Gabas ta Tsakiya na cikin haɗarin damewa da yaƙi - MDD

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yankin Gabas ta Tsakiya na cikin hadarin fadawa rikicin da zai iya durkusar da yankin.
Babbar jami’ar harkokin siyasa ta Majalisar, Rosemary DiCarlo ta bayyana haka ne a yayin taron kwamitin tsaro na majalisar, bayan hare-haren wannan mako da aka kai kan na’urorin sadarwa da wayoyin oba-oba da Hezbollah ke amfani da su, wadanda suka rika fashewa, inda suka hallaka akalla mutum 37 da raunata wajen 3000.
Yayin da kwamitin majalisar ke taron wani hari da Isra’ilar ta kai Beirut, ta kashe wani babban kwamandan Hezbollah.
Kwamitin tsaron Majalisar dinkin Duniyar na tattauna halin da ake ciki ne dangane da hadarin fadawar yankin na Gabas ta Tsakiya cikin kazamin rikici bayan miyagun hare-haren Isra’ila tsawon kwana hudu a kan Hezbollah.
Musamman ma dai hare-haren ranar Talata ta Laraba inda kananan na’urorin sadarwa da wayoyin oba-oba da Hezbollah ke amfani da su, suka rika fashewa a hannun jama’a, lamarin da Lebanon ta ce ya hallaka akalla mutum 37 tare da jikata dubbai.
Isra’ila dai ba ta fito fili ta dauki alhakin kai wadannan hare-haren ba, illa dai ministanta na tsaro Yoav Gallant da ya fito ya ce, Isra’ilar ta bude sabon babi a yakin, inda za ta karkata ga kai hare-hare kudancin Lebanon.
Babban jami’in majalisar kan kare ‘yancin dan’Adam Volker Turk, ya ce hare-haren na na’urori ka iya zama miyagun laifukan yaki.
Mataimakiyar babban sakataren majalisar a kan harkokin siyasa Rosemary Dicarlo ta sheda wa kwamitin tsaro na majalisar cewa ci gaba da wadannan hare-hare ta iya sa a ga halin da yankin yake ciki ya zama kamar ba a ma ga komai ba.
Jami’ar ta ce har yanzu ba a makamara ba a diflomasiyya.
A hare-haren Isra’ilar na baya-bayan nan a jiya Juma’a ta ce ta kashe kwamandojin Hezbollah goma a wani harin sama da ta kai Beirut.
Daga cikin manyan kwamandojin akwai, fitacce Ibrahim Aqil, wanda Amurka ta taba sanya tukuicin dala miliyan bakwai a kansa, bisa zarginsa da kitsa hare-hare biyu a Beirut a 1983.
Harin bama-bamai da aka kai da wata babbar mota da ya kashe sama da mutum 300 a ofishin jakadancin Amurkar da kuma wani harin a wani barikin zaratan sojojin Amurka duka a babban birnin Lebanon din.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jami’an Lebanon sun ce akalla mutum 14 ne suka mutu gommai suka ji rauni a harin da Isra’ila ta kai a wani yanki mai yawan jama’a na Dahie, wanda ‘yan Hezbollah ke da karfi
Harin na ranar Juma’a shi ne na farko da aka kai wa Beirut tun bayan watan Yuli, lokacin da Isra’ila ta kai harin da ya kashe jagoron sojin kungiyar Fuad Shukr.
Da yake jawabi a yayin taron na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ministan harkokin wajen Lebanon Abdallah Bou Habib ya yi Allah-wadari da hare-haren na Isra’ila, wadanda ya ce suna kafar ungulu ga duk wani yunkuri na kawo karshen rikicin.
Ya ce, wadannan hare-hare miyagun abubuwa ne da ba a taba gani ba a tarihin yake-yake, kuma sun zo ne bayan da Israila ta ayyana cikakken yaki a kan Lebanon inda ta mayar da Lebanon zuwa zamanin da na jahiliyya.’’
A martaninsa jakadan Isra’ila a majalisar ta dinkin duniya, Danny Dannon ya ce Isra’ila za ta ci gaba da yin duk wani abu da ta ga ya zama dole domin kare kanta.
Ya ce, duk da cewa Israi’a ba wai tana neman fadada yakin ba ne. To amma ba za ta zauna ta bar Hezbollah ta ci gaba da tsokana ba. Ya kara da cewa ayyukanta sun saba wa dokokin duniya kuma Isra’ila za ta kare kanta.










