rabin miliyan a ciki.

Farfesa Mary Herbert daga Jami'ar Newcastle da ta Monash ta ce:

**Yin ƙarin bincike domin fahimtar cutar mitochondria zai zama dole don ƙara inganta nasarar jinyya."

Wannan gagarumin ci gaba ya ba wa iyalan Kat Kitto fata.

Ƙaramar yarinyar Kat mai suna Poppy, mai shekaru 14, tana ɗauke da cutar. Babbar 'yarta Lily kuma, kuma ƴa'ƴan babbar yarinta ƴar shekara 16 za su iya gadon cutar nan gaba.

Poppy dai ba ta iya tafiya, tana amfani da keken guragu, ba ta iya magana, kuma ana ba ta abinci ta hanyar bututun ciyarwa.

"Cutar ta shafi babban ɓangare na rayuwarta," in ji Kat. "Muna jin daɗin rayuwa da ita yadda take, amma akwai lokuta da za ka gane yadda cutar mitochondria ke da muni sosai."**

Kat Kitto tare da ƴarta Lily da karensu

Asalin hoton, BBC/Josh Elgin

Bayanan hoto, Kat Kitto tare da ƴarta Lily da karensu

Duk da shekaru da dama na bincike, har yanzu babu maganin cutar mitochondria, amma damar hana wucewarta zuwa ga yara na gaba na ba Lily fata.

'Birtaniya ce kaɗai za ta iya yin haka'

Birtaniya ba kawai ta haɓaka ilimin haihuwar jarirai daga ƙwayoyin halittar mutum uku ba, ita ce ƙasa ta farko da ta kafa doka domin halasta hakan bayan kaɗa ƙuri'a a majalisa a 2015.

Farfesa Sir Doug Turnbull daga Jami'ar Newcastle ya ce:

"Ina ganin babu wata ƙasa da za ta iya aiwatar da haka sai Birtaniya — daga bincike mai inganci, zuwa doka, zuwa taimakon NHS — yanzu muna da yara takwas da ba su da cutar mitochondria. Wannan babban nasara ce."

Liz Curtis, wanda ta kafa ƙungiyar taimako ta Lily Foundation, ta ce:

"Bayan shekaru da dama na jiran sakamako, yanzu mun san cewa an haifi jarirai takwas ta wannan hanya, duk kuma ba su nuna alamar ɗauke da cutar mitochondria ba.

"Ga iyalai da dama da abin ya shafa, wannan shi ne farkon haƙiƙanin fata na kawo ƙarshen wannan cuta ta gado."