Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda hare-haren Isra'ila suka tagayyara Lebanon

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, By Ahmed Nour & Erwan Rivault
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Marubuci, BBC Arabic & BBC Visual Journalism
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
Tsananta luguden wuta da Isra'ila ta yi a Lebanon a mako biyu da suka gataba sun lalata gine-gine sama da waɗanda suka lallata a shekara ɗaya da aka yi ana gwabza yaƙin tsakaninta da Hezbollah, kamar yadda wasu hotuna da aka ɗauka da tauroron ɗan'adam da BBC ta gani suka bayyana.
Hotunan da BBC ta nazarta sama da 3,600 na gine-ginen ne aka lalata tsakanin 2 zuwa 14 ga Oktoban 2024 - wanda ya nuna kashi 54 na adadin gine-ginen da aka lalata tun bayan da yaƙin ya ɓarke a tsakanin Isra'ila da Hezbollah, kwana ɗaya bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban shekarar 2023.
Hotunan, waɗanda Corey Scher na Jami'ar City da ke Landan da Jamon Van Den Hoek na Jami'ar Jihar Oregun ne suka ɗauka.
Wim Zwijnenburg, wani masanin harkokin muhalli daga ƙungiyar wanzar da zaman lafiya ta Pax for Peace organisation ya nazarci hotunan, inda ya yi gargaɗin matsalolin da za su biyon tsanantar hare-haren.
"Hare-haren sojin Isra'ila na neman mayar da wasu yankuna 'tarkon mutuwa' a kudancin Lebanon kawai don tana so ta fatattaki Hezbollah da hana su sake taruwa," in ji shi.
Yaƙi ya fara ne tsakanin Isra'ila da Hezbollah bayan ƙungiyar ta Lebanon ta harba wasu rokoki zuwa arewacin Israila domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a ranar 8 ga watan Oktoba a ranar 2023, washegarin harin Hamas a kudancin Isra'ila.
Isra'ila ta kutsa kudancin Lebanon a ranar 30 ga Satumba domin ta fatattaki Hezbollah.
Hotunan da aka ɗauko da tauroron ɗan'adam da alƙaluman soji sun nuna cewa luguden wuta na Isra'ila a Lebanon ya fi ƙamari a kudancin ƙasar Lebanon, daga baya kuma hare-haren suka faɗaɗa zuwa arewacin ƙasar, ciki har da tsibirin Bekaa da wasu ƙauyukan kudancin Beirut.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce hare-haren sun cimma dubban yankunan Hezbollah, har a babban birnin ƙasar.

Yawancin hare-haren da aka yi a Beirut, Isra'ila na harin Dahieh ne, wani ƙauye a kudanci, inda dubban fararen hula suke rayuwa. Amma sojojin Isra'ila ta ce garin ne hedkwatar Hezbollah.
Hare-haren Isra'ila ne suka yi ajalin kwamandan Hezbollah, Hassan Nasrallahi a ranar 27 ga Oktoba.
Tankiya a tsakanin ƙasashen
Wasu hotuna daga cibiyar tattara bayanan rikicin soji ta ACLED, da BBC ta yi nazarinsu, sun nuna cewa aƙalla hare-hare 2,700 daga 1 ga Satumba zuwa 11 ga Oktoban 2024. Duk da cewa waɗannan hare-haren sun fi mayar da hankali ne a kan kudancin tsakanin ƙasashen, Isra'ila ta ƙara faɗaɗa hare-haren zuwa arewaci da tsakiyar ƙasar.
Ita kuma Hezbollah ta kai hare-hare guda 540 a Isra'ila a ɗan tsakanin, kamar yadda ACLED ta bayyana. Hare-haren Hezbollah sun ƙunshi rokoki da makamai masu linzami da jirage maras matuƙa.

Rundunar tsaron Isra'ila ta ce hare-haren sama na Isra'ila a Lebanon suna neman kadarorin Hezbollah ne.
Tana bayyana cewa tana so ne ta dawo da dubban ƴan Isra'ila zuwa gidajensu bayan hare-haren ƙungiyar sun raba su da muhallansu.
An kwashe kusan mutum 60,000 ne daga arewacin Isra'ila saboda hare-haren na Hezbollah, amma wasu rokokin sun isa kudanci, sun kuma lalata wasu gidaje a birnin Haifa.
A gefen Lebanon, hare-haren Isra'ila sun fi ƙamari ne a biranen Tyre da tsibirin Bekaa da babban birnin Beirut, kamar yadda BBC ta gano a hotunan da ta nazarta daga hotunan na ACLED.
Gwamnatin Lebanon ta ce kusan mutum miliyan 1.3 suka rabu da muhallansu, sannan firaiministan ƙasar, Najib Mikati ya yi gargaɗin "yiwuwar raba mutanen da muhallansu mafi muni," a tarihin ƙasar.
IDF ta sha nanata gargaɗinta ga mutane a kan su bar yankunan da take kai hare-haren, ciki har da Beirut.
A kudanci, sojojin ƙasan sun umarci ƴan ƙauyuka da dama da su bar gidajenu, su koma arewa da tekun Awali, wanda yake da nisan kilomita 50 (mil 30) zuwa iyakar shiga Isra'ila.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Wannan wani bala'i ne babba," in ji Gabriel Karlsson, manajan ƙungiyar agaji ta Red Cross a Gabas ta Tsakiya a zantawarsa da BBC.
Ya ce akwai ƙarancin matsugunai ga waɗanda aka raba da muhallansu.
"Na ga ƙananan yara suna kwana a titi," in ji Karlsson, sannan ya yi kira ga ƙungiyoyin agaji da su kawo ɗauki domin magance matsalar.
Hukumomi a ƙasar Lebanon sun ce aƙalla mutum 2,350 aka kashe, sannan sama da mutum 10,000 ne suka jikkata a hare-haren Isra'ila a Lebanon. Ministan lafiyan Lebanon ya ce da yawa daga cikin waɗanda aka kashe fararen hula ne.
Amos Yadlin, tsohon shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar sojin Isra'ila ya shaida wa BBC cewa yaƙin laifin Hezbollah ne, sannan ya ce kutsawar dakarun Isra'ila ta ƙasa za ta tursasa ƴan ƙungiyar su bar iyakar ƙasar.
Zwijnenburg daga ƙungiyar Pax for Peace ya yi gargaɗi a game da hare-haren sojojin Isra'ila a wuraren da fararen hula suka yi yawa.
"Hare-haren na sanadiyar mutuwar fararen hula. Sannan hotunan da aka ɗauka da tauraron ɗan'adam sun nuna yadda hare-haren suka shafi kadarorin fararen hula irin su tashashin gas da manyan layukan lantarki da sauran abubuwa."
Da ƙarin rahoto daga Paul Cusiac da Maria Rashed











