Yadda ƙananan halittun al'aurarki za su inganta lafiyar jikinki

Appareil génital féminin en fleurs.

Asalin hoton, Prashanti Aswani

    • Marubuci, Jasmin Fox-Skelly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ba a cika mayar da hankali kan rawar da ƙananan ƙwayoyin halittun da ke rayuwa a cikin al'aurar mace ke takawa ba kan inganta lafiya ɗaukacin jiki.

A cikin al'aurar mace akwai ƙananan ƙwayoyin halitta waɗanda ke rayuwa a cikin yanayi mai ban-mamaki.

Wuri ne da ke ƙunshe da dubban nau'ukan ƙwayoyin halittun bakteriya da fungi da virus waɗanda ke gogayya da juna domin samun wuri da yanayin zama mafi kyawu.

Wasu daga cikin waɗannan ƙananan halittu na taka muhimmiyar rawa wajen lafiyar ɗaukacin jiki – kamar hana kamuwa da cutuka da bunƙasa samun juna biyu.

Idan aka samu yawaitar halittun Lactocillus a cikin al'aurar mace, hakan na rage hatsarin rashin samun haihuwa da ɓarewar ciki, haihuwar bakwaini da kuma rage hatsarin kamuwa da kansar bakin mahaifa.

To amma ta yaya wadannan ƙananan halittu ke iya tantance lafiyar mace?

Ƙwayar halittar Lactobacilli na da matuƙar amfani ga lafiya. Idan aka samu yawaitar waɗannan nau'in halitta a cikin al'aura, sukan kare mace daga kamuwa da cutukan hanyar mafitsara ta hanyar hana ƙwayoyin cuta samun wurin zama.

"Sukan tare ko'ina sannan su hana ƙwayoyin da ke haifar da cuta samun wurin zama da abinci." In ji Chrysi Sergaki, shugaban sashen ilimin ƙananan halittu a hukumar kula da magunguna da kiwon lafiya ta Birtaniya (MHRA).

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Halittun lactobacilli na kuma samar da wasu sinadarai waɗanda ke hana ƙwayoyin halittun da ke haifar da cuta zama a cikin al'aura.

"Wannan kan sanya ƙwayoyin cuta su gaza zama a cikin farji," in ji Sergaki.

A ɓangare ɗaya, idan halittun da ke cikin al'aura suka fi yawa, sai su kori halittun Lactobacilli, hakan ne yake sanyawa ƙwayoyin cuta da ke addabar al'aura ko hanyoyin fitsari su samu damar taruwa.

Haka nan irin wannan yanayi kann saka mata cikin hatsarin kamuwa da cutakan da ake kamuwa da su a lokacin saduwa.

Misali, matan da ba su da isassun halittun Lactobacillus a cikin al'aura sun fi shiga cikin háɗarin kamauwa da cutar HIV.

"A birnin Cape Town na ƙasar Afirka ta Kudu, hatsarin kamuwa da cutar HIV ya kai kimanin kashi 20% zuwa 30%, amma duk da haka wasu mata masu zaman kansu kan ci sa'ar rashin kamuwa da cutar," in ji Laura Goodfellow, babbar malama a sashen lafiyar mata da yara a jami'ar Liverpool da ke Birtaniya.

"An gano cewa yiwuwar kamuwa da cutar HIV a ƙasashen Afirka, musamman tsakanin mutane masu zaman kansu, ya danganta ne da ƙananan halittu da sinadaran da ke cikin al'aura. Saboda haka idan mace ba ta da isassun ƙwayoyin halittun Lactobacillus a cikin al'aura, to ta fi kasancewa cikin hatsarin kamuwa da cutar HIV."

Haka nan mata da ke da ƙarancin ƙwayoyin Lactobacillus a cikin al'aura sun fi hatsarin kamuwa da cutar papilomavirus (HPV).

Samun ciki

Ƙwayoyin bakteriya da ke zaune a al'aurar mace na taka muhimmiyar rawa wajen tantance damar da take da ita ta ɗaukar juna-biyu da kuma ko za ta iya riƙe ciki har zuwa lokacin haihuwa.

Matan da ba su da isassun halittun Lactobacillus, sun fi kasancewa cikin hatsarin yinɓarin ciki ko kuma ɗaukar ciki a wajen mahaifa.

Haka nan irin waɗannan mata sun fi shiga cikin hatsarin haihuwar bakwaini – wato jariran da ake haihuwa kafin su cika sati 37.

La présence de Lactobacillus crispatus dans le microbiome vaginal est associée à un risque plus faible d'accouchement prématuré.

Asalin hoton, Prashanti Aswani

"Wannan ba shi ne kaɗai abin da ke haifar da haihuwar bakwaini ba, domin akwai mutanen da ba su da isassun irin waɗannan ƙwayoyin halitta a cikin al'aura amma duk da haka sukan ɗauki ciki su haihu a lokacin da ya dace, amma dai muna ganin cewa rashin isassun wadannan ƙananan halittu na ƙara hatsarin (zubewar ciki)," in ji Goodfellow.

Akwai kuma wata ƙwayar halitta mai amfani da ke zama cikin al'aura wadda ake kira Bifidobacterium, na tabbatar cewa tana kare mata daga yin ɓari – sai dai ita irin wannan ƙwayar halitta na zama ne a ƙalilan daga cikin mata, ƙasa da kashi 5%.

Wasu bincike-bincike da aka gudanar sun kuma alaƙanta rashin isassun halittun al'aura da hana yin nasarar maganin samun ciki. "Idan mace na da ƙarancin halittun al'aura masu amfani, kuma sai aka yi mata dashen ɗan tayi (IVF), muna ganin cewa akwai yiwuwar ba za a yi nasara ba," in ji Goodfellow.

Yadda za ki kare halittun al'aurarki

Boire beaucoup d’eau, utiliser des préservatifs et bien dormir peuvent tous contribuer à maintenir un microbiome vaginal sain.

Asalin hoton, Prashanti Aswani

Idan ana magana kan yadda za a kare halittun da ke cikin al'aura, akwai abubuwan da suka kamata a yi da kuma wadanda suka kamata a guje mawa.

Bai kamata a wanke al'aura da sinarai ba. Wannan shi ne yadda ake amfani da ruwa ko wasu sinadarai wajen wanke cikin al'aura.

A maimakon bunƙasa lafiyar al'aura, ana alaƙanta wannan da ƙaruwar halittu masu haifar da cuta, da haihuwar bakwaini da kuma ciwon mara, wanda zai iya haifar da rashin haihuwa.

Haka nan ma amfani da mayukan mata ko turaren fesawa na al'aura duk sukan iya lalata halittu masu amfani da ke zama a cikin al'aura.

Ga mata waɗanda ke saduwa da maza, yin amfani da abin kariya na taimakawa.

Misali, bincike ya nuna cewa masu yin amfani da kwaroron roba na da isassun halittar Lactobacillus a cikin al.'aurarsu.

Haka nan yana da kyau mace ta riƙa lura da abin da take ci. Bincike ya nuna cewa matan da ba su cin abinci mai yawan sinadaran gina jiki na vitamin A, da C da D da E, da sauran su na cikin hatsarin samun ƙarancin halittu masu amfani a cikin al'aura.

Haka nan wani binciken ya nuna cewa mata da ke da ƙiba fiye da kima na iya fama da ƙarancin halittu masu amfani a cikin al'aura, saboda haka zai fi kyau a duba abin da ake ci.

A ƙarshe, bincike ya nuna cewa shan taba na iya haifar da ƙarancin halittu masu amfani a al'aura. Wani bincike, inda aka ɗauki samfurin al'aurar mata 20, masu shan taba da waɗanda ba su shan taba, ya nuna cewa rabin matan da ke shan taba suna fama da ƙarancin halittun Lactobacillus.

Amma kashi 15% ne kacal na mata marasa shan taba ke fama da hakan.

Saboda haka a taƙaice, daina shan taba, daidaita ƙibar jiki da cin abinci mai yawan sinadaran gina jiki da kuma daina wanke farji da sinadarai su ne manyan hanyoyin tabbatar da lafiyar al'aurar mace.