Me ya sa yara mata ke fara jinin al’ada tun shekara shida?

Wasu yara biyu 'yan makaranta rungume da juna, inda suka juya wa kyamara baya.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Deepali Jagtap, Sushila Singh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Marathi / BBC News Hindi correspondents
    • Aiko rahoto daga, India
    • Marubuci, Deepali Jagtap, Sushila Singh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Marathi / BBC News Hindi correspondents
    • Aiko rahoto daga, India
  • Lokacin karatu: Minti 5

Archana, mahaifiyar wata yarinya mai shekara shida, ta fahimci wasu muhimman sauye-sauye a jikin 'yarta wanda ba ta saba gani ba, kuma hakan ya yi matukar damun ta.

"Na tsorata da ganin wannan a jikin ƙaramar yarinya. Ƙaramin abu sai ya riƙa tunzura ta. Wannan abu ya dame ni," in ji ta.

Archana, ba sunanta na gaskiya ba, na zaune da iyalanta a wani ƙauye da ke gundumar Satara a yammacin Indiya.

Tana zaune a wani ƙaramin gida da aka gina cikin wata gona tare da mijinta da kuma 'ya'yansu biyu, namiji da yayarsa mace.

A lokacin da 'yar Archana ta fara bayyana wasu alamu a jikinta da suka zarta shekarunta, sai ta garzaya da ita asibiti domin ganin likita.

'Abin ya zo mana bambarakwai'

Wasu mata biyu riƙe da hannayensu sanye da awarwaro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar Archana ta fara nuna alamun balaga tun tana shekara shida

Haka ita ma, Rashi da ke zaune a Delhi ta riƙa ganin sauye-sauye a cikin yarta, amma sai ta ɗauka ba komai ba ne.

'Yarta mai shekara shida na da nauyin kilomgiram 40, amma sai ta ɗauka ''koshin lafiya'' ne.

Amma kwatsam, sai wata rana 'yar ta fara korafin ganin jini a jikinta.

Bayan sun je asibiti, sai aka gano cewa 'yar tata ta fara jinin al'ada ne.

"Mun ji abin wani bambarakwai. Yar tawa ba ta ma son me ake nufi ba,'' In ji Rashi.

A lokacin ne wani likitan ƙauyensu ya ba ta shawarar tuntuɓar likitan mata.

"A lokacin da Archana ta kawo mana 'yarta, bayan mun yi gwaje-gwaje sai muka gano cewa duka alamun balaga sun bayyana a jikinta. Jikinta ya koma kamar na 'yar shekara 14 zuwa 15, kuma jinin al'ada na dab da fara zuwa mata'', in ji Dakta Sushil Garud na asibitin kula mata a Pune.

Wata mata riƙe da cikinta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Galibi jinin al'ada kan fara daga shekarun 'yan matanci zuwa gomman shekaru.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Guru ya ce yawan sinadarin hormone da ke jikin yarinyar ya zarta na dadin shekarunta, kuma ya ce akwai dalilai da dama da ke haifar da hakan.

"Archana ta faɗa mana cewa akwai jarkunan maganin ƙwari biyu masu nauyin kilogiram biya-biyar a gidanta, kuma 'yar tata na yawan yin wasa a kusa da su. To wannan ɗaya ne daga cikin manyan dalilan da ka iya haifar da samun sauye-sauye a sinadarin hormone a jikin 'yan mata,'' in ji likitan.

Dakta Gurud ya ce sauye-sauyen da ke faruwa da wuri a jikin ƙananan yara ana kiran shi ''balagar wuri''.

Balaga wani mataki ne da ake samu sauye-sauye a jikin yaro ko yarinya, halittar gaɓoɓin saduwarsu kan ƙara girma ta yadda za su iya ba su damar iya mu'amalar saduwa.

A ɓangaren yara maza akan samu fitar gashi a gabansu da hamata, sannan muryarsu kan yi kauri. Su kuwa yara mata bayan fitar gashin akan samu fitar nono, sannan su fara jinin al'ada.

Galibi shekarun balaga a wajen 'ya'ya mata kan fara tsakanin shekara 8 zuwa 13, su kuwa maza tsakanin shekara 9 zuwa 14.

Dakta Vaishakhi Rustegi, ƙwararriyar likitar sinadarai a jikin yara da manya ta ce a shekarun baya-bayan nan ta fahimci an samu sauyi a shekarun balagar yara mata.

"A baya mun saba ganin 'yan mata na fara jinin al'ada wata 18 zuwa shekara uku bayan ganin sauye-sauyen farko a jikinsu. Amma yanzu jinin al'adar kan zo musu bayan wata uku zuwa huɗu,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

Ta ƙara da cewa a yanzu yara maza kan fara gemu da gashin baki cikin shekara ɗaya da rabi bayan ganin alamun farko na balagarsu, inda a baya yakan ɗauke su shekara huɗu kafin su fito.

Wata ƙaramar yarinya tsaye kusa da kofar gilashi yayin da rana ta hasko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekarun balaga a wajen yara mata kan fara tsakanin 8 zuwa 13, yayin da yara maza kuma shekara 9 ne zuwa 14.

Dakta Suchitra Surve, ta sashen binciken lafiyar ƙananan yara na majalisar binciken likitoci ta Indiya, ta faɗa a cikin bincikenta cewa an samu ƙaruwar yaran da ke balaga da wuri.

Binciken - wanda cibiyar bincike ta ƙasar ta gabatar kan yara mata 2,000, ya gano cewa iyaye da dama ba su iya fahimtar alamomin balagar wuri.

Majalisar Likitocin binciken sun kuma yi nazari kan abubuwan da ke haifar da balagar wurin da kuma hatarin hakan kan yara mata 'yan ƙasa da shekara tara.

A 2020, asibitin Bai Jerbai Wadia da ke birnin Mumbai da cibiyar binciken lafiyar ƙananan yara suka haɗa gwiwa kan binciken abin da ya sa shekarun balagar yara mata suka koma tsakanin shida zuwa tara.

“Yara mata 60, waɗanda shekarunsu suka kama daga shida zuwa tara, sun fuskanci balagar wuri, kuma wasu kan fara jinin al'ada a wannan lokaci,'' in ji Dakta Sudha Rau, wanda ke aiki a sashen yara na asibitin.

Me ke haddasa balagar wuri?

Jakar audugar mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Likitoci sun ce abubuwa da dama ne ke haifar da balagar wuri.

Likitoci sun ce akwai dalilai da dama da ke haifar da balagar wuri, kuma sun ce ba za a ɗora alhakin hakan kan dalili guda ba, saboda har yanzu ana kan bincike.

Sun yarda cewa magungunan ƙwari da sinadaran adana abinci, da gurɓacewar iska da matsanancin ƙiba na daga cikin dalilan.

Dr Prashant Patil, wanda ke nazarin batun tsakanin yara mata a Mumbai, ya ce matsanancin ƙiba na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa balagar wuri, kuma matsalar na ƙaruwar sakamakon ƙaruwar yaran da ke da matsanancin ƙiba a lokacin annobar korona.

Fiye da ƙananan yara miliyan 390 da matasa 'yan tsakanin shekara 5 zuwa 19 sun zama masu matsanancin nauyi a 2022, ciki har da miliyan 160 da ke da matsanincin ƙiba, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

Matsanancin ƙiba wata babbar cuta ce da yawan kitse ke haifarwa, wadda kuma za ta iya yi wa lafiya illa.

Akan aunata ta hanyar duba alƙaluman nauyin jiki, da suka haɗa da jinsi da shekaru da nauyi da tsayin yaro ko matashi.

Amfani da wayoyin hannu da kallon talbijin da sauran abubuwa masu screen fiye da ƙima, da rashin motsa jiki na daga cikin dalilan samun matsancin ƙiba.

Dakta Vaisakhi ta ce cikin shekara biyu zuwa uku da suka gabata , a kowace rana akan samu rahoton samun yara biyar zuwa shida da suka fara al'ada a sahshen kula da yara.

"Na kuma samu inda iyaye suka ce sun fuskanci sauye-sauye a jikin 'ya'yansu a watan Afrilu, ama suka fara al'ada a watan Yuni zuwa Yuli. To a yanzu ana samun ƙaruwar ahakan ma tsakanin yara maza,'' in j ta.

Ta ƙara da cewa yawan lokacin da yara ke ɓatawa suna kallon screen na haifar da balagar wuri a fakaice.

A yanzu duka 'ya'yan Archana da Rashi na karɓar magani domin jinkirta fara jinin al'adarsu har sai sun kai shekara 10 zuwa 11.

Likitoci sun ce a shekarunsu a yanzu, yaran ba su da wayon da za su kula da kansu har su tsaftace jikinsu a yayin jinin.

Likitocin sun kuma yi gargaɗin cewa yaran da ke samun balagar wuri ka iya fuskantar matsalolin ƙwaƙwalwa.

Bincike da dama sun gano cewa waɗanan yara jikinsu kan nuna wasu alamu, kuma ƙawayensu kan iya tsangwamarsu saboda sauye-sauyen da aka samu a jikinsu.