Abin da ya sa ba a son a yi wanka idan ana ruwa da walƙiya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da yanayi ta Birtaniya, Met Office, ta fitar da gargadin samun mamakon ruwan sama da cida da iska mai arfi a fadin kasar, wanda zai zo da walƙiya da tsawa.
Duk da cewar akwai yiwuwar faɗuwar tsawa, yana kuma da muhimmanci a san yadda za a kare kai lokacin da ake tsawa da walƙiyar.
An bayyana cewa tsawa tana kashe mutum 24,000 duk shekara a faɗin duniya – da ƙarin mutum 240,000 da ke jikkata.
A duk mace-mace 50 da ake samu a duniya, to ɗaya na faruwa ne a Brasil, wadda ita ce kasar da ke tsahun gaba a duniya da tsawa ke yawan faɗuwa.
Yawancin mutane na sane da hanyoyin kare kai lokacin da ake tsawa, kamar gujewa tsayawa a ƙarƙashin bishiyoyi ko kuma kusa da tagogi da kaucewa amfani da wayoyin salula.
Amma kun san ya kamata kuma ku gujewa yin wanka ko wanke-wanke yayin da ake tsawa da walƙiya?
Domin sanin me yasa, da farko ya kamata ka san mece ce tsawa da yadda take aiki.
Abubuwa biyu ne ke haddasa samun tsawa: yanayin zafi da kuma iska me zafi da ke kaɗawa, waɗanda ke tafiya daidai da lokacin bazara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanayin zafi na ƙara yawan iska mai zafi, waɗanda ke haɗuwa su janyo tsawa. Gajimare na ɗauke da miliyoyin ɗigon ruwa da ƙanƙara – inda haɗuwarsu shi ne abin da ke janyo a samu afkuwar walƙiya. Ɗigo-ɗigon ruwa da ke fitowa na haɗuwa da ƙanƙarar da ke zubowa, wanda ke sa su ba da wani martani na daban. A lokacin da ake tsawa, gajimare na kasancewa kamar manya-manyan injuna na Van de Graaf da ke sauyawa zuwa nau’ukan hasken lantarki domin rabuwa da gajimare. Yayin da gajimare ke matsawa kusa da samaniya, suna samun ƙarfi zuwa kasa, wanda hakan ne ke jawo a samu walƙiya zuwa a kasa. Walƙiya haɗe da tsawa na kokarin daidaita yanayin – suna yin hakan ne ta hanyar aikewa zuwa yankuna. Wani bangare na yanayin na gamuwa da turjiya, inda tsawa ke saurin fadowa kan abubuwa da ke waje kamar ƙarafuna da sauransu. Shawarar da ta dace a irin wannan lokaci na tsawa ita ce: da zarar mutum ya ji alamar tsawa, to kawai ya shiga cikin ɗaki.
Sai dai hakan ba yana nufin kwata-kwata mutum ya kubuta daga fadowar tsawa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai wasu ayyuka da mutane ke yi a waje wadanda ke da hadari kamar zama a waje lokacin da ake tsawa.
In ba wai mutum yana wanka a waje ko cikin ruwan sama ba, da wuya tsawa ta shafi mutumin.
Amma idan tsawa ta fada gidanka, hasken lantarki zai bi wajen zuwa kasa.
Abubuwa kamar wayoyi da ƙarafuna ko kuma magudanan ruwa, na samar da saukakkiyar hanyar da wutar lantarki zai bi zuwa kasa. Zai iya juyar da wannan wanka zuwa wani abu na tashin hankali. Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Amurka, ta umurci mutane da su guji shiga ruwa lokacin da ake tsawa – har ma da wanke-wanke – domin rage afkuwar hadari.
Akwai wasu hadura da ya kamata a kaucewa yayin da ake tsawa.Wani abu da mutane ke yi shi ne jingina da bango.
Bango ba wuri ne mai kyau na jingina ba idan an gina shi da ƙarafa, wanda hakan zai jawo afkuwar walƙiya da tsawa. Ya kamata kuma mutane su guji amfani da duk wata nau’ra da aka saka a caji kamar komfuta da talabijin da wanke-wanke saboda dukkan wadannan za su iya haddasa tsawa. Abin da ya kamata mutane su yi shi ne, idan za ka ji alamar tsawa daga nesa, to tsawar tana kusa da inda kake, ko da kuwa babu ruwan sama. Tsawa ta kan isa waje mai nisan kilomita 16 daga inda aka jiyo ta. Bayan jin alamar tsawa da rabin sa’a, to shi ne lokacin da ya kamata mutum ya shiga wankan da ya yi niyya. A yawan lokuta, walkiya hade da tsawa na farowa da kadan, inda ta baya ke fin ta farkon karfi.











