Illolin ɗora wa jariri magani a saman maɗiga

Jariri

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Habiba Adamu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Madiga wani ɓangare ne na ƙoƙon kan jariri da kan kasance babu ƙashi, inda yake rufe da wani yaɗi a ƙarƙashi, sai kuma fata a sama.

Duk da cewa mutane sun fi ganin maɗigar da ke gaban kai - wadda a lokuta da yawa ake ganin tana lotsawa da ɗagowa - amma akwai wasu madigar guda biyar a ƙoƙon kan jariri. Ko da yake girman su ya banbanta.

Masana sun ce maɗiga biyu ne suka fi girma a ƙoƙon kan jariri: ta gaban kai, wadda ake kira 'anterior fontanelle' sai kuma ta baya wadda ake kira 'posterior fontanelle'.

"Lokacin da jariri ke ciki yana da madiga da yawa, amma idan an kusa haihuwa sukan rufe, sai a bar madiga ta gaba da kuma ta baya," in ji Dakta A'isha Zaidu ta asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Mene ne amfanin madiga?

...

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Aisha ta ce maɗiga na da amfani sosai saboda "tana taimakawa ta yadda kai zai yi sauƙin fita daga cikin mahaifa."

Filin da ake samu a ƙoƙon kai, wanda ake kira madiga kan bayar da damar rage girman ƙoƙon kai a lokacin haihuwa ta yadda jariri zai iya fita cikin sauƙi.

Bayan haihuwa kuma Dakta A'sha ta ce maɗiga kan taimaka wajen samar da isasshen fili a ƙoƙon kai lokacin da ƙwaƙwalwar yaro ke ƙara girma.

Jarirai wadanda ke da tsatso daga nahiyar Afrika, madigarsu ta gaba tafi girma, wadda girman kan kama daga 1.4cm zuwa 4.7cm. Yayin da madigar jarirai maza ta fi ta jarirai mata saurin rufewa.

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraron Lafiya Zinariya kan illar ɗora magani kan maɗigar jariri

Yaushe ya kamata maɗiga ta rufe?

Makalar ilimin lafiya ta Amurka ta ce madigar gaban kan jariri ita ce mafi muhimmanci, kuma takan dauki wata 13 zuwa 24 kafin ta rufe. Haka kuma akwai yanayi na kiwon lafiya da dama da kan shafi madigar, wadanda kan iya jefa rayuwar jariri cikin hadari ko salwantar rai.

Maɗiga ta ƙeya ce ke fara rufewa domin wani lokaci takan rufe da zarar an haihu, amma maɗiga ta gaba takan fi ɗaukan lokaci kafin ta rufe.

"Sai dai wasu lokuta idan akwai matsala ko yaro ya samu shigar ƙwayoyin cuta a ƙwaƙwalwa ko ruwa ya taru ko kuma wasu sinadarai masu muhimmanci sun yi ƙaranci a jikin jariri, akan samu yanayin da maɗigar ba ta rufewa da wuri," in ji Dakta A'isha.

Illar ɗora maganin gargajiya kan maɗiga

Al'ada ce kawai take sa ana sanya wasu magunguna a kan maɗiga, in ji Dakta A'isha.

"Wasu na ganin cewa idan madiga na harbawa sama da ƙasa to kamar alamar ciwo ne".

Likitar ta ce wannan ba gaskiya ba ne kuma ɗora wa yaro wani abu a kan madigar na da "illa sosai."

Babbar illar, a cewar Dakta Aisha ita ce maganin da ake ɗorawa kan hana a gane idan madigar ta samu matsala.