Da gaske ne shafa jinin al'ada na gyara fuska?

'मेंस्ट्रुअल मास्किंग'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata na bin yayi wajen shafa jinin al'ada a fuskarsu da sunan gyaran fata
    • Marubuci, Amrita Prasad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Tamil
  • Lokacin karatu: Minti 4

Mutane da yawa kan aikata abubuwa kawai saboda sun ga wasu na yi ko kuma domin biye wa yayi ko kuma tirendin a shafukan sada zumunta.

A wasu sassan duniya matasa sun fara rungumar ɗabi'ar shafa jinin al'ada a fuska, wanda suka yi imanin cewa yana sanya "fuska ƙyalli" tare da sanya fata haske.

A shafukan sada zumunta wasu na yi wa wannan abu taken ''menstrual masking".

Masu yin hakan sun yi ikirarin cewa jinin al'ada na ƙunshe da sinadarin 'retinol', kuma shafa shi a fuska zai sa fuska haske da ƙyalli.

Mece ce gaskiyar haka? Mene ne abin da ke ƙunshe a cikin jinin al'ada?

Me likitoci suka ce?

 'मेंस्ट्रुअल मास्किंग' पर डॉक्टर क्या कहते हैं

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dr Dinesh Kumar ya ce ɗabi'ar shafa jinin al'ada a fuska na da hatsari

BBC ta tattauna da wani likitan fuska a ƙasar Indiya, Dr. Dinesh Kumar.

Ya ce ‚ ''bai kamata mutane su riƙa shafa jinin al'ada a fuskarsu ba. Hakan zai iya cutar da mutum.''

Dr. Dinesh ya lissafa dalilai da suka sanya bai kamata mutane su shafa jinin al'ada a fatarsu ba:

  • Ba ya da wani alfanu
  • Babu binciken da ya nuna cewa jinin al'ada na gyara fata
  • Akwai yiwuwar cewa jinin na ƙunshe da ƙwayoyin cuta
  • Shafa jini a fatar da ke da ciwo ko ƙujewa zai iya cutarwa da kuma yaɗa cutuka

Me jinin al'ada ya ƙunsa?

पीरियड ब्लड

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jinin al'ada abu ne da jiki ya fitar wanda ba ya buƙata

Binciken cibiyar likitanci ta Amurka, wato 'US National Library of Medicine' ya nuna cewa jinin da mace ke fitarwa lokacin al'ada na ƙunshe da matattun ƙwayoyin halitta.

A kowane wata, jikin mace kan ɗauki haramar ƙyanƙyashe ƙwai, wato ɗaukar ciki, a wannan lokaci fatar cikin mahaifa kan ƙara kauri.

Idan ba a samu ɗaukar ciki ba, wannan ƙwayoyin fata da suka yi kauri kan fito waje a matsayin jinin al'ada.

A lokacin da jinin ke fitowa, yana kuma haɗowa da ruwan da ya ci karo da su a al'aurar mace.

Wannan kan sanya jinin ya cakuɗu da sauran sinadarai a kan hanyarsa ta fitowa waje, kamar abin da ake kira 'Lactobacillus', inda a ƙarshe zai kasance yana ƙunshe da abubuwa da dama, kamar matattun fata da sanadarai.

Bincike ya nuna cewa jinin al'ada na ƙunshe da sinadarai da suka kai 300, waɗanda kuma abubuwa ne waɗanda gangar jiki ba ya buƙata.

Shin za a iya shafa jinin al'ada a fuska?

डर्मटॉलजिस्ट डॉ. दिनेश कुमार कहते हैं कि पीरियड ब्लड को चेहरे पर लगाने का कोई फ़ायदा नहीं है

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ya kamata mutane su tuntuɓi likitoci kafin shafa abubuwa a fuska

Likitan fata Dr Dinesh Kumar ya ce shafa jinin al'ada a fuska ba shi da amfani, kuma zai iya cutarwa.

Ya yi gargaɗin cewa zai iya yin illa ga fata maras ƙwari da ke a fuska.

Likitan ya ce akwai yanayin da ake iya yin amfani da wani ɓangare na jinin jikin mutum wajen gyaran fuska, amma ba irin wannan ba.

Sai dai ya ce akan yi irin wannan ne a asibitoci da ke da ƙwararru a irin wannan fanni.

Ya yi gargaɗin cewa ba komai ne da ke tashe a shafukan sada zumunta mutane za su gwada a Zahiri ba.

Yadda za ki kula da fatarki

स्किन केयर

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a iya yin amfani da mayukan shafawa da suka dace domin kula da fuska

Dr. Dinesh ya ce fatar fuska ba ta da ƙwari, inda ya bayar da shawarar kan wasu hanyoyin da za a iya bi wajen kula da fuska:

  • Wanke fuska da ruwa mai tsafta ko sinadarin cleanser
  • Yin amfani da man shafawa domin hana fata bushewa
  • Amfani da man shafawa mai kare fata daga zafin rana
  • A zaɓi man shafawan fuska da ya dace da mutum
  • Samun isasshen bacci da cin abinci mai kyau