Yaran Gaza da hare-haren Isra'ila suka jawo aka yanke wa gaɓoɓi
Yaran Gaza da hare-haren Isra'ila suka jawo aka yanke wa gaɓoɓi
Yara da dama a Zirin Gaza sun shiga tasku sakamakon hare-haren Isra'ila tun daga 7 ga watan Oktoban 2023, amma halin da Hanan da Misk suka shiga ya yi tsanani da yawa.
An yanke wa yaran ƙafafuwa sakamakon raunukan da hare-haren jirage marasa matuƙa da ake kaiwa kullum.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a watan Janairu da ya gabata, an samu rahoton cewa a kullum sai an yanke wa wani ko wata ƙafa ko hannu sakamakon rauni a Gaza.



