Ko wanka a cikin ruwan sama na da illa?

Wata ƴar gudun hijira ta ƙasar Congo na wasa cikin ruwan sama a sansanin Cishemere da ke kusa da Buganda, ranar 6 ga watan Mayun 2025

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ko domin sha ko wanka da ko sauran ayyuka, ruwan sama wani muhimmin abu ne a rayuwar ɗan'adam.

Bincike ya nuna cewa an fara samun ruwan sama a doron duniya ne shekaru biliyan huɗu da suka gabata. Saboda haka an daɗe ana ruwa a duniya.

A lokuta na damina yara har ma da wasu manya kan yi wanka a cikin ruwan sama, wasu kuma hakan na faruwa ne ba tare da son ransu ba - idan suka sha dukan ruwa.

Sai dai duk da cewa zuciyarku za ta iya raya muku ku shiga cikin ruwan sama ku yi wanka domin nishaɗi, ana bayar da shawarar guje wa amfani da ruwan da ba a tabbatar da tsaftar sa ba wajen yin wanka.

Dakta Umar Abdullahi, ƙwararren likitan fata a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce "shi ruwan sama ruwa ne da ake kallo a matsayin mai tsafta, musamman idan yana sauka kai tsaye".

Bincike ya nuna cewa inda wanka a cikin ruwan sama ke da haɗari wuri biyu ne: a lokacin da ruwan ya bi ta saman rufi ya hadu da ƙwayoyin cuta, da kuma yadda yake iya haifar da mura sanadiyyar sanyi.

Sai kuma tasirin da yakan yi a kan fatar ɗan'adam sanadiyyar ɗan bambancin da ke tsakaninsa da ruwan da aka riga aka tace.

Yawan sinadarin 'acid'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani abu kuma shi ne ruwan sama na ƙunshe da sinadarin 'acid' fiye da ruwan da aka tace. Wannan yawa na sinadarin 'acid' zai iya haifar da bushewa ko ma darewar fata tare da haifar da wasu lalurori ko ƙuraje.

Ruwan saman na zama haka ne sanadiyyar abubuwan da yakan haɗu da su a hanyarsa ta faɗowa ƙasa.

Dakta Umar Abdullahi ya ce: "Ya danganta da yanayin fatar mutum, idan fatar mutum ba ta da ƙwari sosai zai iya samun ƙuraje, saboda sanadarin pH da na ruwan ya yi ƙasa".

Ƙwayoyin cuta

A lokacin da mutum ke wanka a cikin ruwan sama, yakan ci karo da ruwan da ke gangarowa daga saman rufi, wanda hakan ke nufin akwai yiwuwar ruwan ya kwaso datti ko kuma ƙwayoyin cuta waɗanda ba za a iya gani da ido ba, waɗanda ake kira 'bakteriya'.

Dattin da ruwan saman kan iya kwasowa daga saman kwano sun haɗa da kashin tsuntsaye ko kuma ƙura.

Zai iya yiwuwa a sa'ilin wanka cikin ruwan mutum ya haɗiye irin wannan ruwa mai ƙunshe da ƙwayoyin cutar da za su haifar masa da rashin lafiya.

Mura

Ba ruwan saman ne shi kansa ke haifar da mura ba, kasancewar ƙwayoyin 'virus' ne ke haifar da ita.

Sai dai sanyin da jikin mutum zai ci karo da shi a lokacin wanka da ruwan sama "zai iya saukar da yanayin ɗumin jiki, wanda hakan zai iya raunana garkuwar jiki, ya ƙara haɗarin kamuwa da cuta da zarar ya ci karo da ƙwayoyinta.

Ƙaruwar sinadaran PFAS a cikin ruwan sama

...

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai wani bincike ya nuna cewa a yanzu ruwan sama a yankuna mafi yawa na duniya na ƙunshe da wasu sanadarai waɗanda yawansu "ya kai" yadda zai iya yin illa ga mutane.

Waɗannan sanadarai su ne ake kira PFAS, waɗanda ake kira 'poly- and perfluoroalkyl substances' a turance, ana amfani da su ne a cikin kunfar kashe gobara da kuma kayan kariya daga ruwan sama.

Wani bincike da masana kimiyya ke yi ya nuna akwai damuwar cewa irin waɗannan sanadari na iya cutar da lafiya ta hanyar cutuka kamar kansa/daji.

Wani masanin kimiyya a Jami'ar Lancaster da ke Birtaniya, Farfesa Crispin Halsall ya ce "nan gaba za a fi ganin tasirin waɗannan sanadari a lafiyar bil'adama."

"Ta yaya illar za ta bayyana? Shi ne abin da ban sani ba to amma tabbas za a gani, domin kuwa (yawan sanadaran) na zarce abin da ya kamata kuma zai yi illa, musamman ganin cewa za a same su a cikin ruwan sha," in ji farfesan.

Sanadaran, waɗanda ake kira 'poly- and perfluoroalkyl substances' a turance.

Shawara kan amfani da ruwan sama

Yawancin abin da mutane ke amfani da ruwan sama, shi ne wajen wanka ko kuma sha.

Dakta Umar Abdullahi ya ce "wasu na ganin cewa ruwan sama kamar wani magani ne, to amma ko da mutum zai sha ya tabbatar ya tare shi ta hanya mai tsafta ko kuma an tsaftace shi ta hanayar dafawa ko kuma amfani da sanadarin alam".

Haka nan ya bayar da shawarar guje wa amfani da ruwan farko ko na biyu ko na uku bayan saukar damina.

A duk lokacin da mutum ya yi wanka cikin ruwan sama ana bayar da shawarar gaggauta yin wanka da ruwan famfo ko kuma wani ruwa da aka tsaftace domin rage bushewar fata.

Haka nan masana na bayar da shawarar shafa mai domin ƙara danshin da ke jikin fatar ɗan'adam.