Isra'ila ta tsugunar da mutum 60,000 a arewacin ƙasar saboda hare-haren Hezbollah

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Jaroslav Lukiv
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 2
Isra'ila ta samu damar kwashe ƴan ƙasar daga kudanci zuwa arewacin ƙasar wani buri da Isra'ilar take son cimma, kamar yadda ofishin firaiminista Netanyahu ya ce.
A ranar Litinin ne dai firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu bisa shawarar Majalisar Yaƙin ƙasar suka yanke yin hakan.
Kimanin ƴan Isra'ila 60,000 aka kwashe zuwa arewacin saboda irin hare-haren da ƙungiyar Hezbollah mai goyon bayan Iran ke kaiwa kusan kullum.
Rikicin kan iyaka tsakanin Hezbollah da Isra'ila dai ya fara ne a ranar 8 ga watan Oktoban 2023 kwana ɗaya bayan harin da Hamas ta kai a Isra'ila, inda Hezbollah ta harba rokoki a wani abu mai kama da nuna goyon baya ga Hamas.
Ƙudirorin Isra'ila na yaƙi guda huɗu
"Majalisar Yaƙi ta sabunta ƙudurorinta na yaƙi da suka haɗa da mayar da ƴan yankin arewacin ƙasar gidajensu," in ji wata sanarwa da ofishin firaiminista.
"Isra'ila za ta ci gaba da zartar da ƙudirorin nata," kamar yadda sanarwar ta ƙara.
A ranar Litinin, ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce hanya ɗaya kawai da za a mayar da mazaunan arewaci gidajensu ita ce ta "hanyar ƙarfin soji" a yayin wani taro da suka yi da jakadan Amurka na musamman Amos Hochstein.
“Lokaci na ƙurewa dangane da neman cimma yarjejeniya saboda Hezbollah ta "haɗe" da Hamas ta ƙi yarda a ƙare wannan rikici," in ji sanarwar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A saboda haka, hanya ɗaya ta tabbatar da Isra'ila ta mayar da al'ummar arewacin ƙasar zai zama ta hanyar ƙarfin soji."
Kalaman Yoav Gallant dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yaɗa cewa firaiminista Netanyahu zai maye gurbinsa bisa saɓani da ke tsakanin mutanen biyu kan yaƙin Gaza.
Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin ya yi gargaɗi dangane da illar da ke tattare da ta'zzarar rikicin.
Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron Amurka, ta ce " ta tabbatar da wajibicin cimma tsagaita wuta da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma cewa ya kamata Isra'ila ta bayar da damar tattaunawar jakadanci ta yi aiki, bisa la'akari da irin munin da sakamakon rikicin zai yi a kan al'ummar Isra'ila da Hezbollah da kuma yankin gabas ta tsakiya".
Isra'ila ta sha nanata gargaɗin cewa za ta iya amfani da ƙarfin soji wajen korar Hezbollah daga kan iyakar.
Hezbollah dai ƙungiyar Musulmi ce mabiya mazhabar Shi'a wadda da ke da ƙarfin iko kuma ƙungiya mafi ƙarfi da yawan makamai da ke Lebanon.
Har kawo yanzu dai ƙungiyar ba ta ce uffan dangane da batun ba.
Shirin Isra'ila na baya-bayan nan ya sa ƙasar ta ƙara faɗaɗa tsoffin burinta na yaƙi kamar haka:
- Kawo ƙarshen Hamas da ƙarfin sojinta.
- Mayar da dukkannin waɗanda aka yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.
- Tabbatar da cewa zirin Gaza bai ci gaba da zama barazana ga Isra'ila ba
- Har yanzu ƙungiyar ba ta ce komai a game da lamarin.
Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da yaƙi domin kawar da Hamas da sunan martani ga harin da ƙungiyar ta kai mata irinsa na farko wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,200 sannan aka yi garkuwa da 251 zuwa Gaza.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,220 a Gaza tun fara daga lokacin kawo yanzu kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce.










