Hare-haren na'ura kan Hezbollah: Tambayoyin da har yanzu babu amsarsu

Wani hoto da aka ɗauka ranar Laraba ya nuna wata na'urar sadarwa ta pager ta fashe a kudancin birnin Beirut na Lebanon

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani hoto da aka ɗauka ranar Laraba ya nuna wata na'urar sadarwa ta pager ta fashe a kudancin birnin Beirut na Lebanon
    • Marubuci, Tom Bennett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, London
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan dubban na'urorin sadarwa na oba-oba da kuma pager sun farfashe a Lebanon har karo biyu - waɗanda suka raunata dubbai tare a kashe aƙalla mutum 37 - har yanzu akwai bayanan da ba su fito ba game da yadda aka hare-haren.

Lebanon da ƙungiyar Hezbollah, wadda mambobinta da na'urorinta aka kai wa hare-haren, sun zargi Isra'ila da kai su - kodayake zuwa yanzu Isra'ilar ba ta tabbatar ko musanta kai harin ba.

BBC ta bi diddigin abin da ya faru zuwa Taiwan, da Japan, da Hungary, da Isra'ila, da kuma Lebanon ɗin kanta.

Ga tambayoyin da har yanzu babu amsarsu.

Ta yaya aka ɓata na'urorin na pager?

Jita-jita na farko-farko sun nuna cewa kutsen da aka yi wa na'urorin ne daga nesa (ta intanet) suka haddasa farfashewarsu. Sai dai nan take masana suka yi watsi da wannan tunanin.

Idan ana son a kai hari kamar wanda aka kai, akwai yiwuwar an zuba abubuwan fashewa a cikinsu ne kafin a kai su Lebanon, in ji ƙwararru.

Hotunan da aka ɗauka na na'urorin da suka fashe na ɗauke da bajon wani ƙaramin kamfani na ƙasar Taiwan mai suna Gold Apollo.

Wanda ya kafa kamfanin, Hsu Ching-Kuang, ya ce sun daina ƙera na'urorin.

"Idan kuka duba hotunan, babu inda aka ce an ƙera su ne a Taiwan, ba mu muka ƙera pager ɗin ba," a cewarsa.

A madadin haka - sai ya zargi wani kamfani mai BAC Consulting na ƙasar Hungary.

Mr Hsu ya ce ya shekara uku da suka gabata ne ya sakar wa BC damar yin amfani da sunan kamfanin nasa a kan na'urorin pager da shi yake ƙerawa.

Ya ce kuɗin da ya kamata kamfanin ya biya shi sun zo "ta wata irin hanya" - kuma ma an yi ta samun matsala da shigowar kuɗin da aka tura masa daga Gabas ta Tsakiya - duk da cewa Hungary ƙasar Turai ce.

Me ya haɗa kamfanin Hungary da wannan aiki?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta kai ziyara ofishin BAC Consulting da ke rukunin gidaje a Budapest babban birnin Hungary.

Adireshin ya nuna cewa akwai wasu kamfanoni 12 da ke wurin tare da shi - kuma babu wanda ya iya faɗa mana wani abu game da BAC Consulting kwatakwata.

Jami'ai a Hungary sun ce kamfanin, wanda aka fara yi wa rajista a 2022, "dillali ne kawai da ba shi da wata ma'aikata ko ofis" a ƙasar.

Shafin BAC na intanet ya bayyana wata mace a matsayin jagora kuma wadda ta kafa shi - Cristiana Bársony-Arcidiacono.

BBC ta yi yunƙuri daban-daban domin tuntuɓar ta amma mun kasa samun ta.

Sai dai kuma rahotonni sun ce ta yi magana da kafar yaɗa labarai ta NBC tana cewa: "Ba ni ke ƙera pager ɗin ba. Ni dillaliya ce kawai."

Saboda haka wane ne takamaimai ya mallaki BAC Consulting?

Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa hasali ma kamfanin dillalin hukumar leƙen asiri ne ta Isra'ila.

Jaridar da ta ambato majiyoyi daga jami'an Isra'ila, ta ce an kafa wasu kamfanonin dillanci biyu domin ɓoye ainahin mutanen da ke ƙera na'urorin: su ne jami'an leƙen asiri na Isra'ila.

BBC ba ta iya tantance sahihancin waɗannan rahotonni ba da kanta - amma dai mun san cewa hukumomi a ƙasar Bulgaria sun ce sun fara bincike kan wani kamfani da ke da alaƙa da BAC.

Kafar yaɗa labaran Bulgaria mai suna bTV ta ruwaito ranar Alhamis cewa kuɗin da suka kai yuro miliyan 1.6 da ke da alaƙa da cinikin na'urorin sun gilma ta ƙasar kafin daga baya a tura su Hungary.

Ta yaya aka ɓata na'urorin oba-oba?

Ba a gama gane tushen wayoyin oba-oba da suka farfashe ba har yanzu.

Amma mun sani cewa aƙalla wasu daga cikinsu samfurin IC-V82 ne da kamfanin ICOM ke ƙerawa a Japan.

Hezbollah ta saye su ne wata biyar da ska wuce, a cewar wata majiyar tsaro da ta yi magana da kamfanin labarai na Reuters.

Tun da farko wani wakilin kamfanin a Amurka ya faɗa wa kafar labarai ta CBS cewa da alama jabun na'urorin ne suka fashe a Lebanon - yana cewa abu ne mai sauƙi a samu jabunsu a intanet.

Jim kaɗan bayan haka BBC ta gano wasu na'urorin na Icom IC-V82 a kasuwar intanet.

ICOM ya ce ya daina ƙera wanann samfurin kusan shekara 10 da suka wuce, a watan Oktoban 2014 - kuma ya daina ƙera batirin da ke cikinsu.

Ta yaya aka dinga tashin na'urorin?

Hotunan bidiyo sun nuna mutane na saka hannu a aljihu 'yan daƙiƙoƙi kafin na'urar ta fashe, abin da ya jawo hautsini da zullumi a tituna, da shaguna, da gidaje a ƙasar.

Hukumomin Lebanon sun ce an tashi na'urorin ne ta hanyar aika musu "saƙonni na latironi", kamar yadda wata wasiƙa da tawagar wakilan ƙasar a Majalisar Ɗinkin Duniya ta aika wadda kum Reuters ya gani.

Me ya sa aka kai hare-haren a yanzu?

Akwai shaci-faɗi da dama game dalilin da ya sa aka kai hare-haren a makon nan.

Ɗaya daga ciki shi ne, Isra'ila ta zaɓi ta aika wa Hezbollah mummunan saƙo bayan shafe kusan shekara suna harba mata makamai daga kan iyaka tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Ɗayan kuma shi ne cewa Isra'ilar ba ta so kai harin yanzu ba, amma an tilasta mata yin hakan ne saboda tsoron ƙungiyar ta gano shirin da ake yi.

A cewar kafar Axios ta Amurka, ainahin shirin shi ne ya zama wani mafarin babban farmaki da zai kai ga cikakken yaƙi da zimmar karya lagon Hezbollah.

Amma ta ce bayan Isra'ila ta gano ana neman bankaɗo manaƙisar tata sai ta kai harin a yanzu.