Ganyayyaki biyar masu inganta lafiyar ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Masu iya magana kan ce lafiya uwar jiki. Babu mamaki shi ya sa a wannan zamanin mutane suka rungumi ɗabi'ar shan ƙwayoyi da ke samar da sinadarin da jiki ya rasa.
A gefe guda kuma ana yawaita samun korafe-korafe kan cututtuka da dama da ke damun mutane.
Haka zalika masana da ƙwararru na ba da shawarwarin cewa wasu daga cikin cututtukan na da alaƙa da nau'ika ko ire-iren abincin da mu ke ci.
Masana lafiya na yawaita bada shawarwari cin abinci mai gina jiki da amfani da ganyayyeki wajen daidaita sinadaran da jiki ke bukata saboda ingantuwar lafiya a maimakon wasu ƙwayoyin da ake sha.
Wannan ne ya sa muka yi nazari kan ganyayyeki biyar da kwararru suka yi imanin cewa su na da matuƙar muhimmanci a jikin ɗan adam.
Mun tattauna da Maijidda Badamasi da kuma Aliyu Dauda dukkaninsu na da ƙwarewa wajen abinci da tsarin abinci mai gina jiki.
Sun shaida mana cewa yawaita cin waɗannan ganyayyeki na taimakawa wajen kare ko yaƙar wasu cututtuka da suka yawaita a wannan zamanin da kuma bai wa jiki kuzarin da ya ke bukata.
Ganyen Zogale

Asalin hoton, Getty Images
Zogale ba boyayyan ganye ba ne kuma yana da dimbin alfannu ga lafiyar ɗan adam saboda sinadaran da ya ke ƙunshe da shi.
Ana samun bishiyar zogale galibi a ƙasashen Afirka da Asiya da kuma yankin Kudancin Amurka.
Ana ƙiran zogale da ganyen al'ajabi a wasu yankuna na Afirka saboda abubuwan ban mamaki da ya ke yi a jikin ɗan adam.
Bishiyar zogale kama daga ganyenta da ƴaƴan itattuwan da komai na jikinta na da amfani sosai ga lafiyar jiki.
Itacen zogale kan fito har a wurin da babu ruwa, hakan ya sa ganyensa da sassaƙensa duka suna da amfani.
Ya na ƙunshe da sinadaran A,B, C,D har da E ma. Kuma yana ɗauke da Calcium, Potassium.
- Abubuwa 10 da zogale ke yi a jikin ɗan'adam
- Yana ƙunshe da sinadaran vitamins da minerals
- Yana da sinadarin amino acids da ke gina jiki
- Yana karfafa garkuwar jiki da taimakawa wajen yaƙi da cuttuka masu haɗari da kuma saurin warkar da ciwo
- Yana ƙunshe da sinadaran da ke kare sassan jiki daga lalacewa da samun illa, irinsu zuciya da ƙwaƙwalwa
- Yana daidaita sukari da hawan jini a jikin ɗan adam
- Ya na ƙara kuzari
- Ya na taimakawa mata wajen inganta lafiyarsu da haihuwa
- Ya na wanke ciki da narka ƙitse
- Ya na ɗauke da sinadarin kariya daga Kansa
- Ya na gyaran fata da gashi
Ganyen Alayyahu

Asalin hoton, Getty Images
Alayyahu fitaccen ganye ne a kusan duk faɗin duniya.
'Yan Afirka da Turawa na mutunta ganyen sosai kuma ana yawan cin ganyen.
Alayyahu kore ne shar kuma yana ɗaya daga cikin ganyayyaki da aka fi amfani da su a ƙasar Hausa, sai dai mutane da dama ba su san amfanin da ya ke da shi ga lafiyarsu ba.
Ganyen Alayyahu iri-iri ne akwai nau'in wanda ya ke fitowa a ƙasashen Turawa akwai kuma wanda a Afirka musamman ƙasar Hausa aka fi sani.
Ba a cin sa haka nan sai an ɗan turara shi ko an sa shi a cikin girki.
Ya na ɗauke da sinadarai irinsu protein mai gina jiki, da carbohydrates mai kara karfin jiki, da Fibre mai sarafa abinci, da calcium mai taimakawa karfin kashi, da iron da folate mai taimakawa jini, da kuma vitamin c da ke gina jiki.
- Ga abubuwan da ƙwararru suka ce Alayyahu na yi a jikin ɗan'adam:
- Ya na taimakawa lafiyar Ido
- Ya na ƙara kuzari
- Ya na taimakawa lafiyar zuciya
- Ya na taimakawa wajen yaƙi da Kansa
- Ya na kara karfin ƙashi
- Ya na taimakawa wajen rage ƙiba
- Ya na taimakawa lafiyar ƙwaƙwalwa
Ganyen Ugu

Ganyen Ugu shi ma kore ne, kuma yana fitowa ne a Najeriya da wasu sassa na yammacin Afirka. Ugu, kamar yada galibi aka san sa da shi, ana cin sa ne ta hanyar tafasa shi ko dafa shi a cikin abinci, ana kuma iya cin sa shi kaɗai ko a haɗa lemu da shi.
Ganye ne da ake iya samunsa a kowane yanayin lokaci na shekara.
Ganyen na ƙunshe da ɗauke da sinadarai irinsu calcium da iron da potassium da magnesium da vitamin C, A, B2, E da dai sauransu.
- Ga wasu daga cikin abubuwan da Ugu ke yi a jiki, in ji ƙwararru:
- Ya na taimakawa wajen samun haihuwa ga maza da mata
- Ya na taimakawa mata da suka haihuwa samun isashen ruwan nono
- Ya na inganta lafiya da aikin ƙwaƙwalwa
- Ya na hana tsufa da wuri
- Ya na ɗauke da sinadaran narkar da abinci da wuri da ke taimakawa masu ciwon ulcer da wahala wajen bahaya
- Ya na inganta ƙarfin ƙashi da hakori
- Ya na taimakawa ƙashin yara da iyaye mata
- Ya na ƙara jini a jiki
- Ya na taimakawa masu cutar sikari
Ganyen Shuwaka

Asalin hoton, Getty Images
Shuwaka ganye ne da ba kowa ke mayar da hankali a kan shi ba, ko ba shi wani muhimmanci, sai dai ƙwararru sun tabbatar da cewa yana ƙunshe da sinadaran da ke ƙara lafiya wanda a tsawon ɗaruruwan shekaru, al'adu da mutane a sassan duniya na amfani da shi.
Duk da cewa ba ƙasafai za ka ga mutane na sa shuwaka a girki ba, ko a rinka cinsa zalla, babu mamaki saboda ɗanɗanonsa na ɗaci-ɗaci idan ba a wanke shi da kyau ba.
Masu magungunan gargajiya sun san darajar shuwaka saboda ba ɓoyayye abu ba ne tsakaninsu, sannan ya na ɗauke da abubuwa da dama da ke taimaka jikin ɗan adam.
Shuwaka na ƙunshe da sinadarin vitamin A, B, C, B9, Calcium, Iron da dai sauransu.
- Ga abubuwan da shuwaka yake yi a jikin ɗan adam daga ƙwararru:
- Ya na ɗauke da ƙarfafawa garkuwan jiki
- Ya na ɗauke da sinadaran da ke kare sassan jiki daga lalacewa
- Ya na ba da kuzari da yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa
- Ya na inganta lafiyar hanta da hana lalacewarta
- Ya na daidaita sikari a jini
- Ya na kuma maganin Maleriya
- Ya na taikamawa narkewar abinci da wuri a jiki
- Ya na ƙara lafiyar ƙashi
- Ya na narka da kitse da daidaita ƙiba
- Ya na gyara fata
Ganyen Salak

Asalin hoton, Getty Images
Baya ga gyara kalar abinci da haɗin salak mai daɗi, ganyen salak na da dimbin alfannu ga lafiya. Wasu daga cikin abubuwan da ya ke yi ga lafiya sun haɗa da lafiyar zuciya da kuma sinadaran A da K masu inganta lafiya.
Salak ganye ne da kusan kowanne gida ba a ƙinsa. Mutane na cin sa sosai musamman a ƙasashen Afirka. Shi ma dai yana da nau'i daban-daban.
Ana amfani da shi a cikin haɗin salak a ci abinci da burodi da sauran abubuwan makulashe.
Cin salak sau ɗaya ko biyu a mako ya ishe jiki samun sinadaran da ya ke bukata.
- Ga wasu abubuwan da ganyen Salak ke yi a jikin ɗan adam;
- Ya na taimakawa wajen samun ruwa a jiki
- Ya na hana yunwa idan an ci sa da yawa
- Ya na dawo da wasu sinadari da ke karanci a jiki irinsu vitamin A
- Ya na taimakawa lafiya ido
- Ya na kara lafiyar zuciya
- Ya na sauke hawan jini
- Ya na inganta ƙwayoyin halitta
- Ya na ƙara garkuwar jiki da lafiyar hunhu da koda
- Ya na hana cushewar jini
- Ya na taimakawa wajen rage ƙiba da hana shanyewar ɓarin jiki











