Yadda shugaban Hukumar lafiya ta duniya ya tsallake rijiya da baya a harin Isra'ila

Bayanan bidiyo, Yadda aka shiga ruɗani a filin jirgin sama na Sanaa
    • Marubuci, Lana Lam
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da wasu ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya na a babban filin jirgin sama na Sanaa a ranar Alhamis, sa'ilin da Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a cikin ƙasar, lamarin da rahotanni ke cewa ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla shida.

Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da suke gab da shiga jirgi.

Kamfanin dillancin labarai na Saba, wanda ke ƙarƙashin ƴan Houthi, ya bayyana cewa mutum uku ne suka mutu a filin jirgin yayin da guda 30 suka samu rauni.

Ya kuma bayyana cewa an kashe wasu mutanen uku tare da raunata 10 a lardin Hodeida da ke yammacin ƙasar.

Mayaƙan Houthi, waɗanda Iran ke mara wa baya sun bayyana hare-haren - wadanda suka faɗa kan cibiyoyin samar da lantarki na tashoshin - a matsayin "dabbanci".

Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan "cibiyoyin soji bayan samun bayanan sirri".

Tedros Adhanom Ghebreyesus at opening ceremony of WHO academy in Lyon, France - 17 December

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dr Tedros ya ce babu abin da ya same sanadiyyar hare-haren

Babu tabbas kan ko waɗanda aka kashen fararen hula ne da ba su ji ba, ba su gani ba ko kuma mayaƙan Houthi ne.

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Dr Tedros ya ce ya je Yemen ne "domin tattauna yadda za a sako ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ake tsare da su da kuma duba yanayin wahalar da al'umma ke ciki" a ƙasar.

Sai dai bai yi wani ƙarin bayani ba baya ga hakan.

Kan batun hare-haren da Isra'ilar ta kai a filin jirgin saman na Sanaa, ya ce: "An lalata hasumiyyar aikawa da karɓar bayanan zirga-zirgar jirage, da ɗakin jira na fasinjoji - waɗanda ba su da nisa daga inda muke - har ma da titin tashin jirage.

"Dole sai mun jira an gyara ɓarnar da aka yi kafin mu bar ƙasar," in ji Tedros.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana hare-haren a matsayin "abin damuwa ƙwarai."

"Ina takaicin sake ɓarkewar rikici tsakanin Yemen da Isra'ila, kuma na damu ƙwarai da hatsarin ci gaba da tashin hankalin da ake samu a yankin." Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na X.