Yin tattaki kafa 7,000 a kullum na rage haɗarin kamuwa da cututtuka - Bincike

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Josh Elgin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Yin tattaki kafa 7,000 a kullum shi kaɗai yana ƙara wa kwakwalwa lafiya da kuma taimakawa mutum daga kamuwa da cututtuka daban-daban, kamar yadda wani bincike ya gano.
Abu ne mai kyau bayan da aka amince da tattakin kafa 10,000 a can baya, a matsayin iya adadin ya kamata mutum ya yi.
Bincike wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet, ya gano cewa yin tattaki kaɗan ma yana da alfanu wajen rage barazanar kamuwa da cutuka masu tsanani, ciki har da kansa da cutar mantuwa da kuma cutukan zuciya.
Har ila yau, binciken ya kuma bai wa mutane shawarar cewa su riƙa bibiyan irin tattakin da suke yi a matsayin wata hanya ta inganta lafiyarsu, kamar yadda masu binciken suna bayyana.
"Muna sane cewa ya kamata mu riƙa yin tattaki kafa 10,000 a kullum," a cewar jagoran masu binciken Dakta Melody Ding, "sai dai babu wata hujja da ta bayyana haka cewa sai kafa 10,000."

Asalin hoton, Getty Images
An bayyana yin tattakin kafa 10,000 ne a can baya a 1960 a lokacin wani kamfe na kasuwanci a Japan. Gabanin fara wasannin Olympics a Tokyo a 1964, an kaddamar da wata na'ura da za ta riƙa ƙirga tattakin da mutum ya yi wadda ake kira manpo-kei - da aka yi wa lakabi da 'na'urar tattaki kafa 10,000'.
Dakta Ding ta ce an sauya ma'anar waɗannan alkaluma kuma ba ka'idoji bane a hukumance, wanda masu motsa jiki da kuma shafuka suka yi ta ba da shawara a kai.
Wannan sabon bincike ya yi nazari kan alkaluma da ake da su a ɓangaren lafiya a kan mutane sama da 160,000 a faɗin duniya.
Binciken ya gano cewa yin aƙalla tattaki kafa 7,000 a rana na rage barazanar kamuwa da cutukan zuciya da kashi 25, cutar kansa da kashi 6, cutar mantuwa da kashi 38 sai kuma rage kamuwa da cutar tsananin damuwa da kashi 22.
Sai dai, masu binciken sun ce wasu abubuwa da suka gano a binciken sun yi shi ne kan ƙananan bincike da suka yi, kuma babu ƙarara ko cewa hakan gaskiya ne.
Bincikensu ya bayar da shawarar cewa ko da tattakin kafa 4,000 ne a kullum na iya inganta lafiya idan aka kwatanta da tattaki ƙasa da hakan - kusan tattaki kafa 2,000 a kullum kenan.
Tattakin na iya fin kafa 10,000 idan ana son samun lafiya mai inganci, musamman ma zuciya.

Asalin hoton, Getty Images
A yanzu, yawancin ka'idoji da hukumomi suka bayar kan motsa jiki a kullum sunmayar da hankali ne kan yawan mintoci da ake shafewa yayin motsa jiki maimakon yin tattaki kaɗai.
Alal misali, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutanen da suka balaga su riƙa motsa jiki na aƙalla mintoci 150 ko kuma 75 a kowace mako.
Dakta Ding ta ce ba da shawara za ta iya kasancewa mai wahala ga mutane, duk da cewa ka'idojin da ake da su a yanzu su ma suna da muhimmanci.
"Akwai mutanen da ke yin iwo, hawa ƙeƙe ko kuma ke da lalurori na rashin lafiya da ta sa ba sa iya yin tattaki," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Daniel Bailey, wani ƙwararre kan lafiya daga jami'ar Brunel a Landan, ya ce binciken ya kuma kalubalanci "camfi" da aka yi cewa ana buƙatar yin tattaki kafa 10,000 a kullum.
Yayin da yin hakan ke da muhimmanci ga waɗanda ke iya yin sa, Bailey ya ce ƙoƙarin yin tattaki kafa 5,000 zuwa 7,000 abu ne da mutane da yawa za su iya yi.
Dakta Andrew Scott, wani babban malami a jami'ar Portsmouth, ya amince cewa saka adadin alkaluma ba shi da muhimmanci.
Ya ce "yin da yawa shi ya fi muhimmanci" kuma kada mutane su damu ka dole sai sun yi wani adadi, musamman a ranakun da ba a yi motsa jiki sosai ba.











