Ko akwai alaƙa tsakanin rigar-mama da kansar nono?

Rigar mama mai launin ja

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Mata na yawan taraddadi game da tasirin rigar mama ga lafiyarsu. Akwai maganganu da shaci-faɗi da dama game da hakan.

Rigar mama na taimaka wa mata sosai a fannin sutura da kuma ado.

Daga lokacin da ƴanmata suka shiga sakandare zuwa jami'a, har zuwa lokacin da suka fara aiki ko kuma suka yi aure, sukan yi amfani da rigar mama sosai.

To sai dai mata da dama na da shakku game da amfani da ita.

A kowace shekara, 13 ga watan Oktoba ce 'ranar zama babu rigar mama'. Rana ce da aka ware domin wayar da kai game da cutar kansa tare da ƙarfafa wa mata gwiwa su riƙa bincika lafiyar nononsu.

A irin wannan rana mata ba sa saka rigar mama, kuma akan yi gangami a wurare daban-daban domin faɗakar da jama'a kan lafiyar mama.

Amma babu wani bincike da ya tabbatar da cewa rigar mama na haifar da kansar nono. Duk da cewa a baya-bayan nan, ba ana ɗaukar 'ranar zama babu rigar mama' a matsayin ta fadakarwa kan ciwon kansa ba ne kawai, ranar ta zamo ta ƙoƙarin nuna daidaiton jinsi.

Amma akwai matan da ba su sanya rigar mama, kawai saboda ba sa jin daɗin saka ta.

Yayin da kowa ke da nasa dalilin na sanyawa ko kuma ƙin sanya rigar mama, akwai wata babbar tambaya guda ɗaya.

Idan kika daɗe ba ki saka rigar mama ba, ko hakan zai shafi surar jikinki, kuma ko hakan zai iya haifar da zubewar nonuwa?

Me likitoci suka ce a kan hakan?

'Yana da kyau ki fahimci jikinki'

"Domin kauce wa ruɗani, abu na farko shi ne mu fahimci jikinmu. Ya kamata mata su fahimci ɗabi'ar jinin al'adarsu ta wata-wata," in ji likitar mata Balkumari.

"Nonon mace ya ƙunshi kitse ne da wasu masana'antar sinadaran jiki da ke ƙunshe da sinadaran da ke samar da ruwan nono. Kamar yadda muke da abubuwan da ke samar da yawu a baki, haka ake da abubuwan da ke samar da ruwan mama a cikin nono.

"Wasu matan suna da kafofin samar da ruwan nono fiye da kitse a mamansu. Wasu kuma suna da kitse mai yawa fiye da wuraren samar da ruwan nono. Ya danganta ne ga tsarin jikin mace."

Waɗannan abubuwa da ke samar da ruwan nono sukan tsuke yayin da mace ke ƙara yawan shekaru. Hakan na nufin nonon mace zai riƙa zubewa yayin da take ƙara tsufa, haka aka halicci mutane.

"Saboda haka nononki ba zai zube ba haka kawai saboda kin ƙi saka rigara mama," in ji Balkumari.

Shin sanya rigar mama na haifar da kansar nono?

"Haka nan ba gaskiya ba ne cewa sanya matsattsiyar rigar mama zai haifar da kansar nono. Idan mace ta sa matsattsar rigar mama, hakan na yin illa ga jiki. Saboda zufa za ta iya sa fata ta goge.

"Sanya matsattsiyar rigar mama zai sa a riƙa jin zafi a wuraren da rigar ta ɗame jiki. Saboda haka ya kamata mata su zaɓi rigar mama mai girma daidai-wa-daida. Kuma kada su yi fargabar cewa za ta haifar musu da ciwon kansa," in ji likitar.

"Fitar ruwan nono haka kawai abu ne da yakan faru da mata masu girman nono. Kuma za su iya samun ciwon baya. Saboda haka sanya rigar mama za ta taimaka wajen alkinta nonon.

"Hakan zai iya kare kamuwa da ciwon baya. To amma mu sani cewa ita rigar mama tana taimakawa ne na wani dan lokaci. Idan kika ji kina jin zafi a lokacin da kika sa rigar mama, to ki daina sawa."

"Saboda haka rigar mama ba ta da wani tasiri kan ingancin nono. Babu amfani kuma babu cutarwa," in ji dakta Balkumari.

Dr. Kavya Krishnan

Asalin hoton, Dr. Kavya Krishnan

Bayanan hoto, Dakta Kavya Krishnan
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Da farko, ya kamata mu fahimci cewa zubewar nono halitta ce. Musamman maza, ya kamata su san haka.

"Hasashe-hasashen da maza ke yi game da yadda jikin mace ya kamata ya kasance na haifar wa mata damuwa a ƙwaƙwalwa," in ji Dakta Kavya Krishnan.

Ta ƙara da cewa "Yanzu za ka ga ana sayar da wasu mayukan hana zubewar nono a shafukan intanet, ko kuma na ɗaga su. Babu binciken lafiya da ya tabbatar da sahihancinsu. Kada irin tallace-tallacen da ake yi su ruɗe ku. Ya kamata mutane su rungume sauye-sauyen da ke faruwa a jikkunansu, saboda halitta ce."

"Kamar yadda tsufa da zubewar mama ke tafiya tare, masu shayarwa ma na fuskantar zubewar mama. Yana faruwa ga dukkanin mata a ko ina a duniya, babu wadda ba ta fuskantar hakan, saboda haka bai kamata ki damu kanki ba.

"Haka nan akwai shaci-fadin cewa shayarwa na haifar da zubewar mama, ya kamata mu san cewa wannan ba gaskiya ba ne."

"Misali, mata masu manyan nonuwa, idan suka koka kan ciwon baya ko ciwon kafaɗa, ana iya musu tiyata a rage girman."

"Haka nan mata masu ƙananan mama waɗanda kan shiga damuwa saboda hakan, akan yi tiyata a ɗan ƙara girman su. To amma, mu likitoci ba ma bayar da shawarar yin irin haka, amma ya dogara ne ga abin da mutane suka zaɓar wa kansu."

Haka nan likitar ta ce akwai rashin fahimta game da cewa, wai mata masu ƙananan nono ba su samar da ruwan mama kamar mata masu manya., kuma hakan ba daidai ba ne.

Jikin kowace mace na da karfin samar da isasshen ruwan mama da za a shayar da jariri. "Girman nono ba shi da alaƙa da yawan ruwan mama da mace za ta samar," in ji Dakta Kavya.