Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya haura abin da ake ruwaitowa - Rahoto

Yadda masu alhini suka rungume gawar wani Bafalaɗinen da harin Isra'ila ya hallaka a Gaza, ranar 03 ga watan Janairun 2025

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda masu alhini suka rungume gawar wani Bafalaɗinen da harin Isra'ila ya hallaka a Gaza, ranar 03 ga watan Janairun 2025
    • Marubuci, Raffi Berg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Adadin waɗanda aka kashe a yankin Falasɗinawa a sanadiyar yaƙin Gaza zai iya haura alƙaluman da ma'aikatar lafiyar Hamas ke fitarwa a hukumance, kamar yadda wani bincike na cibiyar The Lancet medical journal ya nuna.

Binciken wanda cibiyar, wadda take Burtaniya ta yi, ta yi amfani da tattara bayanan watan tara na farko da fara yaƙin, wanda aka fara bayan Hamas ta kai hari a Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023 ne.

Ta yi amfani da alƙaluma daga ma'aikatar, da ƙididdigar bayanan waɗanda suka rasa ƴanuwansu.

Rahoton ya nuna cewa zuwa ranar 30 ga Yunin 2024, mutanen yankin Falasɗinawa 64,260 da suka rasu, sun haura waɗanda ma'aikatar lafiyar Hamas ke bayyanawa da kusan kashi 41.

Sai dai ofishin jakadancin Isra'ila da ke Burtaniya ya ce, "duk wani bayani da ya fito daga Gaza ba abin yarda ba ne," kuma yana goyon bayan Hamas ne.

Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce alƙaluman ma'aikatar lafiyar sahihai ne.

Alƙaluman ba sa bambanta tsakanin fararen hula da sojoji, amma a wani rahoto na kwanan nan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya ce yawancin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu a yaƙin a tsakanin wata shida, mata ne da ƙananan yara.

Isra'ila ta ce alƙaluman Hamas ba abin yarda ba ne. A watan Agusta, hedkwatar tsaron Isra'ila wato IDF, ta ce, "ta kashe ƴanta'adda sama da 17,000." amma babu tabbacin yadda ta tattara alƙaluman. IDF ɗin ta nanata cewa mayaƙa kawai take hara, kuma tana ƙoƙarin kaucewa kashe fararen hula.

Isra'ila ba ta bari ƴan jarida masu zaman kansu na ƙafafen watsa labarai na duniya, ciki har da BBC, su shiga domin tattaro bayanai daga Gaza, wanda hakan ya sa yake da wahala a tantance alƙaluman.

Sai dai cibiyar da ta yi wannan binciken, ta yi amfani da wani tsari ne da ake kira "capture-recapture", wanda tsari ne da aka yi amfani da shi wajen tattara bayanan waɗanda aka kashe a wasu rikice-rikicen daban.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu bincike daga kwalejin London School of Hygiene & Tropical Medicine sun bincika yadda mutane suka bayyana a wuraren duba waɗanda suka rasu.

Ma'aikatar lafiyar Gaza na fitar da bayanan waɗanda aka kashe ne a kullum, inda suke tattara bayanan waɗanda suka rasu a asibitoci da waɗanda iyalan mamatan suka bayyana, da kuma waɗanda kafafen watsa labarai amintattu suka ruwaito.

Rahoton na The Lancet ya yi nuna cewa waɗanda suka rasu sun kai tsakanin 55,298 zuwa 78,525, ba mutum 37,877 da ma'aikatar lafiya ta ruwaito ba.

Alƙaluman na nuna cewa waɗanda suka rasu za su iya haurawa ko ƙasa da wanda aka ruwaito, bisa la'akari da yanayin tsarin da aka bi na tattara alƙaluman.

Misali, gano waɗanda suka rasu a "sanadiyar mumunar raunuka" yana da wahalar gaske. Rashin tantance hakan zai iya shafar binciken.

Masu binciken sun ce kashi 59 da aka kashe mata ne da ƙananan yara da tsofaffi.

Yaƙin na Gaza ya fara ne tun bayan da Hamas ta kai hari a Isra'ila, inda ta kashe mutum 1,200, sannan ta yi garkuwa da mutum 151. Sai Isra'ila ta fara luguden wuta a matsayin martani a Gaza.

Ma'aikatar lafiyar ta ce mutum 46,000, mafi yawa fararen hula ne Isra'ila ta kashe.