Ana dab da cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce masu shiga tsakani a yarjejeniyar sun bayyana cewa na basu wani sabon kundin yarjejeniya a ranar Litinin sannan kuma zasu sake ganawa a yau Talata don ganin sun kammala abin da ya dace.
Cikin kundin yarjejeniyar bayanai sun ce Isra'ila ta amince da sakin dubban Falasdinawan da ta ke rike da su inda za ayi musayarsu da Isra'ilawa 34 da Hamas ke rike da su.
Shugaba Biden ya ce ya jima yana waya da manyan jagororin da ke kan gaba wajen cimma wannan yarjejeniya.
Ya ce a yanzu an kusa cimma yarjejeniyar.
Ya ce cikin shekaru da dama a yanzu ya koyi wani darasi wato kada ka taba fitar ran samun wani abu da kake nema d asannu a hankali zaka samu.
Shugaba Biden ne ya tsara yadda yarjejeniyar zata kasance tun watanni takwas da suka wuce abin da ya janyo yarjejeniyar ta rika fuskantar matsaloli da dama inda bangarorin da ke fada da juna wato Isra'ila da Hamas suka rika dora alhakin kin amincewa da bukatun juna lamarin daya rika tsananta yakin da suke.
Yanzu haka dai wakilan Mr Biden da na Donald Trump na Doha inda kowanne daga cikinsu ke kokarin nuna cewa shi ne ya taka rawar da har aka kai matakin da ake a yanzu.
Sai dai kuma zancen gaskiya shi ne rantsuwar da Trump zai sha nan da wasu kwanaki ita ce ta kara matsa lamba har aka kawo ga matakin.
Jami'na Palastine sun shaida wa BBC cewa, Hamas da jami'na Isra'ila sun yi tattaunawa ta bayan fage a wani gini tare a ranar Litinin inda suka tattauna wasu muhimman batutuwa da ke cikin kunshin yarjejeniyar.
Dukkan bangarorin sun amince su sake mutum uku da suke rike da su a ranar farko da yarjejeniyar zata fara aiki, daga nan kuma sai Isra'ila ta fara janye dakarunta daga Gaza.
Bayan mako guda kuma sai Hamas ta saki karin wasu mutum hudu da ta ke rike da sui ta kuma Isra'ila sai ta bawa mutanen da suka rasa muhallansu a kudancin Gaza komawa arewaci amma da kafa.
Haka za a ci gaba da da aiwatar da abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa daki-daki.











